Sudan: Al-Burhan ya ce babu sulhu tsakaninsu da dakarun RSF
Published: 16th, August 2025 GMT
Shugaban majaliasar gudanarwa na kasar Sudan kuma babban hafsan hafsan sojojin kasar Sudan Abdel Fattah al-Burhan, ya yi alkawarin fatattakar dkarun RSF, tare da kawar da “duk wata dama ta yin sulhu.”
Kamfanin dillancin labaran Anadolu na kasar Turkiyyay a bayar da rahoton cewa, al-Burhan ya ce sojojin za su ci gaba da yaki ko ta halin kaka, kuma ba za su ci amanar sadaukarwar wadanda aka kashe a rikicin ba.
Al-Burhan ya yaba da irin tsayin dakan da sojojin suka yi a manyan garuruwa irinsu El Fasher, Babanusa, da Kadugli, yana mai cewa suna ci gaba da kare kasar ta kowace fuska.
Majiyar Al-Mayadeen ta bayar da rahoton cewa, Al-Burhan ya gabatar da wani fayil na tsaro da ke nuna yadda wasu kasashe ke da hannu wajen tallafa wa Dakarun RSF da kudade, da horo.
Wannan dai na zuwa ne a yayin tattaunawar tsaro da aka gudanar a birnin Zurich na kasar Switzerland, tare da babban mai baiwa shugaban kasar Amurka shawara kan harkokin Larabawa, Gabas ta Tsakiya da Afirka, Massad Boulos.
Al-Burhan ya kuma tabbatar da cewa “yakin da ake yi a Sudan yana wakiltar wani shiri ne dake nufin raba kan kasar Sudan,” yana mai jaddada cewa “Daular Sudan, da dakarunta da kuma kungiyoyin sa kai na jama’a sun tsaya tsayin daka don dakile wannan shiri.” Ya yi kira da a wargaza ‘yan bindiga, a rusa mambobinsu, a gurfanar da shugabanninsu gaban kuliya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Mali: An kama wasu Manyan Sojoji da Wani Bafaranshe bisa zargin yunkurin juyin mulki August 16, 2025 Wata Kotu a Canada ta ayyana APC da PDP a matsayin kungiyoyin ta’addanci August 16, 2025 Hizbullah Ta Ce Ba Zata Ajiye Makamanta Ba August 15, 2025 China Tace Bata Goyon Bayan A Sake Dorawa Iran Takunkuman MDD August 15, 2025 An Gano Gawar Wani Sojan HKI Wanda Ya Kashe Kansa Saboda yakin Gaza August 15, 2025 India Ta Dage Kan Maida martani da hana Shigowar Kayakin Amurka Kasar August 15, 2025 Duniyarmu A Yau: Ranar 40 Ta Imam Hussain (a) A Bana August 15, 2025 Larijani: Iran Zata Mayar Da Martani Mai Tsanani Kan Duk Wanda Ya Kai Mata Hari August 15, 2025 HRW; Kai Hari Kan Gidan Yarin Evin Na Iran Laifin Yaki Ne August 15, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kai Wani Mummunan Hari Kan Gaza August 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Al Burhan ya
এছাড়াও পড়ুন:
Kungiyar Ansarullahi Ta Kasar Yemen Ya Ce; Yahudawan Sahayoniyya Suna Yakar Al’ummar Falasdinu Duka Ne
Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya jaddada cewa: Makiya yahudawan sahayoniyya suna kai hari ga daukacin al’ummar Falasdinu ne
Babban sakataren kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen Sayyed Abdulmalik Badr al-Din al-Houthi ya tabbatar da cewa: Makiya yahudawan sahayoniyya suna kai hari kan dukkanin al’ummar Falastinu ne, yana mai jaddada cewa: Makiyan ‘yan sahayoniyya sun aikata kowane irin laifi da kowane nau’i na wuce gona da iri kan al’ummar Falastinu a zirin Gaza.
A jawabin da ya gabatar kai tsaye kan sabbin ci gaban da ake samu a hare-haren wuce gona da iri kan zirin Gaza da kuma ci gaban yanki da na duniya, Sayyed al-Houthi ya yi nuni da cewa, yawan hare-haren da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai cikin wannan mako tare da hadin gwiwar Amurka, ya lashe rayukan sama da shahidai 3,500 da jikkata, ciki har da yara, mata, da kuma ‘yan gudun hijira.
Ya kara da cewa, daga cikin wadanda harin kisan kiyashin makiya yahudawan sahayoniyya ya ritsa da su a cikin wannan mako, akwai wadanda kwalaye da fakitin da aka din ga jefa wa a iska a kan Falasdinawa da sunan taimako.
Ya kuma jaddada cewa, laifin kaka yunwa na daya daga cikin munanan laifuka da makiya yahudawan sahayoniyya suke aikata wa a zirin Gaza.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kungiyoyin Kasa Da Kasa Sun Koka Kan Hana Shigar Da Kayayyakin Jin Kai Yankin Gaza August 15, 2025 Laifukan Cin Zarafi Musamman Kisha Kiyashi A Kasar Siyasa Ya Doshi Laifukan Yaki August 15, 2025 Kungiyar Ba Da Agaji Ta Sanar Da Yadda Cutar Kwalara Take Lashe Rayukan Mutane A Kasar Sudan August 15, 2025 Miliyoyin Mutane Sun Taru A Karbala Don Juyayin 40 Na Shahadarsa Imam Hussain(a) August 14, 2025 Sayyid Huthi Ya Yi gargadi Yiyuwar Tarwatsewar kasashen yankin idan HKI Ta Tabbaga Shirinta August 14, 2025 An Bukaci Ficewar Marasa Lafiya da Likitoci daga Wani Babban Asbiti A birnin London August 14, 2025 Za’a Fara tattaunawar Kasa Dangane Da Talauci da Kuma Rashin Adalci A Rabin Arziki A kasar August 14, 2025 Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Yi Tsokaci Kan Furucin Netanyahu Game Da Kafa “Babbar Kasar Isra’ila’ August 14, 2025 Iran Ta Bukaci Mayar Da Martani Kan Aniyar Isra’ila Ta Mamaye Yankunan Kasashe Domin Kafa ‘Babbar Isra’ila’ August 14, 2025 Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ya Bayyana Isra’ila A Matsayar ‘Yar Yaudara August 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci