’Yan sa-kai sun hallaka ’yan bindiga 7 a Katsina
Published: 6th, September 2025 GMT
Rahotanni sun tabbatar da cewa ’yan bindiga bakwai sun mutu a wani hari da suka kai ƙauyen Magajin Wando da ke Ƙaramar Hukumar Ɗandume, a Jihar Katsina.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na daren ranar Juma’a, lokacin da maharan suka afka wa ƙauyen.
Mauludi: Ƙungiyoyin addini sun nemi gwamnati ta sassauta dokar hana hawa babur a Gombe Yadda makarantu ke tatsar kuɗaɗe daga iyayen ɗalibaiKwamishinan tsaro na jihar, Dokta Nasiru Mu’azu Danmusa, ya ce jami’an tsaron al’umma na Community Watch Corps (CWC) sun yi artabu da maharan, inda suka daƙile harin.
A yayin arangamar, maharan sun ƙone motar jami’an tsaron, amma duk da haka, jami’an sun samu nasarar fatattakar su.
Danmusa, ya bayyana cewa, rahotanni sun nuna cewa wannan hari ramuwar gayya ne, bayan kashe wasu mahara a wani hari da suka kai Magajin Wando.
Ya yaba wa jami’an wajen kare al’umma, tare da miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda abin ya shafa.
Kwamishinan ya ƙara da cewa gwamnatin jihar na aiki tare da sojoji, ’yan sanda da sauran jami’an tsaro domin kamo waɗanda suka aikata wannan ta’asa.
Haka kuma ya roƙi jama’a su ci gaba da bayar da rahoton motsin ’yan bindiga.
Hakazalika, ya jaddada cewa gwamnatin ci gaba da ƙoƙari wajen kare rayukan al’umma a jihar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga hari Jami an Tsaro mahara
এছাড়াও পড়ুন:
An kama mabaraci da kuɗaɗen ƙasar waje a Ilorin
Hukumar jin daɗin jama’a ta Jihar Kwara tare da haɗin gwiwar Hukumar Gyaran Hali ta Najeriya sun kama wasu mabarata a titunan Ilorin, ciki har da wasu da aka samu da kuɗaɗen ƙasashen waje.
Daga cikin waɗanda aka kama akwai wani mabaraci mai suna Musa Mahmud daga Jihar Kano, wanda aka samu da takardar daloli.
Musa Mahmud ya shaida wa manema labarai cewa wani ne ya ba shi takardar Dala a Abuja.
Jami’ai sun bayyana damuwa kan yadda masu bara ke riƙe da kuɗaɗen da ba su dace da yanayin rayuwarsu ba.
Mutuwar majinyata: Asibitin Aminu Kano na roƙon KEDCO ya dawo da wutar lantarki Cire tallafin man fetur shi ne abin da ya dace —Sarki Sanusi II“Za mu bincika asalin waɗannan kuɗaɗen da kuma dalilin da ya sa suke da su,” in ji Adebayo Okunola, shugaban cibiyar gyaran hali a Jihar Kwara.
Jami’an gwamnati sun kwashe kusan mutane 40 daga wuraren da suka haɗa da Tipper Garage, Offa Garage, Tank da Geri Alimi Roundabout.
Jami’an sun ce bakwai daga cikin waɗanda aka kama an taɓa kama su a baya, amma sun koma tituna bayan an sako su.
Kwamishinar jin daɗin jama’a ta jihar, Dakta Mariam Imam, ta ce adadin masu bara da aka kama ya ragu sosai idan aka kwatanta da na baya, inda ta ce suna sauya dabaru don su guje wa kama.
Ta roƙi jama’a da su daina ba wa masu bara kuɗi kai tsaye, su maida gudummawarsu ta hanyar wuraren ibada da gidajen marayu.
Jami’an gyaran hali sun ce za a tilasta wa waɗanda aka kama su yi aikin tsaftace tituna a matsayin horo da kuma darasi.
Wasu daga cikin masu barar sun roƙi gwamnati da ta tausaya musu, ba su da wata hanyar rayuwa sai bara.