New York Times: Isra’ila ce ta kashe wasu fursunoninta da ake tsare da su a Gaza
Published: 10th, March 2025 GMT
Fiye da fursunoni 40 na Isra’ila da ke hannun kungiyoyin gwagwarmayar Falastinawa ne suka mutu a hare-haren da sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila suka yi ta kaddamarwa kan al’ummar yankin tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2023, kamar yadda wani rahoton baya-bayan nan na jaridar New York Times ya bayyana.
Binciken, wanda jaridar ta New York Times ta buga a wannan Asabar, ya ce fursunoni 41 daga cikin fursunoni 251 na Isra’ila da ake tsare da su a Gaza, an kashe su ne ta hanyar bama-bamai da Isra’ila ta yi ta jefawa kan yankin.
Binciken ya dogara ne akan rahotanni da kuma binciken soji kan mutuwar fursunonin, da hirarraki da sojoji da jami’an Isra’ila, da kuma wasu daga cikin dangin wadanda aka kama.
Jaridar ta yi nuni da dagewar da Netanyahu ya yi na ci gaba da yakin Gaza domin kubutar da wadanda ake tsare da su ta hanyar daukar matakan soji maimakon daukar matakin kawo karshen fadan ta hanyar tattaunawa da kuma musayar fursunoni, wanda kuma bayan kisan dubun-dubatar mutanen Gaza, da ma wasu daga cikin fursunonin Isra’ila, Netanyahu ya dawo ya amince da yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma musayar fursunoni.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ma’aikata 240 na karɓar albashi biyu, wasu 217 na amfani da lambar BVN ɗaya a Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta gano ma’aikatanta 240 da ke ƙarɓar albashi sau biyu a duk wata, da wasu 217 da ke amfani da lambar tantance asusun banki (BVN) guda ɗaya.
Wani mai magana da yawun gwamnati, Dakta Sulaiman Wali Sani, ya gaya wa manema labarai a ranar Lahadi cewa an gano wannan badaƙalar ce a yayin da ake tantance tsarin biyan albashin gwamnati.
Dr. Sani ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi alƙawarin biyan ma’aikata daidai kuma akan lokaci, kuma gano waɗannan matsalolin wani ɓangare ne na gyara al’amura.
Ya ce sun duba bayanan ma’aikata ta hanyar amfani da hotunan yatsa a matakin jiha da ƙananan hukumomi.
“Tsohuwar hanyar biyan mutane tana da matsaloli. Mun gano ma’aikata 240 suna karɓar albashi sau biyu kuma mutane 217 suna amfani da BVN ɗaya, wanda zai iya nufin akwai ma’aikatan bogi ko kuma mutane suna amfani da BVN na wani,” in ji Dakta Sani.
Ya kuma ce ma’aikata 1,335 ba su zo don a tantance su ba a tsawon fiye da watanni shida, wanda ya sa suke tunanin ko waɗannan mutanen da gaske suna aiki da gwamnati.
Alhaji Umar Idi, wanda ya duba biyan kuɗin ƙananan hukumomi, ya ce sun gano sunaye 247 da babu tabbaci a kansu. Waɗannan sun haɗa da mutanen da suka yi ritaya, waɗanda suka mutu, ko kuma waɗanda aka ci gaba da biyan su ba tare da izini ba bayan lokacin barinsu aiki.
“Daga cikin waɗannan ma’aikata 247, takwas ne kawai suka zo don tabbatar da cewa har yanzu suna aiki. Za a goge sauran sunaye 239, wanda zai rage wa gwamnati asarar naira miliyan 27 a duk wata,” in ji shi, yana mai cewa za a mayar da kuɗaɗen da aka samu ga asusun gwamnati.
Dakta Sani ya ce gwamnati ba ta ƙoƙarin hukunta kowa ba, kawai dai tana gyara tsarin ne don ma’aikata na gaske da ’yan fansho su ci gaba da karɓar haƙƙoƙinsu ba tare da wata matsala ko yanka ba bisa ƙa’ida ba.
“Tun lokacin da Gwamna Abba ya fara aiki, ya tabbatar da cewa ana biyan ma’aikatan gwamnati da ’yan fansho a kan lokaci, ba tare da ɓoyayyun cire-cire da aka riƙa yi a baya ba,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa yanzu da suke tsaftace tsarin biyan kuɗi, ma’aikata su yi tsammanin samun biyan kuɗi mafi inganci a gaba.
Gwamnati ta ce za ta ci gaba da magana da duk masu ruwa da tsaki don tabbatar da cewa an magance duk matsalolin kuma jama’a sun sake amincewa da ayyukan gwamnati.