Gwamnati Ta Kaddamar Da Sabbin Darussan Karatu A Makarantun Nijeriya
Published: 7th, September 2025 GMT
A jawabin ‘yan jaridu wanda darekta na bangaren manema labarai da al’amuran da suka shafi jama’a na ma’aikatar ilimi ta tarayya Folasade Boriowo, abin ya bayyana; “A sashen Firamare , ‘yan aji 1- 3 za su byi darussa 9–10, su kuma wadanda suke aji 4–6 zasu yi darussa 10–12.Sai bagaren karamar Sakandare, abin ya fara ne daga darussa 12–14; Babbar Sakandare kuma dalibanta za su yi darussa 8–9; yayin da su kuma fannin fasaha za su yi darussa 9–11.
Ahmad ya bayyana manhajar an tsara ta ne saboda an rage abubuwan da ta kunsa, aka kara maida hankali ga koyo domin tabbatar da cewa lamarin da ya shafi ilimi ya ci gaba da zama yana tafiya daidai zamanin da ake ciki yanzu a fadin duniya gaba daya.
Ma’aikatar ta jinjinawa masu ruwa da tsaki akan irin maida hankalin da suka yi, aka kuma kara jaddada cewa shi lamarin sabon tsarin darussa za’a tabbatar da an bi shi kamar yadda yadda yake, da kuma tabbatar da an yi amfani da shi a fadin tarayyar Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Ta Kama Bisa Kuskuren Safarar Ƙwayoyi
Hukumar NDLEA ta bayyana cewa wata ƙungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi ce a filin jirgin sama na Kano ta boye jakunkunan ƙwayoyi a cikin kayan matafiyan.
An kama shugaban ƙungiyar, Ali Abubakar Mohammed (wanda aka fi sani da Bello Karama), tare da wasu abokan aikinsa.
Hukumar ta ce mutanen ukun ba su da laifi kuma an zalunce su ne kawai.
An saki su ne bayan bincike da kuma ƙoƙarin diflomasiyya na tsawon makonni.
Lamarin ya tayar da hankali kan tsaro a filayen jirgin sama a Nijeriya da yadda masu aikata laifuka ke amfani da fasinjoji marasa laifi.
Hukumar ta ce za a ɗauki ƙarin matakai don hana faruwar irin wannan lamari.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp