Pezeshkian: Duk wani rikici a gabas ta tsakiya babbar illa ce ga duniya baki daya
Published: 10th, March 2025 GMT
Shugaba Masoud Pezeshkian ya ce manufar Iran ta ginu ne kan samar da hadin kai a yammacin Asiya, kamar yadda kuma ta yi imanin cewa duk wani rikici da tashin hankali a yankin to zai illata kowa.
Pezeshkian ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da Firaministan Norway Jonas Gahr Støre a yammacin waannan Lahadi, inda suka tattauna kan muhimman batutuwa ad suka shafi alaka tsakanin kasashen biyu, da kuma sauran batutuwa na yankin da kuma na kasa da kasa.
Shugaban na Iran ya kara da cewa, Haramtacciyar Kasar Isra’ila na neman yada karya dangane da batun ayyukan nukiliyar Iran a matsayin tushen rashin tsaro a yankin.
Har ila yau ya jaddada cewa Iran ba ta taba neman kera makaman nukiliya ba.
Shugaba Pezeshkian ya ce Iran ta ba da hadin kai kuma za ta ci gaba da hada kai da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA domin kara tabbatar wa duniya da cewa shirinta na ayyukan farar hula ne, sabanin abin da makiyanta suke yadawa..
A nasa bangaren Firaministan Norway ya ce, kasarsa a shirye take ta ba da duk wani taimako da nufin warware matsalolin da ke faruwa a yankin yammacin Asiya a cikin lumana, tare da kara karfafa alakarta da kasar Iran.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jigawa Ta Kara Samar da Shirye-shiryen Inganta Rayuwar Masu Buƙata ta Musamman
Daga Usman Muhammad Zaria
Hukumar kula da masu bukata ta musamman a jihar Jigawa za ta gudanar da aikin gyaran gidajen gajiyayyu na shiyyar Birnin Kudu da Gumel a sabuwar shekara.
Shugaban hukumar, Malam Sale Zakar Kafin Hausa, ya bayyana haka lokacin kare kiyasin kasafin kudin 2026 a gaban kwamatin harkokin mata na majalisar dokokin jihar Jigawa.
Ya ce gidan gajiyayyu na shiyyar Birniwa yana cikin kyakkyawan yanayi da kulawa sosai ta fuskar abinci da sutura da kayan wanka da na wanki da sauran bukatun rayuwa, dan haka gwamnati ta kuduri niyyar gyara sauran gidajen gajiyayyun domin kyautata yanayinsu.
Malam Sale Zakar ya ce an Kara yawan mata masu juna biyu da masu shayarwa da ke amfana da Shirin kula da lafiyar iyali daga 20 zuwa 30 a mazabun jihar 287.
Ya kara da cewa za kuma a kara yawan masu amfana da tallafin masu bukata ta musamman daga 150 zuwa 200 a kowacce karamar hukuma, inda masu bukata ta musamman 540 ke samun tallafin naira 10, 000 a duk wata.
A nasa jawabin shugaban kwamatin harkokin mata na majalisar dokokin jihar Jigawa kuma wakilin mazabar Birnin Kudu Alhaji Muhammad Kabiru Ibrahim ya bayyana gamsuwa da tanade tanaden da aka yiwa mata da yara da tsoffi da marasa galihu da mata masu juna biyu da masu shayarwa da nakasassu.
Ya kuma yi addua’ar Allah Ya sa kasafin kudin ya yi tasiri wajen inganta rayuwar masu karamin karfi da marasa galihu a sabuwar shekara.