Ƙungiyar masu kafafen yada labarai na Arewa za ta daukaka kara kan hukuncin kotu a kan tashar Arewa24
Published: 3rd, September 2025 GMT
Ƙungiyar masu kafafen yaɗa labarai ta Arewacin Najeriya (NBMOA) ta yi watsi da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke na yin watsi da ƙarar da ta shigar a kan tashar Arewa24, inda ta ce za ta ɗaukaka ƙara.
Idan za a iya tunawa, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, a watan Agusta, ta yi watsi da karar da kungiyar NBMOA ta shigar a kan Arewa24, saboda “rashin hukunci da rashin cancanta”, kamar yadda aka gani a cikin kwafin takardar hukuncin kotun (CTC).
Kotun, a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta tabbatar da cewa AREWA24 tana gudanar da harkokinta ne bisa ƙa’ida, kuma ba ta da hurumin samun ƙarin lasisin gudanar da ayyukanta, ba tare da karya wata doka ba.
Sai dai, Shugaban NBMOA, Alhaji Ahmed Tijjani Ramalan, a cikin wata sanarwar da ya raba wa manema labarai a ranar Talata, ya bayyana hukuncin da alƙalin kotun, Mai Shari’a Omotosho ya yanke da cewa ya zama tamkar “halatta tashoshin ƙasashen waje marasa lasisi”, wanda ya yi musu laƙabi da matsayin ‘kaska’, a masana’antar yaɗa labarai ta Najeriya”.
Ƙungiyar ta dage cewa, Arewa24 tashar talabijin mallakar Amurka, wacce ke da ofisoshi a Kano da Legas, na watsawa da yaɗa shirye-shiryenta da wasannin kwaikwayo na Hausa, wanda ake yi wa laƙabi da shirye-shiryen duniya, ana shigo da su zuwa gidajen talabijn na Najeriya ta DStv, GOtv da StarTimes.
A cewar ƙungiyar, duk shirye -shiryen da tashar take watsawa ba ta da lasisi da Hukumar Kula da Kafafen Watsa Labarai ta Ƙasa (NBC).
Kungiyar ta kuma ce tashar tana cajin kuɗin tallace-tallace ba bisa ƙa’ida ba, baya ga farashin da suke caza da ya zarce tunani, kuma ya keta wajibcin da aka sanya wa masu watsa shirye-shiryen gida.
NBMOA ta kuma zargi AREWA24 da watsa shirye-shirye da basu dace ba, tana mai gargaɗin cewa hukuncin da kotun ta yanke zai bai wa tashar damar ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen da suke lalata tsarin Gwamnatin Tarayya, tare da yin barazana ga tashoshin cikin-gida, wanda ke fama da ƙasa mai tsanani.
Ta ƙara da cewa ana tilasta wa masu watsa shirye-shirye na asali, waɗanda ke bin doka, barin kasuwanci.
Ƙungiyar tace wannan hukuncin ya halatta kafafen yaɗa labarai na ƙasashen waje da basu da lasisi su riƙa yaɗa shirye-shiryen da suka ci karo da al’adunmu, da ɗabi’un al’umman ƴan Arewa.
“Ba za mu tsaya haka kawai ba yayin da tashohin ƙasashen waje ke yin katsalandan a harkar yaɗa labarai, da kuma lalata masana’antarmu,” in ji Ramalan.
Tuni dai Ƙungiyar NBMOA ta shigar da ƙara a Kotun Ɗaukaka ƙara da ke Abuja, inda ta buƙaci da a yi mata adalci, inda kuma ta nemi da a soke hukuncin da waccan kotu ta zartar don tabbatar da adalci.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Arewa 24 shirye shiryen yaɗa labarai shirye shirye
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar
Daga Usman Muhammad Zaria
Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da bayar da rancen kudi ga hukumar gidaje ta jihar domin gina gidaje 52 a Dutse.
A cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ya fitar, ya bayyana cewa gidajen za su kunshi masu dakuna uku da kuma dakuna biyu kowanne.
Ya ce aikin zai kasance a gaban tsohuwar unguwar majalisar dokoki, kusa da hanyar wucewa ta Jami’ar Tarayya da je Dutse, a matsayin wani shiri na asusun gina gidaje karkashin ma’aikatar gidaje, ci gaban birane da tsare-tsaren yankuna, ta hannun hukumar gidaje ta jihar.
Alhaji Sagir ya bayyana cewa, wannan mataki na nuna kudirin gwamnati wajen magance matsalar gidaje a babban birnin jihar, kara habaka ci gaban birane, tare da samar da ayyukan yi ga matasan jihar.
Ya ce an tsara wannan asusu ne domin tabbatar da dorewa, ta yadda za a ci gaba da zuba jari a ayyukan samar da gidaje masu araha a fadin jihar.
Haka kuma ya kara da cewa, gwamnatin jihar tana da kudirin ci gaba da inganta rayuwar al’ummarta, ta hanyar ayyuka masu amfani da jama’a, da ke inganta walwala, karfafa tattalin arziki, da tallafa wa matasa.
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa, majalisar ta amince da bayar da kwangilar gyara da inganta gidan baki guda biyu (Malam Adamu Chiroma House da kuma Senator Francis Ella House) da ke cikin G9 Quarters a Dutse, da kudin sama da naira miliyan 219.7.
Ya ce aikin zai haɗa da cikakken gyara da inganta gine-ginen, gyaran hanyoyin ruwa da kuma girka tankokin ruwa ga kowanne daga cikin gidajen biyu.
Ya ce hakan na da nufin tabbatar da wadataccen ruwan sha mai dorewa a wuraren.
Alhaji Sagir Musa Ahmed ya kara da cewa, amincewar da aka yi da wannan kwangila na nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen kula da dukiyar jama’a da kuma tabbatar da cewa gine-ginen gwamnati suna cikin yanayi mai kyau da nagarta.