Aminiya:
2025-09-17@23:21:51 GMT

Harin Boko Haram: Zulum ya kai ziyarar jaje garin Darajamal

Published: 7th, September 2025 GMT

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ziyarci garin Darajamal da ke Ƙaramar Hukumar Bama, domin jajanta wa iyalan mutanen da Boko Haram suka kashe.

Rahotanni sun nuna cewa ’yan ta’addan Boko Haram sun hallaka aƙalla mutum 63, yayin da dakarun soja suka kashe 30 daga cikinsu.

Tsadar Rayuwa: NLC ta buƙaci gwamnati ta sake duba albashin ma’aikata Najeriya ce ƙasa ta biyar mafi yawan Musulmai a duniya

Da yake magana da mazauna garin Zulum ya ce: “Abin takaici ne sosai.

An dawo da wannan al’umma nan ba daɗewa, amma sai ga shi an sake fuskantar mummunan hari a daren jiya.”

Gwamnan ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ƙara ƙarfafa jami’an tsaro a dazuka, inda ya bayyana cewa akwai buƙatar ƙara yawan sojoji domin kare rayukan jama’a yadda ya kamata.

Idan ba a manta Aminiya ta ruwaito yadda maharan suka farmaki ƙauyen, inda suka kashe gomman mutane.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: hari Ƙauye

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Kano Ta Inganta Cibiyoyin Horas Da Sana’o’i Domin Dakile Aikata Laifuka Tsakanin Matasa

Gwamnatin Kano ta raba kayayyakin aiki na zamani na kimanin Naira Miliyan 250  ga cibiyoyin horas da sana’o’in hannu biyu da ke Kofar Mata da Gwale, domin yaƙi da shan miyagun kwayoyi da aikata laifuffuka a tsakanin matasa, ta hanyar samar da aikin yi.

Kwamishinan Kimiyya da Fasaha, Dakta Yusuf Kofarmata, ya ce an amince da tallafin ne bisa umarnin Gwamna Abba Kabir Yusuf don bunƙasa tsare-tsaren ƙarfafa matasa a jihar.

Ya bayyana cewa an samar da injinan sarrafa fata guda 26 domin cibiyoyin wadanda al’ummar yankunan suka kafa, amma ba su da isassun kayayyakin aiki.

Ya ce Gwamna Yusuf ne ya gina Cibiyar Horaswar ta Gwale  kasancewar nan ce mazabarsa, yayin da Dakta Yakubu Adam ya taka rawa wajen gina ta Kofar-Mata.

Ya ce cibiyoyin za su samar da daruruwan ayyukan yi tare da rage matsalolin zaman kashe-wando da ta’addanci a tsakanin matasa.

 

A nasa jawabin, Ali Musa Kofar-Mata na ƙungiyar IKMA ya gode wa gwamnati bisa wannan gudummawar da ya kira mai sauya rayuwa.

Ya ce cibiyar ta fara ɗaukar matasa maza da mata, kuma horon zai ɗauki watanni uku kafin a shiga sabon zagaye.

 

Abdullahi Jalaluddeen 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnati ta ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani 20 a Sakkwato
  • Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ta Kammala Ziyarar Yini 3 A Ma’aikatar Kananan Hukumomin Jihar
  • Al’ajabi: Yadda Aka Shirya Bikin Haihuwar ‘Ya’yan Awaki Biyar A Garin Dakasoye
  • Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
  • Gwamnatin Kano Ta Inganta Cibiyoyin Horas Da Sana’o’i Domin Dakile Aikata Laifuka Tsakanin Matasa
  • Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno
  • ’Yan ‘Mafiya’ na ƙoƙarin kashe matatar man fetur da na gina —Ɗangote
  • Ɗan Majalisar Tarayya Ya Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-haren Ta’addanci A Sakkwato 
  • An kama tsohon minista kan zargin kisan kai domin tsafi a Nijar
  • Dole sai mun tantance wa’azi kafin a yi —Gwamnan Neja