Aminiya:
2025-11-02@19:37:48 GMT

Harin Borno: Dole ’yan Najeriya su haɗa kai su fuskanci Boko Haram — Atiku

Published: 8th, September 2025 GMT

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi Allah-wadai da sabon harin da Boko Haram suka kai a Jihar Borno, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama; ciki har da sojoji.

Atiku, ya bayyana halin da ’yan Najeriya ke shiga sakamakon hare-haren ta’addanci.

Ambaliyar Ruwa: NEMA ta ceto mata 2 da jaririya a Kaduna  Harin Boko Haram: Zulum ya kai ziyarar jaje garin Darajamal

A cikin saƙon da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, Atiku ya yi kira ga ’yan Najeriya da su haɗa kai wajen yaƙi da matsalar tsaro ta hanyar haɗin kan al’umma.

Ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, jama’ar Jihar Borno, da kuma Gwamna Babagana Umara Zulum.

Ya kuma yaba wa gwamnan bisa ziyarar jaje da ya kai wa al’ummar da abin ya shafa.

Atiku ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa waɗanda suka rasu, Ya kuma sanya su a Aljanna Firdausi.

Hakazalika, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su ci gaba da jajircewa wajen samar da zaman lafiya da tsaro.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Boko Haram hari Tsaro yan Najeriya

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu ya yanke hulɗa da Amurka kawai — Sheikh Gumi

Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya shawarci Shugaba Bola Tinubu da ya ɗauki mataki mai tsauri a kan Shugaban Amurka, Donald Trump, game da barazanar da ya yi na amfani da ƙarfin soja a kan Najeriya.

Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, malamin ya bayyana cewa irin wannan magana ta Trump cin mutunci ce ga ’yancin Najeriya.

Tsaro: Taimakonmu Amurka ya kamata ta yi maimakon barazana — Kwankwaso Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka

Don haka malamin ya yi kira da a ɗauki matakin diflomasiyya cikin gaggawa.

“Trump ya yi barazana ga ƙasa mai cin gashin kanta da harin soja, wannan girmamawa ne ga ƙasarmu,” in ji Gumi.

Sheikh Gumi, ya nemi Gwamnatin Tarayya ta kira Jakadan Amurka domin neman bayani da kuma a janye wannan barazanar, inda ya yi gargaɗin cewa idan ba a yi haka ba, to Najeriya ta yanke hulɗa da Amurka.

“Shugaba Tinubu ya kamata ya kira Jakadan Amurka idan ba su janye barazanar ba, to mu yanke hulɗa da wannan gwamnati mara mutunci,” in ji shi.

Gumi, ya kuma jaddada cewa Najeriya tana da damar bunƙasa tattalin arziƙinta ba tare da dogaro da Amurka ba.

“Akwai hanyoyi da dama da za mu iya faɗaɗa tattalin arziƙinmu da ƙarfafa haɗin kan soji ba tare da dogaro da su ba,” in ji Gumi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu ya yanke hulɗa da Amurka kawai — Sheikh Gumi
  • Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci
  • Gwamnatin Jihar Kwara Ta Kafa Kwamitoci 2 Don Tantance Wadanda Suka Yi Ritaya
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar
  • Zaben 2027 Zai Kasance Ne Tsakanin Mulkin Tinubu Da Zabin Ƴan Nijeriya —Atiku Abubakar
  • Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da shirin amfani da ma’adanai
  • An raba wa iyalan jami’an ’yan sandan da suka rasu a bakin aiki a Borno N63.4m
  • Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Kutsen Na Isra’ila A Kudancin Kasar
  • Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Duk Wani Kutse Na Isra’ila A Kudancin Kasar
  • NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Daliban Makarantar Kudi Suka Fi Na Gwamnati Kokari