Aminiya:
2025-09-17@22:28:57 GMT

Rundunar sojin ruwa za ta kafa sansaninta a Kebbi

Published: 1st, August 2025 GMT

Rundunar sojin ruwan Najeriya ta bayyana aniyar kafa sansaninta a Ƙaramar Hukumar Yauri ta Jihar Kebbi a wani mataki don bunƙasa harkokin tsaron iyakokin ruwa.

Hakan na zuwa ne bayan da wata tawagar manyan jami’an sojojin ruwan suka kai ziyara gidan gwamnatin Jihar Kebbi.

Ɗaliban da aka sace a Binuwai sun kuɓuta  ’Yan Najeriya miliyan 34 na cikin barazanar yunwa

Sojojin sun kai ziayarar ne ƙarƙashin jagorancin Rear Admiral Patrick Nwatu – wanda ya wakilci babban hafsan sojin ruwan ƙasar.

Rundunar ta ziyarci Kebbi ne domin duba yadda za ta samar da sansaninta a jihar.

Patrick Nwatu ya yi tir da harin ta’addanci a kogin Neja, yana mai cewa yankin ya zama maɓoyar masu safarar makamai da sauran masu aikata laifuka.

Rundunar sojin ruwan Najeriya ta ce ta kammala shirye-shiryen kafa sansanin sojin ruwa a garin Yauri da ke jihar.

Babban Hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ogalla ne ya bayyana hakan a wata ziyarar ban girma da suka kaiwa Gwamnan Kebbi, Nasir Idris a gidan gwamnati da ke Birnin Kebbi a ranar Alhamis.

Da yake jawabi yayin ziyarar, jagoran tawagar Rear Admiral Patrick Nwatu, ya ce ziyarar wani ɓangare ne na faɗaɗa dabarun teku na sojojin ruwan Najeriya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Sojojin ruwa Yauri

এছাড়াও পড়ুন:

Sarki Sanusi II ya koka kan yawan cin bashin Najeriya

Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya koka bisa yawan bashin da Najeriya ke ciyowa da kuma yadda gwamnati ke facaka da kuɗaɗen.

Sarkin wanda tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) ne, ya kuma bayyana cewa cire tallafin man fetur da Gwamnatin Tarayya ta yi shi ne mafi alheri, yana  mai cewa da Gwamnatin ba ta cire tallafin mai ba, da Najeriya ta daɗe da tsiyacewa.

“Adawata a ɓangaren shan man ne, saboda muna ba da aikin yi ga matatun mai a Turai. Muna ba da aikin ga masu tace ɗanyen man,” in ji Sarki Sanusi.

Da yake jawabi a Taron Adabi na Duniya na Kano (KAPFEST) da aka gudanar a Kano ranar Asabar, masanin tattalin arzikin ya bayyana cewa ɗabi’ar yawan cin bashin Najeriya za ta yi mummunar illa ga tattalin arzikin ƙasar na tsawon lokaci.

Mutuwar majinyata: Asibitin Aminu Kano na roƙon KEDCO ya dawo da wutar lantarki Gidauniyar Misilli ta mayar da yara 150 makaranta a Gombe

Masanin tattalin arzikin ya bayyana damuwa musamman kan yadda gwamnati ke kashe kuɗaɗen da ta ciyo bashin.

Zuwa ƙarshen watan Maris, yawan bashin da ake bin Najeriya ya haura Naira tiriliyan 150.

A yayin taron wanda cibiyar Poetic Wednesdays Initiative (PWI), ta shirya, Sarki Sanusi II ya ce, ya ce, “Ina muke kai wannan tulin bashin da muke ciyowa a ƙasar nan?

“Zan yi farin cikin ganin an yi amfani da kuɗaɗen a fannin ilmantar da matasanmu, saboda su ne za su biya. Amma bai kamata mu yi ciyo bashi muna lafta wa tattalin arzikin ƙasa ba tare da zuba jari a fannin ilmantar da waɗanda su ne za su biya bashin ba.

“Nan da shekara 20 za mu faɗa a matsala a dalikin cin bashi. Dole a zuba jari a fannin inganta rayuwarsu domin samar da abubuwa.”

Ya bayyana cewa Najeriya ba ta yi sa’ar shugabanni nagari ba a tsawon lokaci, yana mai cewa yawancin shugabannin ƙasar ragwage ne masu yawan kawo uzuri.

Sarki Sanusi II ya bayyana kyakkyawan shugabanci a matsayin muhimmin abin da zai ceto Najeriya daga halin da take ciki, wanda ya kira na rashin sa’a.

Da yake sukar yanayin koma-bayan Najeriya alhali wasu ƙasashe sun yi gaba ta fannin kimiyya da fasaha da ci-gaban zamani, Sarki Sanusi II ya buƙaci matsala da su tashi domin karɓar ragamar shugabancin ƙasar, yana mai jaddada cewa hakan abu mai yiwuwa ne idan matasan suka jajirce.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnati ta ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani 20 a Sakkwato
  • Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ta Kammala Ziyarar Yini 3 A Ma’aikatar Kananan Hukumomin Jihar
  • Lakurawa Sun Hallaka Jami’in Kwastam A Jihar Kebbi
  • Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo
  • Isra’ila Ta Kai Hari A Tashar Jirgin Ruwan Hudaidai Dake Kasar Yamen
  • ’Yan sanda sun kama mutum 6 kan satar zinarin N109m a Kebbi
  • NAJERIYA A YAU: Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba
  • Bayanin Bayan Taron Doha Ya Yi Kira Da A Kafa Runduwar Hadin Gwiwa Ta Kare Kai
  • Sarki Sanusi II ya koka kan yawan cin bashin Najeriya
  • NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar Ruwa