HausaTv:
2025-12-15@08:24:36 GMT

Harin Isra’ila ya kashe mutum 3 a kudancin Lebanon

Published: 15th, December 2025 GMT

Sojojin Isra’ila sun kashe akalla mutane uku a kudancin Lebanon a lokacin wasu hare-haren sama daban-daban bayan sun yi barazanar sake ci gaba da kai muggan hare-hare kan kasar.

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar lafiya ta Lebanon ta fitar ta ce wani “harin makiya ” a yankin Yater, a kudancin kasar, ya kashe mutum daya tare da raunata wani.

A wani bangare kuma, wani harin Isra’ilar da aka kai kan wata mota shi ma ya kashe wani mutum a tsakanin garuruwan Safad al-Batikh da Barashit.

A lokaci guda kuma, an kashe wani memba na majalisar birnin Jouaya, Tyre, bayan wani hari da Isra’ila ta kai kan garin.

Ministan yakin Isra’ila, Israel Katz, a karshen watan da ya gabata, ya yi gargadin cewa Tel Aviv ta shirya kaddamar da sabon yaki kan Lebanon idan kungiyar Hezbollah ba ta mika makamanta ba kafin karshen shekarar nan ta 2025.

Lebanon ta samu sakon gargadin daga bangarorin kasashen Larabawa da na kasa da kasa cewa Isra’ila na shirin kaddamar da wani babban hari kan kasar, in ji Ministan Harkokin Waje Youssef Raggi a ranar Juma’a.

M. Raggi ya ce Beirut na kara karfafa huldarta da kasashen yankin don “kare Lebanon daga duk wani hari.”

Babban sakataren kungiyar Hezbollah, Sheikh Naim Qassem, a wani jawabi da ya yi kwanan nan, ya yi alkawarin cewa kungiyar ba za ta taba ajiye makamanta ba, yana mai sukar shirin gwamnatin kasar wanda y ace Amurka da Isra’ila ne ke amfani da batun don matsa lamba kan kungiyar ta kwance damarar makamai.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Firaministan Ostiraliya ya goyi bayan tsauraran dokokin mallakar bindiga bayan harin Sydney December 15, 2025 Burtaniya: Masu Kin Baki Da Musulmi Suna Kai Masu Hare-Hare December 14, 2025 Iran Ta Bukaci Mutanen Yemen Su Daina Kashe Juna December 14, 2025 Iran Tayi Tir Da Hare-Haren Sydney Na Kasar Austaralia December 14, 2025 Sudan: Makaman ‘Drones’ Sun Kashe Ma’aikatan MDD 6 A Kadugli Na Kurdufan Ta Kudu December 14, 2025 Eritrea Ta Fice Daga Kungiyar Raya Kasahsen Gabacin Afrika (IGAD) December 14, 2025 َA Yau Ne Za’a Gudanar Da Taron Koli Na Kungiyar ECOWAS A Birnin Abuja December 14, 2025 Iran Ta karbi Bakunci Taron Kasashen Dake Makwabtaka Da Afghanistan Da Rasha December 14, 2025 Isra’ilaTa Kashe Wani Bafalasdine Matashi A Wani Hari Da Takai A Arewacin Kogin Jodan. December 14, 2025 Shuwagabannin Majalisar Kasar Iran Da Na Ethiopia Sun Gudanar Da Taron Manema Labarai December 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Iran Ta Bukaci Mutanen Yemen Su Daina Kashe Juna

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaei ya gargadi mutanen kasar Yemen daga kungiyoyi daban daban da su yi kokarin sasantawa a tsakaninsu, saboda ci gaba ta yakar juna yana taimakawa HKI ne kawau.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Baghaei ya na fadar haka a yau Lahadi a cikin wani  bayanin da ya watsa a shafinda na X.

Ya kara da cewa a cikin yan makonnin da suka gabata yan bindiga wadanda suke samun goyon bayan saudia sun fara yaki da sojojin Gwamnatin Yemen a kudancin kasar mai arzikin man fetur da nufin tada hankali a kasar.

Wasu kafafen yada labarai suna maganar cewa kudancin kasar Yemen zata shelanta bellewarta daga arewacin kasar nan ba da dadewa ba.

Baghaei ya bayyana cewa dukkan wadan nan al-amura suna faruwa ne a cikin shirin HKI na sake tsara kasashen yammacin Asiya.  Kuma shi yasa bata barin wata kasa daga kasashen yankin ta ci gaba da zaman lafiya ba.

 Daga karshen ya bukaci kungiyoyi daban-daban a kasar ta Yemen su yi kokarin sasantawa a tsakaninsu kada su ci gaba da aiki wa yahudawa ta hanyar rarraba kansu da kuma zubar da jinanensu don amfanin yahudawa.

Yayi kira ga gwamnatin kasar Yemen ta yi kokarin sasantawa da sauran Kabilun kasar don dawo da zaman lafiya a kasar. Duk wanda bai son zaman lafiya shi ne wanda yake khidima wa makiyan kasar.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Tayi Tir Da Hare-Haren Sydney Na Kasar Austaralia December 14, 2025 Sudan: Makaman ‘Drones’ Sun Kashe Ma’aikatan MDD 6 A Kadugli Na Kurdufan Ta Kudu December 14, 2025 Eritrea Ta Fice Daga Kungiyar Raya Kasahsen Gabacin Afrika (IGAD) December 14, 2025 َA Yau Ne Za’a Gudanar Da Taron Koli Na Kungiyar ECOWAS A Birnin Abuja December 14, 2025 Iran Ta karbi Bakunci Taron Kasashen Dake Makwabtaka Da Afghanistan Da Rasha December 14, 2025 Isra’ilaTa Kashe Wani Bafalasdine Matashi A Wani Hari Da Takai A Arewacin Kogin Jodan. December 14, 2025 Shuwagabannin Majalisar Kasar Iran Da Na Ethiopia Sun Gudanar Da Taron Manema Labarai December 14, 2025 Ghana Ta Kori Wasu Yahudawa Guda 3 Don Mayar Da Martani December 14, 2025 Araghchi ya bukaci Amurka ta girmama al’ummar Iran da gwamnatinta December 14, 2025 Dan bindiga ya kashe sojojin Amurka biyu da wani farar hula a Siriya December 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Firaministan Ostiraliya ya goyi bayan tsauraran dokokin mallakar bindiga bayan harin Sydney
  • Iran Ta Bukaci Mutanen Yemen Su Daina Kashe Juna
  • An kashe mutum 11 da jikkata wasu 29 a bikin Yahudawa a Ostireliya 
  • Isra’ilaTa Kashe Wani Bafalasdine Matashi A Wani Hari Da Takai A Arewacin Kogin Jodan.
  • Dan bindiga ya kashe sojojin Amurka biyu da wani farar hula a Siriya
  • Mutum biyu sun mutu a harbin bindiga a Jami’ar Brown ta Amurka
  • Isra’ila Ta Kai Hari A Kudancin Labanon  A Ci Gaba Da Keta Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta
  • MDD ta amince da wani kuduri da ke neman Isra’ila ta bada damar shigar da agaji a Gaza   
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Amince Ya Ziyarci Beirut