Hajjin 2025: Jihar Kaduna Ta Yi Tanadin Masauki Na Musamman Ga Alhazan Bana
Published: 10th, April 2025 GMT
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna ta samu nasarar samo ingantaccen masauki ga alhazan jihar a birnin Makkah, gabanin gudanar da aikin Hajjin 2025.
Daya daga cikin mambobin kwamitin musamman da ke kula da aikin hukumar, Malam Buhari Marabar-Jos ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Talata a Kaduna.
Buhari Marabar-Jos ya bayyana cewa masaukan sun cika dukkan sharuddan da Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) da Ma’aikatar Hajji ta Saudiyya suka gindaya.
Ya kuma bayyana cewa wata tawaga ƙarƙashin jagorancin Shugaban Hukumar, Malam Salihu Abubakar, tana can ƙasar Saudiyya don kammala sauran shirye-shirye kafin dawowarsu Najeriya.
Ya jaddada cewa Gwamna Uba Sani ya ƙuduri aniyar kula da jin daɗin alhazan jihar, tare da tabbatar da cewa gwamnati ta himmatu matuƙa wajen ganin an gudanar da aikin Hajji cikin sauƙi da nasara.
Ya yi kira ga maniyyata aikin Hajjin bana da su ci gaba da halartar taron bita na mako-mako da hukumar ke gudanarwa a faɗin ƙananan hukumomi 23 na jihar.
Safiyah Abdulkadir
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnan Sokoto Ya Amince Da Sauya Wa Manyan Sakatarori 25 Ma’aikatu A Jihar
Gwamnatin jihar ta ce, matakin na daya daga cikin kokarin gwamnati mai ci na inganta ayyukanta domin samar da romon dimokuraɗiyya ga al’ummar jihar Sokoto.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp