Mun bai wa Akpabio sa’o’i 48 ya dawo da Sanata Natasha — SERAP
Published: 10th, March 2025 GMT
Ƙungiyar SERAP, mai fafutukar haƙƙin ɗan Adam da yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya, ta buƙaci Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio da ya gaggauta janye dakatarwar da majalisar ta yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
SERAP ta ce dakatarwar da aka yi wa Sanata Natasha ba komai ba ne illa tauye mata ’yancinta na faɗin alabarkacin baki, wanda Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya ba ta.
Cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa da ta fitar a ranar 8 ga watan Maris, SERAP ta ce muddin ba a kiyaye wannan gargaɗi ba za ta ɗauki matakin shari’a nan da sa’o’i 48.
Wasiƙar mai ɗauke da sa hannun matamaikin shugabanta, Kolawole Oluwadare, SERAP ta ce kasancewar Natasha a matsayin Sanata ba zai haramta mata ’yancinta na faɗin albarkacin baki ba
SERAP ta nanata cewa dakatar da Sanata Natasha ya saɓa wa duk wasu tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya da kuma Dokokin Duniya da suka sahale mata ’yanci a matsayinta na bil Adama.
Ƙungiyar ta kafa hujja da sashe na 39 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya da kuma sashe na 9 na Kundin Kare Haƙƙoƙin ɗan Adam na Afirka, inda ta ce matakin da Majalisar Dattawan ta ɗauka ba bisa ƙa’ida ba ne kuma ya saɓa doka.
Ƙungiyar ta kuma yi Allah wadai da take haƙƙin da aka yi wa Sanata Natasha ta hanyar haramta mata wakilcin al’ummar mazaɓar Kogi ta Tsakiya a Majalisar Dattawan ƙasar.
A makon da ya gabata ne dai Majalisar Dattawa ta sanar da dakatar da Sanata Natasha Uduaghan tsawon watanni shida bayan kwamitin ladabtarwa na majalisar ya zarge ta da karya wasu daga cikin dokokinta.
Kwamitin ya yi zargin cewa Sanata Natasha ta yi magana ba tare da izini ba, kuma ta ƙi komawa sabon wurin zaman da aka sauya mata a zauren majalisar.
Har ila yau, an dakatar da albashinta da sauran haƙƙoƙinta na kuɗaɗe har tsawon lokacin dakatarwar, kuma an hana ta gabatar da kanta a matsayin Sanata.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Majalisar Dattawa SERAP wa Sanata Natasha a Majalisar
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnan Kano ya naɗa mace ta farko a matsayin shugabar Jami’ar Northwest
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗin Farfesa Amina Salihi Bayero, a matsayin sabuwar Shugabar Jami’ar Northwest.
Naɗin nata zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Disamban 2025, har zuwa tsawon shekaru biyar.
EFCC ta tsare tsohon ministan ƙwadago, Chris Ngige An koro ’yan Najeriya 32 kan kasuwancin miyagun ƙwayoyi a IndiyaMai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.
Sanarwar, ta ce gwamnan ya amince da naɗin ne bayan tantancewa da kwamitin gudanarwar jami’ar ya yi mata.
A matsayinsa na jagoran jami’ar, Gwamna Abba, ya yaba wa shugaban kwamitin da mambobinsa kan jajircewarsu wajen bin ƙa’idojin tantancewar.
Haka kuma ya nemi a yi mata addu’ar samun nasara wajen gudanar da jagorancin Jami’ar.
Farfesa Amina Salihi Bayero ƙwararriya ce a fannin Chemistry, musamman Analytical Chemistry, kuma ita ce mace ta farko da ta samu digiri na uku a fannin daga Jami’ar Bayero Kano.
Ta taɓa riƙe muƙamai da dama a harkar ilimi da gudanarwa, ciki har da shugabar sashen Chemistry, da kuma Mataimakiyar Shugabar Jami’a (DVC) a Jami’ar Yusuf Maitama Sule.
Ana girmama ta saboda jajircewarta wajen horar da matasan masana kimiyya.
Ana sa ran naɗin nata zai ƙara ɗaukaka martabar jami’ar, ya inganta tsarin ilimi, tare da bai wa mata ƙofar samun manyan muƙamai a Jihar Kano.