Mizanin Hada-hadar Tattalin Arzikin Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 5.4% A Rubu’in Farko Na Bana
Published: 16th, April 2025 GMT
Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar a yau Laraba 16 ga wata cewa, mizanin hada-hadar tattalin arziki da aka fi sani da GDP na kasar Sin ya karu da kashi 5.4 bisa dari kwatankwacin makamancin lokacin bara a cikin rubu’in farko na shekarar 2025. A tsakanin wannan lokacin, alkaluman hukumar sun kuma bayyana cewa, mizanin ya nuna hada-hadar tattalin arzikin kasar ta kai yawan adadin kudin Sin yuan tiriliyan 31, da biliyan 875 da miliyan 800, kwatankwacin dala tiriliyan 4.
Har ila yau, kamar yadda alkaluman mahukuntan suka nuna, karuwar darajar kayayyakin da masana’antu suka samar ta kai kaso 6.5 bisa dari duk dai a rubu’in farkon na bana. An samu wannan bunkasa ce cikin hanzari daga ci gaban da aka samu da kashi 5.9 a cikin watanni biyun farko. (Abdulrazaq Yahuza Jere).
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sojojin Mamayar Isra’ila Suna Ci Gaba Da Yin Kutse Cikin Yankunan Kasar Siriya
Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun sake yi wasu sabbin kutse a yankunan Quneitra na kasar Siriya
Rahotonni sun bayyana cewa: Da sanyin safiya ne sojojin mamayar Isra’ila suka kutsa cikin yankunan garin Saida da kuma kauyen Abu Mathra da ke yankin kudancin Quneitra na kasar Siriya.
Wannan ya zo daidai da wani sintiri da sojojin mamayar Isra’ila da ke ci gaba da yi a kauyen Kodna da ke cikin karkarar Quneitra, ba tare da wata arangama ko gargadi daga mahukuntan Siriya ba.
Ana ci gaba da yin shiru a hukumance dangane da irin wadannan tsauraran matakan da gwamnatin mamayar Isra’ila ke yi a kan iyakar kasar da tuddan Golan na Siriya da ta mamaye, lamarin da ya sanya ayar tambaya na cikin gida da na kasa da kasa game da yanayin tsaro a yankunan.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasar Siriya ta sanya ido kan yadda sojojin mamayar Isra’ila da suka hada da tankar yaki da mota mai sulke da kuma babbar mota dauke da sojoji kusan 30, inda suka kutsa cikin kauyen al-Samadaniyya al-Sharqiya da ke cikin yankin Quneitra. Sojojin mamayar Isra’ila sun binciki gidaje da dama kafin su janye zuwa sansanonin su, ba tare da samun rahoton kama mutane ba.