An haramta wa makarantu tilasta wa iyaye sayen sabbin litattafai duk shekara a Filato
Published: 6th, September 2025 GMT
Majalisar Dokokin Jihar Filato, ta haramta wa makarantu a jihar tilasta iyayen ɗalibai sayen sabbin littattafai duk shekara.
Wannan mataki ya biyo bayan ƙudurin da Hon. Joseph Bukar, ɗan majalisa mai wakiltar Shendam ya gabatar, tare da goyon bayan Hon. Mathew Kwarpo Sylvanus daga Mangu ta Kudu.
Sarkin Zazzau ya jagoranci jama’a domin murnar Maulidin bana Gwamnatin Sakkwato ta bai wa ’yan gudun hijira tallafin kuɗi da shinkafaBukar, ya ce bai dace ba a ci gaba da tilasta wa iyaye siyan sabbin littattafai duk shekara, inda ya ce hakan cin zarafi ne.
’Yan majalisar sun ce wannan mataki zai rage wa iyaye nauyin kashe kudi.
Sun bayyana cewa ana iya sake amfani da littattafai, har ma a raba wa ’yan uwa da abokan arziƙi.
Majalisar ta amince da cewa:
1. Iyaye su samu ’yancin sayen littattafai daga ko ina, ba dole sai a makarantu ba.
2. An riƙa amfani da littattafai aƙalla shekaru huɗu, kamar yadda ake yi a jihohin Edo da Imo.
3. Makarantu da ƙungiyoyin iyayen ɗalibai su kafa bankin littattafai da tsarin musayar littattafai domin rage kashe kuɗi.
Majalisar ta kuma yi Allah-wadai da al’adar yin bikin kammala makaranta a matakin firamare da ajin ’yan yara.
Ta bayyana cewa hakan ɓata lokaci da kuɗi ne, kuma ba shi da amfani ga ilimi.
Domin tabbatar da bin dokar, majalisar ta umarci kwamitin ilimi da ya kira shugabannin makarantu masu zaman kansu tare da jami’an ma’aikatar ilimi, don sanar da wannan matsaya.
An kuma gargaɗi makarantu cewa duk wanda ya saɓa wa wannan umarni za a hukunta shi.
Hakazalika, majalisar ta tattauna kan matsalar dillalan gidaje waɗanda ba su lasisi.
’Yan majalisar sun koka da yadda ake cutar da jama’a ta hanyar tatsarsu maƙudan kuɗaɗe.
Don haka, an amince da haramta ayyukan dillalai waɗanda ba su da lasisi tare da samar da sabon tsari domin maye gurbin tsohuwar dokar haya.
Kakakin majalisar, Rt. Hon. Naanlong Daniel, ya yaba wa ’yan majalisar bisa gudunmawarsu, tare da tabbatar da cewa majalisar za ta ci gaba da samar da dokoki da za su kawo sauƙi da ci gaban al’ummar Filato.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ɗalibai iyaye Majalisar Dokoki makarantu majalisar ta
এছাড়াও পড়ুন: