Ndume ya koka kan sabbin hare-haren Boko Haram a Borno
Published: 2nd, September 2025 GMT
Sanata Mohammed Ali Ndume, ya koka kan yawaitar sabbin hare-haren mayaƙan Boko Haram ƙananan hukumomin Gwoza da Askira/Uba, inda suka kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a ƙarshen mako.
A safiyar ranar Asabar din da ta gabata a garin Ngoshe da ke Gwoza an kashe manoma biyar a lokacin da suke aiki a gonakinsu.
Haka zalika, a yankin Mussa da ke Askira/Uba, wasu ’yan bindiga sun kai farmaki ƙauyen a ranar asabar da daddare, inda suka kashe matasa uku, kafin su ƙona wasu gidaje da shaguna da ƙauyen.
Waɗannan munanan hare-haren sun jefa al’ummomin cikin zaman makoki wanda ya ƙara nuna damuwa kan rashin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar yankin.
Sai dai kuma Sanata Ndume ya yaba da sadaukarwar da sojoji rundunar‘Operation Hadin Kai’ da ke Arewa maso Gabas, bisa nasarorin da aka samu a kan ’yan ta’adda.
Ndume ya bayyana duka abubuwan da suka faru a baya-bayan nan a matsayin “abin takaici” tare da cewa ci gaba da kai hare-hare a kan al’ummar yankin da ba su ji ba ba su gani ba, musamman manoma da matasa, wani abu ne mai muni na rashin tsaro da ke ci gaba da wanzuwa a Borno ta Kudu.
Sanata Ndume ya tabbatar wa al’ummar Ngoshe, Mussa, da ma ɗauƙacin yankin Borno ta Kudu, kan y\ƙudurinsa na tsayawa tare da su a wannan mawuyacin lokaci.
Ya kuma jaddada cewa, yana aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatocin tarayya da na jihar Borno, da kuma rundunar sojojin Nijeriya da sauran hukumomin tsaro, domin ƙarfafa matakan tsaro a yankunan karkara.
Ya kuma yi qira ga mazauna yankunan da su kasance masu lura da kuma bayar da cikakken haxin kai ga jami’an tsaro domin daƙile hare-haren da za a iya kaiwa nan gaba.
Ya buƙaci a haɗa kai a tsakanin al’ummomi, yana mai jaddada muhimmancinsu wajen tinkarar ƙalubalen ’yan tada ƙayar baya.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Iran ta damu da halin da ake ciki a yankin El Fasher na Sudan
Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta nuna damuwarta game da irin tashin hankali da ake ciki a Sudan musamman a yankin El Fasher.
Iran ta sake jaddada goyon bayanta ga ‘yancin Sudan, da hadin kai, da kuma cikakken yankin kasar yayin da tashin hankali ya mamaye kasar dake Arewacin Afirka.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa ta waray tarho da takwaransa na Sudan Mohiuddin Salem a ranar Juma’a.
Na farko ya nuna damuwa musamman game da hare-hare da kisan gillar da aka yi wa fararen hula a birnin El Fasher da ke kudu maso yammacin Sudan.
Duniya ta damu matuka a daidai lokacin da ake ci gaba da samun karuwar tashin hankali a Sudan.
A ranar Talata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmaeil Baghaei ya bayyana matukar damuwa game da rikice-rikicen makamai da ake ci gaba da yi a El Fasher, yana mai Allah wadai da lalata kayayyakin more rayuwa da kuma kisan fararen hula a birnin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kwamitin Tsaron MDD ya goyi bayan shirin Morocco game da yankin Yammacin Sahara November 1, 2025 Samia Suluhu Hassan ta lashe zaben shugaban kasa a Tanzaniya November 1, 2025 Najeriya ta musanta ikirarin Trump, na cewa Kristoci na fuskantar babbar barazana a kasar November 1, 2025 Majalisar Dinkin Duniya ta damu da hare-haren Amurka a Caribbean da Pacific November 1, 2025 Israila Ta Kai Hari Kan Ofishin kungiyar UNICEF Dake Gaza A November 1, 2025 Amurka Na Shirin Kai Hari Kan Kasar Venzuwela A Kowanne Lokaci November 1, 2025 Iran Ta Sanya Da Ranar 30 Ga Watan Nuwamba A Matsayin Ranar Kasa Ta Tsibirai 3 October 31, 2025 Isra’ila Na Ci Gaba Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza October 31, 2025 An Tube Yarima Mai Jiran Gado Na Birtaniya Bayan Da Aka Tabbatar Da Laifinsa October 31, 2025 Kasashen Pakistan Da Afghanistan Sun Tsawaita Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta October 31, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci