Sojoji sun bankaɗo mafakar ’yan ta’adda da makamai a Taraba
Published: 7th, September 2025 GMT
Sojojin runduna ta 6 da ke Jalingo, babban birnin Jihar Taraba, sun gano wata mafakar ’yan ta’adda tare da ƙwato makamai da dama a ƙauyen Ikyaior da ke ƙaramar hukumar Wukari, a kan iyakar Taraba da Benuwai.
Bayanan sirri da sojojin suka samu ne suka taimaka musu wajen kai farmakin da ya kai ga gano mafakar da kuma ƙwato makaman.
Mataimakin mukaddashin kakakin rundunar, Laftanar Umar Mohammed, ya tabbatar wa da wakilin Aminiya cewa sojojin sun gudanar da bincike a yankin, inda suka gano makamai masu tarin yawa.
“Mun samu makamai daban-daban, ciki har da bindigogi ƙirar AK-47 guda uku, bindigogi ƙirar FN guda uku, da wasu ƙarin makamai da harsasai. Sai dai ba mu kama kowa ba a wajen,” in ji Laftanar Umar.
Ya ƙara da cewa mafakar na tsakanin kan iyakar Jihohin Taraba da Benuwai ne, wanda hakan ke nuna cewa ana amfani da yankin wajen boye makamai da kitsa hare-hare.
Shi ma kwamandan rundunar, Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya jinjina wa dakarun da suka kai samamen, tare da kira ga al’ummar yankin da su riƙa ba da rahotannin sirri don taimaka wa sojoji wajen yaƙi da ta’addanci.
“Muna buƙatar hadin kan jama’a. Sojoji na rundunar ta 6 za su ci gaba da aikin kawar da ’yan ta’adda da bata-gari a Taraba da ƙasa baki daya,” in ji Janar Uwa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan ta adda Jihar Benuwe Jihar Taraba
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji Sun Kashe Mayaƙan ISWAP 11 A Borno Da Adamawa
Nijeriya dai ta daɗe tana fama da ta’addancin Boko Haram da ISWAP a Arewa Maso Gabas.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp