2025-08-02@09:26:22 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1240

«Sarakunan Gargajiya»:

    Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum ya haramta sayar da man fetur a Ƙaramar Hukumar Bama ta jihar, ciki har da garin Banki. Gwamnan ya ce haramcin ya zo ne bayan tattaunawa da hukumomin tsaro a jihar, kuma an yi haka ne domin shawo kan matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta. Gidauniya ta yi wa masu...
    Shugaban kungiyar ya yi magana Ibrahim Yusuf Babayo,Shugaban kungiyar  Miyetti Allah masu kiwon dabbobi na kasa ya bayyanawa jaridar karshen mako cewar dukkan hare- haren da ake kaiwa dabbobin da kuma kashesu an sanar da jami’an tsaro daban- daban,da suka hada da Kwamanda na rundunar soja ta,3 kuma kwamandan Operation Safe Haben (OPSH), Manjo- Janar...
    BBC ta rawaito cewa, babban abin da ke damun kamfanin na Meta shi ne, yadda al’amarin ya shafi Hukumar Kare Bayanan Sirri ta Nijeriya (NDPC), wanda kamfanin ke zargin karya dokokin kare bayanan sirrin kasar. Baya ga tarar Hukumar FCCPC, hukumar ta NDPC ta ci tarar kamfanin Meta dala miliyan 37.8, bisa zargin satar bayanan...
    Hukumomi a Jami’ar Colombia dake birnin NewYork na kasar Amurka sun bada sanarwan cewa, sun dakatar da karatun daliban jami’ar fiye da 65 saboda shiga cikin zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a kusa da babban dakin ajiyar littafai ko karatu a Jami’ar a ranar Laraban da ta gabata. Tashar talabijin ta Press tv a nan Tehran...
    Daga ranar 7 zuwa ta 8 ga watan Mayun nan, tawagar likitocin kasar Sin a kasar Saliyo karo na 26 ta shiga cikin yankunan karkara da dama na kasar Saliyo, inda ta kammala ayyuka hudu na bayar da jinya kyauta cikin kwanaki biyu, tare da bayar da hidimar jinya ga mazauna kauyakan da ma’aikatan kamfanoni....
    Wannan mataki ya haifar da gagarumar muhawara a duniya. Yayin da manufar ke da nufin farfado da Hollywood da karfafa shirya fina-finai na cikin gida. Amma mu tambayi kanmu, shin da gaske wannan ita ce hakikanin manufar? Amma bari mu yi la’akari da wannan hasashen mu gani, ko shi ne ya fusata Amurka ta maka...
    Gwamnatin Nijeriya ta sanar da dakatar da tsarin bai wa ɗalibai tallafi domin samun damar zuwa ƙetare ƙarin ilimi. Ministan Ilimi, Tunji Alausa, shi ne ya sanar da wannan mataki, da ke nufin cewa za a kawo ƙarshen wannan tsari da aka share tsawon shekaru ana aiwatarwa. Yadda yara 5 suka mutu a cikin motar...
    Ƙungiyar Allied Group of Nasarawa Professionals (AGNP), wadda ta ƙunshi ’yan kasuwa da masu sana’o’in hannu, ta goyi bayan tsohon Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Mohammed Adamu, wanda ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Gwamnan Jihar Nasarawa a 2027. A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a ofishinta da ke Keffi, AGNP ta ce matakin...
    Masana harkokin masana tsaro sun nuna rashin amincewarsu da iƙirarin sojojin Najeriya cewa baƙi daga ƙasashen waje ne ke kai yawancin hare-haren da ake kaiwa al’ummomin ƙasar, musamman a jihohin Filato da Benue. Wannan ƙalubalen ya fito ne bayan wata sanarwa da Hedikwatar Tsaro ta yi a ranar Alhamis, cewa yawancin hare-haren da ake kai...
    Yau Juma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bukukuwan cika shekaru 80 da cimma nasara a yakin kishin kasa na tsohuwar Tarayyar Soviet. An gudanar da faretin soja na ranar samun nasara, wanda ke ayyana cika shekaru 80 da samun nasara a yakin kishin kasa na Tarayyar Soviet ne a birnin Moscow. Shugabanni daga...
    Masana harkokin masana tsaro sun nuna rashin amincewarsu da iƙirarin sojojin Najeriya cewa baƙi daga ƙasashen waje ne ke kai yawancin hare-haren da ake kaiwa al’ummomin ƙasar, musamman a jihohin Filato da Benue. Wannan ƙalubalen ya fito ne bayan wata sanarwa da Hedikwatar Tsaro ta yi a ranar Alhamis, cewa yawancin hare-haren da ake kai...
    Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-husy ya bayyana cewa kisan kiyashin  da HKI take yi wa Falasdinawa a tsawon  watanni 19 a jere, shi ne laifi mani muni  akan bil’adama da ya faru a cikin karni daya. Sayyid Abdulmalik al-Husi ya kuma ce, abinda ya kara munin wannan laifin shi ne yadda...
    A yau, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Rasha Vladimir Putin sun gana tare da manema labarai bayan tattaunawa a fadar Kremlin dake birnin Moscow. Inda Xi ya jaddada cewa, a yayin da yanayin kasa da kasa ke fuskantar sauye-sauye da hargitsi, kamata ya yi kasashen Sin da Rasha su yi riko da...
    Babban Sufeto Janar na ’yan sandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun ya ƙaddamar da Ƙwararrun Jami’an tsaro da za su kare makarantu a Bauchi, Egbetokun ya ƙaddamar da tawagar ne a ranar Alhamis a Bauchi. A wajen ƙaddamar da taron masu ruwa da tsaki na ‘Saɓe Schools’ a ɗakin taro na otal ɗin Hazibal.  Ya ce,...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa akwai bukatar kasashen Indiya da Pakisatan su daure su daina musayar wuta a tsakaninsu saboda tabbatar da zaman lafiya a yankin Asiya. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a safiyar yau Alhamis bayan isarsa birnin News Delhi. A...
    Wasu yan jaridu masu bincike a kasar Amurka sun gano sunan sojan HKI wanda ya bindige yar rahoton tashar Aljazeera ta kasar Qatar a shekara ta 2022 a lokacinda take Shirin bada rahoton hare-harenn da sojojin yahudawan suke kaiwa kan wata unguwa ta Falasdinawa a birnin Jenin na yankin yamma da Kogin Jordan. Tashar talabijin...
    Shugaban kasar Rasha Vladimit Putin ta tokwaransa na kasar China Xi Jinping sun tattauna a birnin Mosco a yau Alhamis, inda kasashen biyu suka kara dankon zuminci a tsakaninsu, da fatan zasu bukasa harkokin kasuwanci da ci gaba a tsakaninsu nan da shekara ta 2030. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa...
      Karamar Hukumar Birnin Kudu ta nuna gamsuwa da yadda aikin tantance yan fansho ya gudana a yankin. Shugaban Karamar Hukumar, Dr Builder Muhammed Uba ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin jami’an gudanar da aikin tantance yan fanshon jim kadan da kammala aikin a sakatariyar Karamar hukumar. Yace karamar hukumar ta gamsu...
    Tawagar jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal ta haɗa da sakataren gwamnatin jihar, da masu ba da shawara na musamman guda biyu, da babban sakataren ZITDA, tare da Siobhan Wilson, shugaban Oracle na Ingila da kuma babban mataimakin shugaban EMEA.   Sanarwar ta ƙara da cewa: “Gwamnatin jihar Zamfara ta rattaba hannu kan wata...
    Amurka ta matsa wa gwamnatocin wasu ƙasashe da Shugaba Donald Trump ya ƙaƙaba musu haraji su  amince da kamfanin intanet na Starlink mallakin Elon Musk a ƙasashensu. Elon Musk shi ne mai kuɗin duniya kuma babban makusanci ne ga Shugaba Donald Trump. Jaridar Washington Post ce ta ruwaito hakan a ranar Laraba, tana mai ambaton...
    Houthis sun kai hari kan babban filin jirgin sama na Isra’ila kusa da Tel Aviv a ranar Lahadi, a wani ɓangare na yaƙi da ‘yan tawayen ke yi kan Isra’ila, a matsayin tallafin ga Falasdinawa a Gaza. Iran ta musanta cewa ta goyi bayan Houthis a harin. Duk da haka, Isra’ila ta mayar da martani...
    An gabatar da shirin talabijin na kasa da kasa mai taken “Kalaman Magabata dake Jan Hankalin Xi Jinping” jiya Laraba a kasar Rasha, yayin da shugaban Sin Xi Jinping ya isa birnin Moscow domin ziyarar aiki a kasar da kuma halartar bukukuwan cika shekaru 80 da samun nasarar yakin ceton kasa na tsohuwar tarayyar Soviet....
    Fira ministan kasar Siriya ya bayyana cewa: Kasar Siriya zata gudanar da tattaunawa ba na kai tsaye ba da haramtacciyar kasar Isra’ila! Shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Siriya Abu Mohammed al-Julani ya sanar a jiya Laraba cewa: Kasar Siriya zata gudanar da zaman tattaunawa ba na kai tsaye ba da gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar...
    A cewar sa, wannan bita tana da nufin tantance yadda aka samu cigaba a aiki, da kuma tabbatar da cewa hukumomin da ke ƙarƙashin ma’aikatar suna tafiya daidai da abin da aka ɗora masu a matsayin nauyi.   Ya ce: “Muna nan ne don sauraron shugabannin hukumomi domin mu ga yadda suka aiwatar da muhimman...
    Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayana labarummu na yau zai yi magana dangane da ‘Mahangar Jumhuriyar Musulunci na Iran ta yadda za’a kai ga fahintar juna a tattaunawanta da kasar Amurka da suke yi wanda ni tahir amin zan karanta. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi a wata tattaunawa ta wayar tarho da tokwaransa...
    Al’ummar garin Izge da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza ta Jihar Borno sun fatattaki ’yan ƙungiyar Boko Haram bayan kai musu hari a ranar Laraba. Ƙungiyar ‘yan ta’addan ta kuma kashe wani kaftin ɗin soji a harbin na ba zata. Jami’an tsaro na ba da gudunmawar aikata miyagun laifuka a Nijeriya — Zulum Jami’an tsaro na...
    “Dole ne mu daina tallata miyagun ayyukan ‘yan ta’adda. Dole ne mu cire su daga jerin shafukan manyan labarai na jaridunmu, mu rahoto ayyukansu a matsayin masu aikata laifuka, sannan mu kore labaran karya.”   Ministan ya jaddada cewa, kungiyoyin ta’addanci da masu aikata laifuka sukan yi amfani da kafafen yada labarai da shafukan sada...
      Duk da yadda Amurka ke haifar wa tattalin arzikin duk fadin duniya da barazana da kalubale bisa matakin harajin kwastam da ta kara kakkaba wa sauran kasashen, da yanayi maras tabbas da Sin take fuskanta a waje, ingancin tattalin arzikin Sin yana shaida abun da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fada, wato tattalin...
    Sai dai, rikice-rikicen cikin gida da matsalolin tsaro da tattalin arziƙi sun sa gwamnatin ke ci gaba da yin gyare-gyare don samar da hanyoyin da za su ba ta kariya da cikakken iko kan harkokin leƙen asiri da tsaro. Wannan mataki yana iya nuni da cewa Nijar na ƙoƙarin zama mai dogaro da kai a...
    Kasar Sudan ta yanke huldar jakadancinta da kasar Hadaddiyar Daulart Larabawa tana mai ayyana UAE a matsayin ‘kasa mai cin zali’ Kamfanin dillancin labaran Sudan (SUNA) ya watsa rahoton cewa: Kwamitin tsaro da kula da matakan tsaron kasar Sudan ya sanar a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Talata cewa: Sudan ta yanke...
    Karamar Hukumar Birnin Kdu tace tana nazarin samar da cibiyar horas da maniyyata aikin hajji ta dindindin a yankin domin karawa mahajjata kaimi wajen gudanar da aikin karbabbe.   Shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Muhammad Uba Builder ya bada wannan tabbacin a lokacin rufe bitar da aka shiryawa maniyyatan yankin na Birnin kuudu.   Yana mai...
    Hukumar Kula da Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna za ta fara jigilar maniyyata zuwa kasar Saudiyya a ranar 14 ga watan Mayu, 2025. Shugaban hukumar, Malam Salihu S. Abubakar, ne ya bayyana hakan a wani shirin rediyo kai tsaye da aka watsa daga Kaduna, inda ya bayyana shirye-shiryen da jihar ta kammala domin aikin...
    A wani bangare na wasikar na cewa, “An umurce ni da in isar da amincewar Gwamnati na fitar da jimillar kudi Naira miliyan 15,227,272.72 a asusun kowace karamar hukuma domin gyaran motoci biyu tare da siyo karin wasu guda hudu ga Majalisar masarautar Kano wanda kamfanin Sottom Synergy Resources Ltd zai dauki nauyin siyowa.  ...
    Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da “Bankasar tattalin arzikin Iran duk tare da takunkuman tattalin arziki masu tsanani wadanda kasashen yamma musamman Amurka suka doramata, wanda ni tahir amin zan karanta. ////…A dai-dai lokacinda gwamnatin kasar Amurka take barazanar zata hana sayan danyen man fetur daga kasar Iran kwatakwata,...
    Kotun duniya ta yi watsi da karar da Sudan ta kai Hadaddiyar Daular Larabawa tana mai zarginta da hannu a kisan kiyashin da aka yi wa al’ummar wannan kasa. A yau Litinin ne kotun duniyar ta yi watsi da karar ta Sudan, tana mai wanke Hadaddiyar Daular Larabawa. Ita dai Sudan ta zargi Hadaddiyar Daular...
    ’Yan fashi sun harbe mafarauta da fararen hula kimanin 19 har lahira a Karamar Hukumar Alƙaleri ta Jihar Bauchi. A yayin ziyarar da ya kai wurin, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Bauchi, Sani-Omolori Aliyu, ya ba da umarnin yin cikakken bincike da kuma tura karin jami’an tsaro yankin. Mazauna kauyen Mansur sun ce an kashe ’yan...
    ’Yan fashi sun harbe mafarauta da fararen hula kimanin 19 har lahira a Karamar Hukumar Alƙaleri ta Jihar Bauchi. A yayin ziyarar da ya kai wurin, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Bauchi, Sani-Omolori Aliyu, ya ba da umarnin yin cikakken bincike da kuma tura karin jami’an tsaro yankin. Mazauna kauyen Mansur sun ce an kashe ’yan...
    Yau Litinin ne kotun kasa da kasa ta ICJ za ta yanke hukunci kan karar da Sudan ta shigar kan Hadaddiyar Daular Larabawa. Khartoum ta kai karar UAE a gaban kotun kasa da kasa da ke birnin Hague, inda ta zarge ta da hannu wajen kisan kiyashin da ake yi wa al’ummar Masalit, sakamakon zarginta...
    Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa: Gaza na gaf da afkawa cikin babbar masifa saboda zaluncin ‘yan mamayar Isra’ila A yayin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke ci gaba da killace Zirin Gaza sama da watanni biyu, abubuwan da ke faruwa a kowace rana, abubuwa ne da suke yadda bala’i ke shafar kowane gida, kowane...
    Tawagar haɗin gwiwar jami’an tsaro na aikin gano gawarwakin wasu mafarauta da mayaƙan Lakurawa suka kashe a yankin Ƙaramar Hukumar Tangaza da ke Jihar Sakkwato. Ana fargabar Lakurawa sun yi garkuwa da wasu daga cikin mafarautan da suka fito daga ƙananan hukumomin Tangaza da Gwadabawa, bayan sun faɗa tarkon ’yan ta’addan Aminiya ta ruwaito cewa...
    Ana ci gaba da gwabza kazamin fada a yammacin Sudan tsakanin sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa na kasar Jiragen saman yaki marasa matuki ciki na dakarun kai daukin gaggawa sun kai hare-hare kan sansanin sojin sama na Osman Digna da ke gabashin Sudan, inda suka janyo bullar gobara a ma’ajiyar harsasai. Jiragen saman...
    Rahotonni na cewa mayaƙan Boko Haram sun kai kashe dakaru huɗu yayin wani hari da suka kai sansanin soji a Jihar Yobe. Aminiya ta ruwaito cewa ’yan bindigar sun ƙaddamar da hari kan sansanin soji na “27 Task Force Brigade” da ke garin Buni Yadi, a yankin Ƙaramar Hukumar Gujba da tsakar daren Asabar. Abin...
    Gwamnatin HKI ta bada sanarwan halakar sojojinta biyu da kuma jikatan wasu alokacinda suke bincike da kuma kokarin shiga wani rami na karkashin kasa a inda wani bom ya tashi ya kashe su ya kuma raunata wasu. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakafen yana labaran yahudawan na fadar haka a safiyar...
      Liverpool ta yi wannan kwazon karkashin sabon koci, Arne Slot da ta dauka kan a fara kakar nan, wanda ya maye gurbin Jurgen Klopp, wanda ya yi ritaya. Tun farko Liberpool ta yi fatan lashe kofi hudu a kakar nan, sai dai an yi waje da ita a League da FA Cup. Haka kuma...
    Gudu ya zamto wani bangare na rayuwar Antonio Rao tsawo dan kasar Italiya da yake da shekara 80, wanda yanzu yake da shekara 92, inda ba shi da shirin daina shiga gasar tsere. A bana, ya kammala gasar gudun fanfalaƙi na Rome karo na 30 a jere cikin kasa da sa’o’i bakwai. Ɗan shekara 19...
    Rundunar sojojin Najeriya ta 1 karkashin jagorancin Birgediya Janar Timothy Opurum ta samu gagarumar nasara a yakin da take yi da ta’addanci da ‘yan bindiga a jihar Zamfara, musamman a kananan hukumomin Talata Mafara da Kaura Namoda.   A wata sanarwa da mukaddashin mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar soji, Kyaftin Sulaiman Omale ya...
    Khalifa Aminu, matashi ne mai shekaru 19 wanda ya ƙirƙiri na’urori da abubuwan ban mamaki waɗanda hatta mutanen da suka zurfafa karatu a fannin kimiyya da kere-kere ba su sami irin wannan nasarar ba. A tattaunawarsa da Aminiya, Khalifa wanda ya ce da kyar ya iya kammala karatunsa na sakandare, ya bayyana yadda ya kirkiro...
    Dakta Abdulmalik ya ce, a halin yanzu gwamnatin jihar na da likitoci 99 kadai ne, wadanda ke kan tsarin albashi, ya kara da cewa; adadin da ake bukata kuma sun kai kimanin 180 zuwa 200.   “Likitoci ukun da suka bar aiki, sun dawo bayan karin albashin likitocin da gwamnan ya yi a baya-bayan nan....
    Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta tabbatar da cewa: Adadin wadanda suka yi shahada sakamakon ayyukan ta’addancin ‘yan sahayoniyya ya karu zuwa 52,495 Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar a jiya Asabar 3 ga watan Mayu, shekara ta 2025 cewa: Falasdinawa 77 ne da suka yi shahada da suka hada da gawarwakin mutane 7 da aka...
    A cikin jawabin sa a taron, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana wasu manyan fa’idoji da kuma irin barazanar da ke tattare wajen amfani da AI a cikin ɗakunan buga labarai.   Ya ce duk da cewa AI na taimaka wa ‘yan jarida a Nijeriya wajen saurin bayar da...