Majalisar dokokin Gombe ta fara duba ƙudirin ƙirƙirar sabbin gundumomi 13
Published: 16th, August 2025 GMT
Majalisar Dokokin Jihar Gombe, ta fara duba ƙudirin ƙirƙirar sabbin gundumomin ci gaban Ƙananan Hukumomi 13 da Gwamna Inuwa Yahaya ya gabatar.
Ƙudirin ya tsallake karatu na farko da na biyu cikin rana guda.
Zaɓen cike gurbi: An samu ƙarancin masu kaɗa ƙuri’a a Zariya An kama ’yan daba 288 yayin zaɓen cike gurbi a KanoKakakin majalisar, Abubakar Muhammad Luggerewo, ya bayyana hakan ne yayin zaman sauraron ra’ayin jama’a a kan ƙudirin, wanda aka gabatar wa majalisar kwanaki uku da suka gabata.
Ya ce majalisar ta yi gaggawar karanta ƙudirin saboda muhimmancinsa, domin zai taimaka wajen kusantar da gwamnati ga jama’a.
Hakazalika ya ce zai kawo ci gaba a ƙauyuka, da kuma tabbatar da amfani da dukiyar jihar ta hanyar da ta dace.
Kakakin ya ƙara da cewa an shirya sauraron ra’ayin jama’a domin samun shawarwari daga al’umma, shugabanni da ƙungiyoyi domin ƙara wa ƙudirin armashi.
Taron ya samu halartar manyan masu ruwa da tsaki a jihar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Majalisar Dokoki
এছাড়াও পড়ুন:
Kungiyar ‘Yan Dako Ta Kasa Ta Nada Sabon Sakatare A Jigawa
Kungiyar ‘Yan Dako ta kasa reshen jihar Jigawa ta kaddamar da Malam Muhammad Tajudeen Maigatari a matsayin sakataren kungiyar na jihar.
Da yake jawabin a lokacin bikin kaddamawar a garin Maigatari, Shugaban kungiyar na jihar Malam Nasiru Idris Sara, ya bayyana shugabanci a matsayin rikon amana a maimakon hanyar tara dukiya da alfahari, a don haka akwai bukatar sakataren ya yi aiki tukuru dan kare martabar sana’ar dako da masu yin ta.
Yana mai cewar shugabancin kungiyar zai hada kai da shugabannin kananan hukumomi da masu rike da sarautu da jami’an tsaro a matsayin abokan kawo cigaba wajen daga likkafar sana’ar dako.
Nasiru Idris Sara ya kuma yi kira ga daukacin ‘yan dako a fadin jihar da su yi rijista da kungiyar domin kasacewa a karkashin inuwa daya ta yadda za su ci moriyar tanade tanaden ta, sannan su kasance masu mutunta shugabanci da kuma bin doka da oda domin inganta rayuwar su.
Ya ce yayin da kungiyar ta ke da ‘yan dako kimanin dubu 20 a karkashin ta, akwai bukatar duk ‘yan dakon da ba su da katin zabe su karbi sabo ko kuma su sabunta wanda ya bata ko ya lalace domin amfani da damar su wajen zaben shugabanni.
A sakon sa, Hakimin Maigatari Alhaji Sani Alhassan Muhammad wanda ya sami wakilcin Sarkin Kasuwar Maigatari Alhaji Muhammadu Sarkin Kasuwa, ya bukaci sabon sakataren kungiyar Malam Muhammad Tajudeen ya kasance mai nuna gaskiya da adalci wajen huldar sa da ‘yan dako da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin kasuwanci, inda ya bayyana murnar samun wannan mukamin.
Cikin wadanda suka halarci taron sun hada da Sarkin hatsin Maigatari, Malam Mu’azu Bako da Shugaban leburorin Dingas na Jamhuriyar Nijar Malam Lawwali Hassan.
Usman Mohammed Zaria