Ambaliya: Gwamnatin Yobe ta samar wa magidanta 250 matsugunin wucin gadi
Published: 27th, August 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Yobe ta kwashe magidanta sama da 250 daga Garin Kolo da ke Ƙaramar Hukumar Nangere, zuwa sabon matsuguni bayan ambaliyar ruwa ta lalata musu gidaje.
An ƙaddamar da sabon matsugunin ne ƙarƙashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni domin kare rayukan waɗanda abin ya shafa.
Amurka ta ɗaure basaraken Osun kan zamba a tallafin COVID-19 Amurka ta ɗaure basaraken Osun kan zamba a tallafin COVID-19Babban sakataren Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar (YOSEMA), Alhaji Idi Jidawa, ya bayyana cewa an gina gidajen wucin gadi guda 22 domin amfanin mutanen.
Haka kuma, an samar da rijiya, banɗakunan wucin gadi guda biyar, da motar ɗaukar marasa lafiya.
Jami’an tsaro da suka haɗa da ’yan sanda da jami’an Sibil Difens na tabbatar da tsaron jama’a a wajen.
Waɗanda suka samu rauni kuma an tura su zuwa Babban Asibitin Nangere don samun kulawa.
Magidantan da ambaliyar ta shafa sun samu kayan abinci, inda gwamnatin ke shirin ƙara ba su wani tallafi.
Jidawa, ya ƙara da cewa gwamna Buni na da niyyar ganin duk wanda aka raba da gidansa ya koma cikin kwanciyar hankali.
Ya kuma gode wa Sarkin Tikau, ƙaramar hukumar Nangere, ma’aikatar lafiya, RUWASA, jami’an tsaro, da saurasu wajen ganin an cimma wannan nasara.
Hukumar YOSEMA ta roƙi masu hannu da shuni da ƙungiyoyin agaji da su ci gaba da tallafa wa wannan shiri na taimakon gaggawa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ambaliya
এছাড়াও পড়ুন:
NECO ta saki sakamakon jarabawar 2025
Hukumar Shirya Jarabawa ta Ƙasa (NECO), ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare (SSCE) na shekarar 2025.
Daga cikin ɗaliban da suka zana jarabawar guda 818,492, kashi 60.26 sun ci aƙalla darusa biyar da suka haɗa da Lissafi da Turanci.
Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu KanoShugaban NECO, Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi, ya ce ɗalibai 1,367,210 suka yi rajistar jarabawar; maza 685,514 da kuma mata 681,696.
Amma daga cikinsu, ɗalibai 1,358,339 ne suka zana jarabawar.
Ya ce ɗalibai 1,144,496, wanda ya kai adadin kashi 84.26, sun samu darusa biyar ba tare da cin Lissafi da Turanci ba.
Sai dai an dakatar da sakin sakamakon makarantu takwas a Ƙaramar Hukumar Lamorde ta Jihar Adamawa saboda rikicin ƙabilanci da ya auku tsakanin 7 zuwa 25 ga watan Yuli, 2025.
Rikicin ya yi sanadin wanda ya hana zana jarabawar darusa 13 da takardu 29.
Hukumar na tattaunawa da gwamnati don sake bai wa ɗaliban damar rubuta jarabawar.
NECO ta kuma bayyana cewa an samu makarantu 38 daga jihohi 13 ds laifin aikatar satar amsa yayin zana jarabawa.
Za a gayyace su zuwa babban ofishin NECO kafin ɗaukar mataki a kansu.
Haka kuma, hukumar ta dakatar da mutum tara da ke aikin sanya ido sake kula da jarabawa saboda gazawarsu wajen hana satar amsa.
Mutanen da aka dakatar, uku sun fito daga Jihar Ribas, uku daga Babban Birnin Tarayya, da kuma mutum ɗai-ɗai daga Jihohin Neja, Kano da Osun.