Aminiya:
2025-09-17@21:51:06 GMT

Tsohon mataimakin Gwamnan Gombe da wasu jiga-jiga sun fice daga PDP zuwa APC

Published: 5th, September 2025 GMT

An samu sauyi a siyasar Jihar Gombe, yayin da tsohon mataimakin gwamnan jihar, Mista Tha’anda Jason Rubainu, tare da babban jigon jam’iyyar PDP, Mista Jerry Damara, suka sauya sheƙa zuwa APC.

Rubainu, wanda ya yi mataimakin gwamna a ƙarƙashin tsohon gwamnan jihar, Ibrahim Hassan Dankwambo daga 2011 zuwa 2015, ya hada kai da Damara da kuma wasu manyan ’ya’yan jam’iyyar PDP daga yankin Kuancin Gombe.

Mauludi: ’Yan sanda sun haramta hawa babur da daddare a Gombe Gwamnatin Yobe za ta ɗauki nauyin jinyar Malam Nata’ala

Yayin da yake miƙa katin shaidar shigarsa APC ga Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, Mista Damara, wanda shi ne shugaban Mesotho Group Limited, ya ce dalilin sauya sheƙarsu shi ne kyawawan ayyukan raya ƙasa da gwamnan ya gudanar a fannoni daban-daban.

“A matsayina na wanda ke harkar gine-gine, na san muhimmancin shiga harkokin ci gaban al’umma.

“Ranka ya daɗe, ka yi ƙoƙari wajen gina Gombe don amfanin kowa,” in ji Damara.

Gwamna Inuwa, ya bayyana wannan sauya sheƙa a matsayin babban ci gaba ga siyasar jihar da ƙasa baki ɗaya.

“Wannan lokaci ne mai muhimmanci a gare mu domin yana nuna babu sauran jam’iyyar hamayya a jihar. Mun karya ƙashin bayan adawa a Gombe,” in ji gwamnan.

Wannan sauya sheƙa na zuwa ne a lokacin da dama daga cikin manyan jiga-jigan PDP suka bar jam’iyyar a ’yan watannin baya.

Hakan ya ƙara wa jam’iyyar APC ƙarfi a jihar yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Damara Siyasa Tsohon Mataimakin Gwamna

এছাড়াও পড়ুন:

Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ta Kammala Ziyarar Yini 3 A Ma’aikatar Kananan Hukumomin Jihar

Kwamatin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa ya bukaci ma’aikatar kananan hukumomi da ta karfafa matakan yiwa kananan hukumomin jihar 27 jagoranci akan sha’anin mulki da harkokin kudi domin inganta ayyukan su.

Shugaban Kwamatin, Alhaji Aminu Zakari ya yi wannan kiran a karshen ziyarar kwanaki 3 da kwamatin ya yi a ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar a Dutse.

Alhaji Aminu Zakari wanda shi ne wakilin mazabar Gwiwa a majalisar dokokin jihar Jigawa, ya ce ziyarar kwamatin na da nufin tantance yadda ma’aikatar ta ke gudanar da ayyukan ta, ta fuskar harkokin mulki da na kudi da kuma dangantakar aiki tsakanin ta da kananan hukumomin jihar 27 kamar yadda tsarin mulki ya dorawa majalisa nauyi.

A nasa jawabin, mataimakin shugaban Kwamatin kuma wakilin mazabar Kaugama, Alhaji Sani Sale Zaburan ya bayyana bukatar ganin jami’an ma’aikatar da ke kula da kananan hukumomi a shiyya shiyya suna gudanar da ayyukan su ba tare da jingina da shugabannin kananan hukumomi ba a ko da yaushe amma Kuma su na yiwa kananan hukumomin jagoranci wajen gudanar da sha’anin mulki da harkokin Kudi kamar yadda ya kamata.

Daya daga cikin ‘yan kwamatin Malam Ibrahim Sabo Ahmad Roni ya duba kundin bayanan sha’anin mulki yayin da Oditoci su ka duba kundin bayanan harkokin Kudi tare da yabawa da kuma bada shawarwari da za su inganta ayyukan ma’aikatar.

Da ya ke mayar da jawabi, kwamishinan ma’aikatar kananan hukumomi Alhaji Ibrahim Garba Hannun Giwa wanda Babban Sakatare na maikatar ya wakilce shi, Alhaji Muhammad Yusha’u ya ce ma’aikatar ce ke uwa da makarbiya wajen yiwa kananan hukumomi jagoranci a sha’anin mulki da harkokin Kudi da zamantakewa domin kawo cigaba a yankunan karkara.

Kazalika, a daya bangaren kuma, karamin Kwamatin da Babban Kwamatin kananan hukumomi na majalisar Dokokin jihar Jigawa ya kafa bisa jagorancin wakilin mazabar Kiyawa Alhaji Yahaya Muhammad Andaza domin duba aikin gyaran gidajen kananan hukumomin jihar 27 da ke kan titin Bypass a Dutse ya mika rahoton sa ga babban kwamatin.

Alhaji Yahaya Muhammad Andaza Wanda sakataren Kwamatin Alhaji Yusha’u Muhammad ya wakilta, ya ce karamin Kwamatin ya duba gidajen Inda ya dauki samfur din yanayin da su ke ciki.

Ya ce daga cikin gidajen akwai wadda ke funskatar matsaloli kamar na tsagewar bango da sanya darduma da kujeru da kayan amfani a dakin girki marasa inganci yayin da ba a mayar da na’urar sanyaya daki a wasu gidajen ba.

Yusha’u wanda shi ne mataimakin Akawun majalisar, ya lura cewa akwai rashin kyawun flasta a wasu gidajen yayin da kan dakin wasu ke yayyo sai Kuma rashin fankar sama da karayyayun kujeru da rashin hada wasu gidajen da wutar lantarki mai amfani da hasken rana da rashin kyawun kofofi da magudanin ruwa da ke kawo barazanar ambaliyar ruwa ga wasu gidajen.

A nasa jawabin, shugaban Kwamatin kananan hukumomi na majalisar Dokokin jihar Jigawa Alhaji Aminu Zakari ya ja hankalin shugabannin kananan hukumomin jihar da su dauki nauyin cikakkiyar kulawa ga gidajen bisa la’akari da dinbin kudaden da aka kashe wajen gyara gidajen.

 

Usman Mohammed Zaria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnati ta ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani 20 a Sakkwato
  • Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ta Kammala Ziyarar Yini 3 A Ma’aikatar Kananan Hukumomin Jihar
  • An tattauna yadda za a inganta walwalar malamai a Gombe
  • Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
  • Lakurawa Sun Hallaka Jami’in Kwastam A Jihar Kebbi
  • Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC Na Nasarawa, Aliyu Barde, Ya Rasu
  • DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya
  • Kukan al’umma kan lalacewar hanyar Dukku
  • An kama tsohon minista kan zargin kisan kai domin tsafi a Nijar
  • Dole sai mun tantance wa’azi kafin a yi —Gwamnan Neja