NDLEA Ta Kama Haramtattun Magungunan Gargajiya A Jihar Kano
Published: 2nd, September 2025 GMT
Hukumar NDLEA a Kano ta kama kwalabe 8,000 na Akuskura da ake zargin na ɗauke da ƙwayoyi, tare da tabar wiwi guda 48.
An cafke wani mutum mai shekara 37, Ali Muhammad, bayan an gano kayan a cikin tirela ɗauke da kekuna a kan hanyar Zariya zuwa Kano a Gadar Tamburawa.
’Yansanda Sun Kama Masu Safarar Makamai A Katsina, Sun Ƙwato Makamai ’Yansanda Sun Kama ‘Yan Daba 107 A Kano, Sun Ƙwato Makamai Da ƘwayoyiNDLEA ta ce tana tsare da wanda ake zargin da kuma kayayyakin, yayin da ake ci gaba da bincike.
Hukumar ta buƙaci jama’a su riƙa sanar da ita duk wani abin da suka zarga na da alaƙa da miyagun ƙwayoyi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Akuskura Ƙwayoyi Tabar Wiwi
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Neja Ta Musanta Rahoton Hana Da’awa A Jihar
Rahoton rashin fahimtar da aka fara yadawar, ya biyo bayan taron kwamitin zaman lafiya da kwantar da tarzoma na jihar, wanda Darakta Janar ya jagoranta a ranar 4 ga watan Satumba.
Rashin fahimtar sahihin sakamakon taron ya sa wasu suka rahoto cewa, kwamitin ya dakatar da Malamai daga yin wa’azi.
Sanarwar ta kara da cewa, “Hukumar ba ta da hurumin haramtawa Malaman Addinin Musulunci yin wa’azi sai dai in ya bayyana a fili an taka ƙa’idojin hukumar da ta shimfiɗa”.
A cewar Hukumar, an kira taron ne domin gabatar da fom din rijistar yin wa’azi ko Da’awah da kuma bin tsarin tantancewa.
Ta bayyana shirin a matsayin wani yunkuri na wayar da kan jama’a don “hana rashin fahimtar juna da kuma daƙile yaɗuwar wa’azin yaudara” a faɗin jihar Neja.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp