’Yan sanda sun kama ɗan bindiga da shanu 10 a Kebbi
Published: 3rd, September 2025 GMT
Rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi ta cafke wani ɗan bindiga da ake zargin ɗan ƙungiyar Lukurawa ne tare da shanu goma da ya sato, a wani samame da aka kai kasuwar shanu ta Bachaka.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Nafi’u Abubakar, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata.
A cewarsa, “bayan samun sahihan bayanan sirri, an kama wani Salihu Umar, mai shekaru 42, ɗan asalin Dogon Dutse a Jamhuriyar Nijar, wanda ya shiga kasuwar shanu ta Bachaka da shanu 10 da ya sace wa wani Usman Aliyu na garin Zogirma a Ƙaramar Hukumar Bunza.”
Ya ce shanun na daga cikin guda 68 da ake zargin ’yan bindigar Lukurawa sun sace sannan suka tsallaka da su zuwa Nijar a ranar 20 ga watan Agusta.
Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Kebbi, CP Bello M. Sani, ya jinjina wa DPO na Bachaka da tawagarsa bisa wannan nasara, yana mai kira gare da su ƙara jajircewa wajen kare al’umma.
Kwamishinan ya kuma jaddada cewa rundunar za ta ƙara ƙaimi wajen cafke duk mambobin ƙungiyar tare da ƙwato sauran shanun da aka sace.
Ya roƙi al’ummar jihar da su kasance masu lura da gaggauta bayar da bayanai kan duk wani motsi da ba su aminta da shi ba zuwa jami’an tsaro mafi kusa domin daƙile ayyukan ’yan ta’adda.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ɗan Bindiga Jihar Kebbi Lakurawa
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Gabatar Da Sabbin Kayayyaki Guda 5 A Wajen Taron Kolin kere-kere .
Rahotanni sun bayyana cewa kasar iran ta bayyana sabbin kayayyaki guda 5 da ta kera a wajen babban taron kere-kere na kasa da kasa karo na 23,kuma dukkansu kamfanonin kasar iran ne suka yi su domin rage dogaro da kayyakin kasashen waje.
Taron ya samu halartar mataimakin shugaban hukumar kula da kimiya da fasaha ta kasa da sauran shuwagabannin kamfanoni inda ya nuna irin karfin iran wajen kere-kere da kuma mayar da hankali kan kamfanoni dake filin shakatawa na pardis technology park.
Daga cikin magungunan da aka gabatar a wajen akwai Sirolimus wanda Zist takhmir company ya kera, kuma magungunan rigakafi ne da ake amfani da su wajen hana dashen gabobin jiki da kuma kula da cututtuka da ba kasafai ake samun su ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta Bukaci IAEA Tayi Tir Da Harin Da Isra’ila Ta Kai A Tashoshin Nukiyarta. September 16, 2025 Jonathan Zai Jagoranci Taron Tattaunawa Kan Dimokuraɗiyya A Ghana September 16, 2025 Pezeshkian: Saudiyya Na Iya Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Samar Da Hadin Kan Kasashen Musulmi September 16, 2025 Pezeshkian: Ta’addancin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Kan Kasar Qatar Zalunci Ne Ga Diflomasiyya September 16, 2025 Baqa’i: Kowace Kasa A Duniya Tana Da Hakkin Mallakar Makamashin Nukiliya Na Zaman Lafiya September 16, 2025 Kungiyar Human Rights Watch; Isra’ila Ta Kashe ‘Yan Jarida Fiye Da 30 A Kasar Yemen Ne Da Gangan September 16, 2025 Kungiyar Kare Hakkokin Bil’Adama Ta Siriya Ta Bankado Karin Fararen Hula Da Aka Kashe A Rikicin Suweida September 16, 2025 Tawagar Yan Wasan Damben Gargajiya Ta Iran Ta Zama Zakara A Damben Ta Duniya September 16, 2025 An Fara Taron Hukumar Makamashin Nukliya Ta Duniya IAEA Karo Na 69 A Birnin Vienna September 16, 2025 Espania Ta Soke Cinikin Makamai Na EUR Miliyon 700 Da HKI Saboda Kissan Kiyashi A Gaza September 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci