Kemi Badenoch ta shiga tsaka mai wuya kan karatun likitanci
Published: 2nd, September 2025 GMT
’Yar Najeriya kuma Shugabar Jam’iyyar Conservative a Birtaniya, Kemi Badenoch, ta shiga tsaka mai wuya kan iƙirarinta na cewa Jami’ar Stanford ta ba ta gurbin karatun horon shiga likitanci bisa rangwamen kuɗi tun tana ’yar shekara 16.
An fara sanya alamar tambaya a kan iƙirarinta ne bayan da wani tsohon jami’in kula da ɗaukar ɗalibai a jami’ar mai suna Jon Reider, ya musanta iƙirarin na Kemi Badenoch, wadda ta yi kaurin suna wajen sukar ƙasarta ta haihuwa.
Kemi Badenoch ta yi iƙirari cewa ta samu gurbin ƙaramin tallafin kuɗi daga Jami’ar Stanford, amma rashin kuɗin iyayenta ya hana ta amfani da damar.
Sai dai Jon Reider, wanda a lokacin yake kula da ɗalibai daga ƙasashen waje da tallafin karatu a Stanford, ya ƙaryata ikirarin nata.
An kai wa tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami hari a Kebbi NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Da Mutane Zasu Bi Wajen Neman DiyyaYa ce: “Duk da cewa shekaru 30 sun shuɗe, amma tabbas da zan tunawa idan da mun taɓa ɗaukar wata ɗalibar Najeriya bisa wani tallafi — gaskiya ba mu yi ba,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa jami’ar ba ta ɗaukar ɗalibai bisa sakamakon SAT kaɗai, kuma ba ta bayar da tallafin ragin kuɗi ba; domin idan ɗalibi na bukatar $30,000 a shekara, ragi ba shi da amfani domin ba zai iya wucewa ba.
Haka kuma, ya ce bai taɓa samun umarnin sauke shawarar sa ba daga wani shugaba a jami’ar.
Masu suka daga cikin jam’iyyun Labour da Liberal Democrats sun buƙaci Badenoch da ta bayyana dalilin wannan iƙirarin, saboda haƙƙin jama’a ne su san gaskiya, musamman abin da ya shafi shugabar adawa.
Duk da wannan tirjiyar, Badenoch ta tsaya kan cewa ta samu tayin bisa ga sakamakon SAT ɗinta.
Ta ce: “Na tuna ranar da wasiƙun suka iso a gare ni — ba na da takardu yanzu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gurbin karatu Jami ar Stanford karatun likitanci
এছাড়াও পড়ুন:
Babu wani uzuri da za a yi wa sabbin hafsoshi kan matsalar tsaron Nijeriya — Tinubu
Shugaba Bola Tinubu ya nemi sabbin hafsoshin tsaron ƙasar su zage damtse domin magance duk wata barazanar tsaro da ake fuskanta a halin yanzu da ma wadda ka iya kunnowa nan gaba.
Shugaban ya gargadi sabbin hafsoshin tsaron cewa ’yan Nijeriya sakamako kawai suke buƙata, ba uzuri ba, saboda haka dole ne su cika aikin da aka ɗora musu.
Gwamnatin Gombe ta saurari ra’ayoyin jama’a kan kasafin kuɗin 2026 Ƙwallo ta kashe ɗan wasan CricketTinubu ya bayyana hakan ne bayan bikin ƙara wa sabbin hafsoshin tsaron da shugabannin rundunonin soji girma da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa yau Alhamis a Abuja.
A cewarsa, “Barazanar tsaro na ƙara sauyawa a kodayaushe, kuma abin da ya fi damun gwamnatinmu shi ne ɓullar sababbin ƙungiyoyin ’yan bindiga a Arewa ta Tsakiya, da Arewa maso Yamma, da wasu sassa a Kudanci.”
A ranar Laraba ce Majalisar Dattawa da ta Wakilai suka amince da naɗin Laftanar Janar Olufemi Oluyede a matsayin Babban Hafsan Tsaro; Manjo Janar Waidi Shaibu a matsayin Hafsan Sojan Ƙasa; Rear Admiral Idi Abbas Hafsan Sojan Ruwa; Air Marshall Kennedy Aneke Hafsan Sojan Sama; da Manjo Janar Emmanuel Undiendeye a matsayin Shugaban Tattara Bayanai na Soja.
“Ba zai yiwu mu ƙyale wannan sabuwar barazanar ta ci gaba ba. Dole ne mu ɗauki mataki da wuri. Mu sare kan macijin.
“’Yan Najeriya suna sa rana ganin sakamako, saboda haka babu wani uzuri da za su karɓa. Ina kuma kira da ku kasance masu dabaru da hangen nesa da kuma jarumta.
“Mu kasance mun tari hanzarin duk waɗanda ke neman tayar da zaune tsaye a ƙasarmu,” in ji Tinubu.
Yayin bikin, an ƙara wa Olufemi Oluyede muƙami zuwa Janar, Waidi Shaibu zuwa Laftanar Janar, Idi Abbas zuwa Vice Admiral, da Kevin Aneke zuwa Air Vice marshall, da kuma Emmanuel Undiendeye zuwa Laftanar Janar.