Takht-Ravanchi: Iran a shirye take ta ci gaba da tattaunawa kan hakkinta na nukiliya
Published: 16th, August 2025 GMT
Wani babban jami’in diflomasiyyar Iran ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shirye take ta ci gaba da tattaunawa da kasashen Turai da kuma kare hakkinta na nukiliya cikin lumana.
Mataimakin ministan harkokin wajen Iran Saeed Khatibzadeh ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da tashar dillancin labaran Turkiyya, a lokacin da yake amsa tambaya kan tattaunawa da aka shirya yi tsakanin Iran da E3 (Faransa, Birtaniya da Jamus) a nan gaba, yayin da kuma an riga an gudanar da zama zagaye na biyu na masana da kwararru a matsayin sharar fage a birnin Istanbul na kasar Turkiyya a karshen watan Yuli.
“Yanzu, wadannan shawarwari za su ci gaba, mun yanke shawarar ci gaba, kuma za mu yi hakan,” in ji shi.
Sai dai ya jaddada bukatar yin taka-tsan-tsan don tabbatar da cewa babu wanda zai yi amfani da shawarwarin bangarorin biyu a matsayin wata hanya ta cimma burins ana siyasa.
Ya bayyana fatan cewa kasashen Turai uku za su fahimci cewa “idan manufar ita ce cimma yarjejeniya mai ma’ana tsakanin bangarorin biyu, to komai mai yiwuwa ne.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sudan: Al-Burhan ya ce babu sulhu tsakaninsu da dakarun RSF August 16, 2025 Mali: An kama wasu Manyan Sojoji da Wani Bafaranshe bisa zargin yunkurin juyin mulki August 16, 2025 Wata Kotu a Canada ta ayyana APC da PDP a matsayin kungiyoyin ta’addanci August 16, 2025 Hizbullah Ta Ce Ba Zata Ajiye Makamanta Ba August 15, 2025 China Tace Bata Goyon Bayan A Sake Dorawa Iran Takunkuman MDD August 15, 2025 An Gano Gawar Wani Sojan HKI Wanda Ya Kashe Kansa Saboda yakin Gaza August 15, 2025 India Ta Dage Kan Maida martani da hana Shigowar Kayakin Amurka Kasar August 15, 2025 Duniyarmu A Yau: Ranar 40 Ta Imam Hussain (a) A Bana August 15, 2025 Larijani: Iran Zata Mayar Da Martani Mai Tsanani Kan Duk Wanda Ya Kai Mata Hari August 15, 2025 HRW; Kai Hari Kan Gidan Yarin Evin Na Iran Laifin Yaki Ne August 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sudan: Al-Burhan ya ce babu sulhu tsakaninsu da dakarun RSF
Shugaban majaliasar gudanarwa na kasar Sudan kuma babban hafsan hafsan sojojin kasar Sudan Abdel Fattah al-Burhan, ya yi alkawarin fatattakar dkarun RSF, tare da kawar da “duk wata dama ta yin sulhu.”
Kamfanin dillancin labaran Anadolu na kasar Turkiyyay a bayar da rahoton cewa, al-Burhan ya ce sojojin za su ci gaba da yaki ko ta halin kaka, kuma ba za su ci amanar sadaukarwar wadanda aka kashe a rikicin ba.
Al-Burhan ya yaba da irin tsayin dakan da sojojin suka yi a manyan garuruwa irinsu El Fasher, Babanusa, da Kadugli, yana mai cewa suna ci gaba da kare kasar ta kowace fuska.
Majiyar Al-Mayadeen ta bayar da rahoton cewa, Al-Burhan ya gabatar da wani fayil na tsaro da ke nuna yadda wasu kasashe ke da hannu wajen tallafa wa Dakarun RSF da kudade, da horo.
Wannan dai na zuwa ne a yayin tattaunawar tsaro da aka gudanar a birnin Zurich na kasar Switzerland, tare da babban mai baiwa shugaban kasar Amurka shawara kan harkokin Larabawa, Gabas ta Tsakiya da Afirka, Massad Boulos.
Al-Burhan ya kuma tabbatar da cewa “yakin da ake yi a Sudan yana wakiltar wani shiri ne dake nufin raba kan kasar Sudan,” yana mai jaddada cewa “Daular Sudan, da dakarunta da kuma kungiyoyin sa kai na jama’a sun tsaya tsayin daka don dakile wannan shiri.” Ya yi kira da a wargaza ‘yan bindiga, a rusa mambobinsu, a gurfanar da shugabanninsu gaban kuliya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Mali: An kama wasu Manyan Sojoji da Wani Bafaranshe bisa zargin yunkurin juyin mulki August 16, 2025 Wata Kotu a Canada ta ayyana APC da PDP a matsayin kungiyoyin ta’addanci August 16, 2025 Hizbullah Ta Ce Ba Zata Ajiye Makamanta Ba August 15, 2025 China Tace Bata Goyon Bayan A Sake Dorawa Iran Takunkuman MDD August 15, 2025 An Gano Gawar Wani Sojan HKI Wanda Ya Kashe Kansa Saboda yakin Gaza August 15, 2025 India Ta Dage Kan Maida martani da hana Shigowar Kayakin Amurka Kasar August 15, 2025 Duniyarmu A Yau: Ranar 40 Ta Imam Hussain (a) A Bana August 15, 2025 Larijani: Iran Zata Mayar Da Martani Mai Tsanani Kan Duk Wanda Ya Kai Mata Hari August 15, 2025 HRW; Kai Hari Kan Gidan Yarin Evin Na Iran Laifin Yaki Ne August 15, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kai Wani Mummunan Hari Kan Gaza August 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci