NNPP ta kori Kofa daga jam’iyyar, ta yi barazanar maka shi a kotu
Published: 6th, September 2025 GMT
Jam’iyyar NNPP ta Jihar Kano, ta kori Abdulmumin Jibrin Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Kiru/Bebeji.
Jam’iyyar ta zarge shi da yi mata zagon ƙasa da kuma gaza biyan kuɗaɗen da ake binsa.
’Yan bindiga sun kashe jami’an NSCDC 8, sun sace ɗan China a Edo APC ta yi barazanar hukunta “Yaran Badaru” a JigawaShugaban NNPP na jihar, Hashim Sulaiman Dungurawa ne, ya bayyana haka ranar Asabar a Kano.
Ya ce Jibrin ya daɗe yana fitowa a kafafen watsa labarai yana zagin jam’iyya da shugabanninta.
Wannan na zuwa ne kwana ɗaya bayan da Kofa, ya ce zai iya barin NNPP, inda ya ce yana da ƙwarewar da zai iya yanke shawara kan makomar siyasarsa.
Dungurawa, ya ce Kofa ba shi da ƙarfin da zsi iya lashe zaɓe a ƙashin kansa ba don darakar Kwankwasiyya da NNPP ba.
Ya ce a baya Kofa ya kasa samun nasara lokacin da ya yi takara a jam’iyyar APC.
Shugaban ya ƙara da cewa an kafa kwamitin sulhu domin yin sulhu da shi bayan hirar da ya yi a gidan talabijin na Channels.
A cewarsa daga baya Kofa ya ci gaba da fitowa a kafafen yaɗa labarai yana biyayya ga wasu da ba ’yan jam’iyyar ba.
“Saboda haka mun kore shi. Ba shi da wani abin da zai ƙara wa jam’iyya,” in ji Dungurawa.
Haka kuma, ya zargi Kofa da ƙin biyan kuɗin da jam’iyya ta wajabta, inda ya ce za su kai shi kotu domin karɓo haƙƙinsu.
Kan jita-jitar Kofa na iya komawa APC, Dungurawa, ya ce hakan ba zai rage wa NNPP ƙarfi ba.
Ya jaddada cewa siyasa tana tafiya da ƙungiyoyi, kuma Kwankwasiyya na nan daram ƙarƙashin jagorancin Rabiu Musa Kwankwaso.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: hira Kora Kwankwasiyya Siyasa zargi
এছাড়াও পড়ুন:
Barazanar Amurka Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya: Tinubu Da Trump Za Su Gana Kwanan Nan — Bwala
Da yake mayar da martani ga wannan zargin na Amurka, Bwala ya ce gwamnatin Tinubu tana jajircewa wajen kare dukkan ‘yan Nijeriya ba tare da la’akari da addini ba, yana mai cewa Amurka da Nijeriya sun dade suna hadin gwiwa a yaki da ta’addanci.
“Shugaba Bola Tinubu da Shugaba Donald Trump suna da kudiri iri ɗaya a yaƙi da ta’addanci da duk wani nau’in ta’addanci a kan bil’adama,” in ji Bwala.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA