Ranar Mata: UNICEF Da Jihar Jigawa Sun Horar Sa Mata 600 Shirin Jari Bola
Published: 10th, March 2025 GMT
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar Jigawa, sun fara horas da mata 600 kan inganta muhalli ta hanyar bola jari.
Shugaban Hukumar Kare Muhalli ta Jihar Jigawa JISEPA, Alhaji Adamu Sabo ya bayyana haka a wajen taron tunawa da ranar mata ta duniya da kuma fara horaswar da aka gudanar a Dutse.
Alhaji Adamu Sabo ya ce, baya ga jajircewa, da juriya, da nasarorin da mata suke da, bikin ya yi duba kan irin rawar da mata suke takawa wajen dorewar muhalli da bunkasar tattalin arziki.
Ya jaddada cewa ta hanyar shirin bola jari, watiWaste to Wealth Initiative, za su iya baiwa mata damar kare muhalli da kuma samar da kyakkyawan yanayi ga iyalansu.
Shugaban hukumar ya bayyana cewa, duk da kalubalen da ake fuskanta a duniya a fannin sarrafa shara, da kuma yadda ake zubar da shara ba bisa ka’ida ba, da ke barazana ga muhalli, har yanzu akwai damar da za a iya maida sharar da aka tara a gida zuwa dukiya.
Ya ce horon zai koyar da mata yadda za su yi kasuwanci da sharar da suka tara a gida, tare da tabbatar da karfafa tattalin arziki da kuma inganta muhalli.
Ya kara da cewa, hakan zai baiwa mata matasa damar ba da gudumawa wajen samun kudaden shiga a gida da kuma ci gaban tattalin arzikin kasa.
Bugu da ƙari, shugaban na JISEPA ya bayyana cewa horaswar za ta yi amfani da shirin da UNICEF ta fara na “Samun Damarar Kasuwanci ga Matasa” (YOMA), wani sabon tsarin na dandali ta yanar gizo, da ke haɗa matasa daga ko’ina a fadin duniya don koyon kasuwanci, da samun kuɗi, da tasirin zamantakewa.
Adamu Sabo ya yabawa masu ruwa da tsaki da suka goyi bayan wannan shiri da suka hada da kungiyar jari bola ta Najeriya WAPAN, da gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi bisa goyon bayan da suka bayar.
A jawabinta lokacin da take bayyana bude horaswar, uwargidan gwamnan jihar Jigawa, Hajiya Amina Umar Namadi, ta yaba da kokarin hukumar da sauran masu ruwa da tsaki da suka taimata wajan samun nasarar horon.
Ta ce shigar da mata cikin shirin inganta muhalli ba shakka zai samar da wani tasiri, ba a Jigawa kadai ba har ma a duniya baki daya.
Ta yi kira ga mahalarta taron da su yi amfani da damar da suka samu wajen inganta rayuwarsu, baya ga ba da gudummawa wajen tsaftace muhallinsu.
Taken ranar Mata ta Duniya ta 2025 shi ne, “Bayar Da Dama ga Mata da ‘Yan Mata: Hakkoki, Daidaito, da Ƙarfafawa, “wanda ke kira ga bai wa mata hakkokinsu, da samar musu da damarmaki, ba tare da an bar su a baya ba.”
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa Ranar Mata
এছাড়াও পড়ুন:
Ma’aikatar Ilimi ta Jigawa Za Ta Kashe Naira Biliyan 18 a 2026
Daga Usman Muhammad Zaria
Ma’aikatar ilimi matakin farko ta jihar Jigawa ta ce za ta kashe fiye da naira miliyan dubu 18 domin gudanar da harkokinta a sabuwar shekara.
Kwamishinan ma’aikatar, Dr. Lawal Yunusa Danzomo ne ya bayyana haka lokacin da yake kare kiyasin kasafin kudin 2026 a gaban kwamatin ilimi matakin farko na majalisar dokokin jihar Jigawa.
Dr. Lawan Yunusa Danzomo ya ce zasu mayar da hankali ga aikin gina ajujuwa da gyaran wadanda suka lalace.
Za kuma a samar da littatafan darussa da tebura da kujeru domin inganta harkokin koyo da koyarwa.
Hakazalika za a gina bandakuna da samar da ruwan sha da wutar lantarki da tsaro.
Danzomo, ya ce aiwatar da haka zai yi matukar tabbatar da kyakkyawar da’irar ilimi da ta kunshi samar da ilimi cikin sauki ta hanyar shiga makaranta har a kammmala karatu.
Dr. Lawan Danzomo ya kara da cewar za a dauki malaman wucin gadi har su 4000 a karkashin shirin J-Teach.
Ya kuma yi nuni da cewar, za a shirya jarrabawa ga kason farko na malaman J-Teach su 1,450 na gwamnatin da ta gabata domin daukar su aiki na dindindin.
A nasa jawabin shugaban kwamatin ilimi matakin farkio na majalisar dokokin jihar Jigawa kuma wakilin mazabar Fagam, Alhaji Yahaya Zakari Kwarko ya bada tabbacin hadin kai da goyon baya domin samun nasarar da ake bukataa sabuwar shekara.