Za Ayi Aiki Hadin Gwiwar Tsakanin Efcc Nuj Domin Yaki Da Hako Ma’adanai A Neja
Published: 10th, April 2025 GMT
Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) za ta hada gwiwa da kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) a yaki da hako ma’adinai da kuma ayyukan ta’addanci a kasar nan.
Mukaddashin Daraktan shiyyar Kaduna mai kula da shiyyar Kaduna, Mista Bawa Usman Kaltungo ne ya bayyana hakan a lokacin da ya jagoranci tawagar ofishin shiyya ta Kaduna na EFCC zuwa NUJ a jihar Neja a Minna.
Mista Bawa Usman wanda ya shaida wa manema labarai cewa an kama masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba amma ya ci gaba da cewa “yaki da wadannan laifuffuka ba na EFCC kadai ba ne domin yana da girma da yawa a gare mu don haka yana bukatar hadin kan kowa da kowa.
Ya yabawa ’yan jarida kan kasancewarsu abokan huldar dabarun yaki da cin hanci da rashawa, inda ya jaddada cewa, ayyukan da ake yi a baya-bayan nan kan ayyukan ta’addanci a jihar, shi ne na dakile ayyukan ta’addanci, kuma suna fuskantar shi sosai kuma za mu yi nasara a kan aikin da ke gabanmu.
Mista Musa Bawa Kaltingo ya ce “su (masu aikata laifuka) a yanzu suna kallon jihar Neja a matsayin mafaka kuma suna garzayawa nan don gudanar da ayyukansu.
Da yake mayar da jawabi shugaban majalisar NUJ na jihar Neja, Kwamared Abu Nmodu ya bayyana damuwarsa kan karuwar aikata laifuka ta yanar gizo a jihar Neja, yana mai cewa “abin damuwa ne kuma dole ne mu kawar da duk wani abu mara kyau da ake gani barazana”.
Yayin da yake tabbatar wa EFCC goyon bayan kungiyar, Kwamared Abu Nmodu ya jaddada bukatar hadin gwiwa don tabbatar da cewa an horar da ‘yan jarida kan mafi kyawu a cikin rahoton ayyukan EFCC don samun sakamako mafi kyau.
COV ALIYU LAWAL.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Ɗan Majalisar Tarayya Ya Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-haren Ta’addanci A Sakkwato
Mataimakinsa kan harkokin majalisa Honarabul Attahiru Danmadi ne ya wakilci dan majalisar ya kuma tabbatarwa wadanda lamarin ya shafa kokarinsa kan daukar matakan da suka kamata domin tabbatar da tsaron rayukan su da dawowa da zaman lafiya a yankunan.
Garuruwan da ‘yan bindigar suka tarwatsa a gundumar Kuchi sun hada da Fakku, sha’alwashi, tulluwa da Rafin- gora a inda mutane bakwai suka rasa rai. A gundumar Jabo kuwa kauyukan da lamarin ya shafa su ne; Gesolodi, Hilya, Guraye, Guma, Chakai, Modo, Badariya, Tafki, Balera, Gudumawa da Rafin shinka.
“Mun girgiza kwarai da wannan halin da kuke ciki. A matsayina na wakilin ku, zan ci-gaba da kokarin da ya kamata a majalisa domin ganin jami’an tsaro sun kawo karshen wannan ta’addancin.”
Dan Majalisar ya ce ya gabatar da bukata ga Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa domin tallafawa wadanda lamarin ya shafa kuma zai ci- gaba da bibiya domin ganin tallafin ya samu cikin lokaci.
Ya ce yana kokarin ganin rundunar sojoji ta kara tura wadatattun jami’ai tare da tallafa masu domin yakar ‘yan ta’addan da wanzar da zaman lafiya a yankunan.
Tallafin kayan abinci na gaggawa da dan majalisar ya bayar sun hada da buhuhuwan masara, gero, garin kwaki da kuma kuli- kuli.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp