APC ta yi barazanar hukunta “Yaran Badaru” a Jigawa
Published: 6th, September 2025 GMT
Jam’iyyar APC reshen Jihar Jigawa ta gargaɗi mambobinta da su guji aikata rashin ladabi da halayen da ba su dace ba da za su iya kawo rabuwar kai a cikin jam’iyyar.
A cikin wata sanarwa da sakataren jam’iyyar na jiha, Muhammad Dikuma Umar ya sanya wa hannu, APC ta nuna damuwa kan abin da ta kira yawaitar rashin ɗa’a daga wani rukunin magoya bayan tsohon gwamna kuma Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar, da ta kira da suna “Badaru Boys.
Sanarwar ta zargi wannan rukunin da haddasa rikice-rikice a wuraren tarukan siyasa, tare da yunƙurin ɓata sunan gwamnatin Gwamna Malam Umar Namadi.
Ta bayyana cewa hakan ya faru a wurare da dama ciki har da Majiya, Gumel da kuma zaben cike gurbin Babura/Garki, inda aka ce sun tayar da rikici.
Tsohon mataimakin Gwamnan Gombe da wasu jiga-jigai sun fice daga PDP zuwa APC An haramta wa makarantu tilasta wa iyaye sayen sabbin litattafai duk shekara a FilatoJam’iyyar ta kuma zargi magoya bayan tsohon gwamnan da kai hare-hare da cin fuska ga gwamnatin yanzu, musamman a taron da aka gudanar a Kafin Hausa, garin Gwamna Namadi, inda suka yi ta zage-zage.
APC ta bayyana takaicinta kan yadda tsohon gwamna bai tsawatar wa magoya bayansa ba, sai dai ta yaba wa Gwamna Namadi bisa haƙuri da natsuwa da yake nunawa duk da tayar da hankali da ake yi masa.
“Fitinar ‘Badaru Boys’ ta yi yawa. Wannan ɗabi’a, wadda za ta iya ɓata wa jam’iyya suna, ta sabawa sashe na 21 na kundin tsarin mulkin APC,” inji sanarwar.
Jam’iyyar ta yi gargaɗi cewa idan irin wannan hali ya ci gaba, ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen amfani da tanade-tanaden kundin tsarin mulki domin kawo ɗa’a. Ta kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su ɗauki matakan gaggawa don hana ɓarkewar rikici daga rashin jituwar siyasa.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Jihar Jigawa Ta Amince Da Karin Kasafin Kuɗi Na Naira Biliyan 75 Na Shekarar 2025
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da ƙarin kasafin kuɗi na Naira Biliyan 75 na shekarar 2025, ga gwamnatin jiha da kuma ƙananan hukumomi 27.
Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan zaman majalisar da aka gudanar a gidan gwamnati dake Dutse, babban birnin jihar.
Ya bayyana cewa, wannan ƙarin kasafin kuɗi ya samo asali ne daga ƙarin kuɗaɗen shiga domin biyan buƙatun kuɗaɗen da suka taso, da kuma ƙarfafa manyan fannoni da za su kawo ci gaba mai ɗorewa a faɗin jihar.
Alhaji Sagir Musa Ahmed ya ce, majalisar ta amince da Naira Biliyan 58 ga gwamnatin jiha da kuma Naira Biliyan 17 ga Kananan Hukumomi 27, wanda ya shafi kashe-kashen kudade na yau da kullum da kuma manyan ayyuka.
Ya ce, wannan ƙarin kasafin kuɗin zai inganta ayyuka da tsare-tsare da ake gudanarwa a muhimman fannoni irin su ilimi, kiwon lafiya, ababen more rayuwa, noma da sauran muhimman ayyukan ci gaba.
Sagir ya ƙara da cewa, za a mika ƙarin kasafin kuɗin ga Majalisar Dokokin Jihar domin tattaunawa da amincewa da shi, kamar yadda kundin tsarin mulki da ka’idojin kasafi suka tanada.
Kwamishinan ya ƙara jaddada cewa, wannan mataki ya nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen gudanar da mulki bisa gaskiya da adalci, da kula da kuɗaɗen jama’a yadda ya dace, da kuma tabbatar da samar da ingantattun ayyuka ga al’ummar jihar baki ɗaya.
Usman Muhammad Zaria