Dilan ƙwaya ya shiga hannu a Borno
Published: 27th, August 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta kama wani mutum da ake zargi da dillancin miyagun ƙwayoyi a Ƙaramar Hukumar Bayo.
An cafke shi ne ranar 23 ga watan Agusta, 2025, yayin wani samame da ’yan sanda suka kai tare da haɗin gwiwar sashen leƙen asiri.
DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Amurka ta ɗaure basaraken Osun kan zamba a tallafin COVID-19Kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya ce an kama wanda ake zargin mai suna Nasiru Ibrahim da fakiti 25 na tabar wiwi.
Ragowar ƙwayoyin da aka samu a wajensa sun haɗa da fakiti 34 na ƙwayar Exzol, da kuma ƙwayar D5 guda 600.
An miƙa shi tare da kayan da aka ƙwato zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar domin ci gaba da bincike kafin gurfanar da shi a gaban kotu.
Rundunar ta jaddada aniyarta na yaƙi da miyagun laifuka, musamman ta’ammali da ƙwayoyi, waɗanda ke jawo matsalolin tsaro a cikin al’umma.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda Bayo Ƙwaya Tabar wiwi zargi
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno
Sojojin Najeriya sun kashe aƙalla mayakan ƙungiyar ISWAP 8, ciki har da manyan kwamandojinta biyu a Jihar Borno.
Wata majiyar leƙen asiri daga rundunar haɗin kai ta OPHK ta bayyana cewa an kashe ’yan ta’addan ne a wata arangama da suka yi da sojojin a kan hanyar Maiduguri zuwa Baga a safiyar ranar Litinin.
DSS ta maka Sowore da Facebook a Kotu kan cin zarafin Tinubu Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabalaA cewar majiyoyin, an yi arangamar ce a kusa da Garin Giwa da ke gab da ƙauyen Kauwa, lokacin da ’yan ta’addan suka yi wa dakarun da ke sintiri kwanton ɓauna.
“A yayin wannan artabu, an kashe ’yan ta’adda takwas, ciki har da Munzirs biyu (kwamandojin filin daga na ƙungiyar) da kuma Qaid ɗaya (shugaban sashe).
“An kashe Modu Dogo, Munzir daga Dogon Chukun, wani Munzir da ba a bayyana ba, da Abu Aisha, shugaban sashe (Qaid) daga Tumbun Mota,” in ji wata majiya.
Majiyar ta ƙara da cewa wasu mayaƙa da dama sun samu raunuka, musamman waɗanda suka tsere da ƙafa bayan sun yi watsi da babura 14 da sojojin suka ƙwato.