Aminiya:
2025-11-02@15:25:04 GMT

Tsohon mataimakin Gwamnan Gombe da wasu jiga-jigai sun fice daga PDP zuwa APC

Published: 5th, September 2025 GMT

An samu sauyi a siyasar Jihar Gombe, yayin da tsohon mataimakin gwamnan jihar, Mista Tha’anda Jason Rubainu, tare da babban jigon jam’iyyar PDP, Mista Jerry Damara, suka sauya sheƙa zuwa APC.

Rubainu, wanda ya yi mataimakin gwamna a ƙarƙashin tsohon gwamnan jihar, Ibrahim Hassan Dankwambo daga 2011 zuwa 2015, ya hada kai da Damara da kuma wasu manyan ’ya’yan jam’iyyar PDP daga yankin Kuancin Gombe.

Mauludi: ’Yan sanda sun haramta hawa babur da daddare a Gombe Gwamnatin Yobe za ta ɗauki nauyin jinyar Malam Nata’ala

Yayin da yake miƙa katin shaidar shigarsa APC ga Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, Mista Damara, wanda shi ne shugaban Mesotho Group Limited, ya ce dalilin sauya sheƙarsu shi ne kyawawan ayyukan raya ƙasa da gwamnan ya gudanar a fannoni daban-daban.

“A matsayina na wanda ke harkar gine-gine, na san muhimmancin shiga harkokin ci gaban al’umma.

“Ranka ya daɗe, ka yi ƙoƙari wajen gina Gombe don amfanin kowa,” in ji Damara.

Gwamna Inuwa, ya bayyana wannan sauya sheƙa a matsayin babban ci gaba ga siyasar jihar da ƙasa baki ɗaya.

“Wannan lokaci ne mai muhimmanci a gare mu domin yana nuna babu sauran jam’iyyar hamayya a jihar. Mun karya ƙashin bayan adawa a Gombe,” in ji gwamnan.

Wannan sauya sheƙa na zuwa ne a lokacin da dama daga cikin manyan jiga-jigan PDP suka bar jam’iyyar a ’yan watannin baya.

Hakan ya ƙara wa jam’iyyar APC ƙarfi a jihar yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Damara Siyasa Tsohon Mataimakin Gwamna

এছাড়াও পড়ুন:

 Gaza: Daga Tsagaita Wuta Zuwa Yanzu Fiye Da Mutane 200 Ne Su Ka Yi Shahada

Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta sanar da cewa daga lokacin da aka tsayar da wuta zuwa yanzu adadin Falasdinawan da HKI ta kashe sun kai 200, yayin da wasu  kusan 600 sun jikkata.

Sanarwar ta ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta kuma ci gaba da cewa; A cikin sa’o’i 48 da su ka gabata,an sami shahidai 22, biyar daga cikinsu basu dade da yin shahada ba, sai kuma 17 da aka tono su daga karkashin baraguzai. Haka nan kuma na kai wasu 9 zuwa asibitocin da suke a yankin.

Wani sashe na sanarwar ma’aikatar kiwon lafiyar ta Gaza ya ce, har yanzu da akwai shahdai masu yawa da suke a karkashin baraguzai, wasu kuma a kan hanyoyi, saboda rashin kayan aiki da kungiyoyin agaji za su yi amfani da su.

Tun daga ranar 7 ga watan Oktoba na 2023 zuwa yanzu, adadin shahidai ya kai 68,858, sai kuma wani adadin da ya kai 170,664 da su ka jikkata.

Amma daga tsayar da wuta a ranar 11 ga watan Oktoba zuwa yanzu, an sami shahidai da sun kai 226, sai kuma wasu 594 da su ka jikkata. Haka nan kuma an iya tsamo gawawwakin shahidai daga cikin baraguzai har su 499.

Haka nan kuma ma’aikatar kiwon lafiyar tra sanar da karbar gawawwaki 30 da HKI ta mika wa bangaren Falasdinawa ta hannun hukumar agaji ta “Red-Corss.

Tun bayan tsagaita wutar yaki, har ya zuwa yanzu dai HKI tana ci gaba da kai hare-hare a sassa daban-daban na Gaza.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shugaban Kasar Najeriya Ya Mayar Da Martani Ga Takwaransa Na Amurka Akan Rikicin Addini November 1, 2025 Iran ta damu da halin da ake ciki a yankin El Fasher na Sudan November 1, 2025 Kwamitin Tsaron MDD ya goyi bayan shirin Morocco game da yankin Yammacin Sahara November 1, 2025 Samia Suluhu Hassan ta lashe zaben shugaban kasa a Tanzaniya November 1, 2025 Najeriya ta musanta ikirarin Trump, na cewa Kristoci na fuskantar babbar barazana a kasar November 1, 2025 Majalisar Dinkin Duniya ta damu da hare-haren Amurka a Caribbean da Pacific November 1, 2025 Israila Ta Kai Hari  Kan Ofishin kungiyar UNICEF Dake Gaza A November 1, 2025 Amurka Na Shirin Kai Hari Kan Kasar Venzuwela A Kowanne Lokaci November 1, 2025 Iran Ta Sanya  Da Ranar 30 Ga Watan Nuwamba A Matsayin Ranar Kasa Ta Tsibirai 3 October 31, 2025 Isra’ila Na Ci Gaba Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza October 31, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  •  Gaza: Daga Tsagaita Wuta Zuwa Yanzu Fiye Da Mutane 200 Ne Su Ka Yi Shahada
  • PDP ta dakatar da Anyanwu da wasu ’yan tsagin Wike
  • PDP ta dakatar da Anyanwu da wasu da ke da alaƙa da Wike
  • Gwamna Uba Sani Ya Bayyana Tsare-tsaren Ci Gaban Kaduna a Taron Duniya a Dubai.
  • Sanata Sunday Marshall Katung Ya Sauya Sheka Zuwa Jam’iyyar APC
  • An yi garkuwa da Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Kebbi
  • Kotu ta tsige dan majalisar da ya sauya sheka zuwa APC
  • Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar
  • Juventus ta ɗauki tsohon kociyan Italiya, Luciano Spalleti
  • Borno ta fara fitar da kayan robobi zuwa ƙasashen waje – Zulum