Gwamna Uba Sani ya amince da sabon tsarin biyan  diyya ta hanyar amfani da fasahar zamani  ga Hukumar Kula da Bayanan Filaye ta Kaduna (KADGIS), da nufin dakile almundahana a harkokin biyan diyya na filaye a fadin jihar.

Daraktan Hukumar KADGIS Dr. Bashir Garba Ibrahim, ne ya bayyana hakan yayin da ya karbi bakuncin mambobin Kungiyar ‘Yan Jarida ta kasa (NUJ), rashen Rediyon Najeriya Kaduna, a ofishinsa da ke Kaduna.

Dr. Bashir Garba Ibrahim ya bayyana cewa wannan sabuwar manhaja za ta rika adana bayanan masu asalin filayen da za a biya diyya, da suka hada da daukar hoton ‘yan yatsun da lambar katinsu na dan kasa NIN, domin hana masu zamba karbar diyya akan filayen da ba nasu ba ne.

Haka zalika, Daraktan ya yi bayanin sauye-sauye da aka aiwatar a karkashin jagorancinsa tun bayan hawansa kan mukami.

Ya ce cikin shekaru biyu da suka gabata, KADGIS ta warware sama da kararrakin rikicin fili 700, tare da kaddamar da tsarin rangwamen kashi 20 bisa 100 ga wadanda suka biya dukkan bashin da ke kansu gaba daya, wanda hakan ya inganta samun kudaden shiga da inganta ayyuka matuka.

Dr. Bashir Garba ya tabbatar da cewa yanzu takardar mallakar fili (Certificate of Occupancy – C of O) tana cikin tsarin gaggawa, inda ake iya fitar da ita cikin sa’o’i 24 muddin dukkan sharudda sun cika, inda ake iya bayar da takardun shaidar mallakar sama da 200 a kowane mako.

A nasa jawabin, Shugaban NUJ reshen Rediyon Najeriya Kaduna, Umar Adamu S. Fada, ya yaba wa Daraktan da dukkan ma’aikatan hukumar bisa wadannan sauye-sauye, musamman na sabuwar manhajar  biyan diyya, da kuma hanzarta fitar da takardun shaidar mallaka.

Ya nuna farin ciki da damar hadin gwiwa a tsakanin bangarorin biyu, tare da bayyana shirin kungiyar na yin aiki tare da sashen hulda da jama’a na hukumar domin inganta samar da bayanai.

Kungiyar ta kuma yi tayin tallafawa hukumar, ta hanyar amfani da shirye-shiryen tasharsu don kara kusantar da jama’a ga ayyukan hukumar, da kara fadakar da su kan harkokin filaye a fadin jihar.

 

Umar S. Fada 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

An kama shi da N25m na sayen kuri’u a zaɓen Kaduna

Jami’an tsaro sun kama wani mutum da tsabar kuɗi Naira miliyan 25 da ake zargin kuɗin sayen kuri’a ne a zaɓen cike gurbin da ke gudana a Jihar Kaduna.

Da misalin ƙarfe 3 na dare kafin wayewar garin safiyar Asabar da ake gudanar da zaɓen ne ’yan sanda da jami’an hukumar tsaro ta DSS suka kama mutumin a wani otel da ke hanyar Turunku a cikin birnin Kaduna.

A cewar rundunar ’yan sandan binciken farko da aka gudanar ya tabbatar da cewa wanda ake zargin ya shirya yin amfani da kuɗaɗen ne wajen sayen kuri’u

A yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ke  ya amsa laifinsa kuma ya roki a yi masa sassauci.

A wata sanarwa da kakaki rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar, Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Rabi’u Muhammad, ya yaba wa haɗin gwiwar jami’an tsaro, inda ya bayyana kama mutumin a matsayin wani muhimmin mataki na kare martabar zabe.

Ya kuma yi gargaɗin cewa duk wanda aka kama yana ƙoƙarin kawo cikas ga zaben, zai fuskanci hukunci ba tare da la’akari da matsayinsa ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An kama shi da N25m na sayen kuri’u a zaɓen Kaduna
  • Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ta Kai Ziyarar Gani Da Ido A Karamar Hukumar Gwiwa
  • Ba mu da tabbas na ci gaba da rijistar kaɗa ƙuri’a a Borno – INEC
  • An sake ceto matafiya 10 da aka sace a Kogi
  • Sojoji Sun Ceto Shugaban Fulani, Mutane 5 Daga Hannun Ƴan Bindiga A Kogi
  • NPA Ta Fito Da Sabuwar Doka Kan Kayan Da Ake Ajiyewa A Tashoshinta
  • An zabi sabuwar firaminista a Luthuania
  • NDLEA ta lalata gonar tabar wiwi a Gombe
  • ’Yan bindiga sun kashe tsohon malamin makaranta a Edo
  • Majalisar Dokokin Kano Ta Dakatar Da Shugaban Karamar Hukumar Rano Na Tsawon Watanni Uku