Iran, Rasha da China, sun fara wani atisayin sojojin ruwa a kusa da tashar ruwa ta Chabahar
Published: 9th, March 2025 GMT
Ma’aikatar tsaron kasar Sin ta sanar da fara atisayen sojan ruwa na hadin gwiwa da kasashen Rasha da Iran, wanda za a ci gaba da gudanarwa har zuwa mako mai zuwa a kusa da tashar ruwa ta Chabahar ta kasar Iran.
Ma’aikatar tsaron kasar Sin ta sanar a yau Lahadi cewa, kasashen Sin, Rasha da Iran sun fara atisayen jiragen ruwa na hadin gwiwa daga tashar ruwan Chabahar ta Iran ne domin karfafa hadin gwiwa na tsaro tsakanin wadannan kasashe guda uku.
Kwanaki biyu da suka gabata, Beijing ta mayar da martani ga kalaman sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth na cewa kasarsa a shirye take domin shiga kowane irin yaki, kuma idan muna son dakile Sinawa ko wasu, dole ne mu kara karfinmu na yaki, inji sakataren tsron na Amurka.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya ce, kalaman da jami’in na Amurka ya yi suna haifar da sabani da kuma yada abin kasar Sin ke kallonsa a matsayin barazana ga kasarta.
Lin ya kara da cewa, “Muna kira ga Amurka da ta daina gina tunaninta akan masaniyarta dangane da Sin a lokutan baya, musamman lokacin yakin cacar baki, domin kuwa a yanzu Sin ba wadda Amurka ta san ice a lokutan baya ba.
Sakataren tsaron Amurka ya fada a wata hira da kafar yada labarai ta Fox News a ranar Larabar da ta gabata cewa, Amurka ta shirya tsaf domin shiga kowane irin yaki a duniya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Dokokin Akwa Ibom ta yi fatali da ƙudurin neman hana cin naman kare
Majalisar Dokokin Jihar Akwa Ibom ta ƙi amincewa da wani kudiri da ya nemi haramta ci da sayar da naman kare a jihar.
Kudirin, wanda ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Etinan, Uduak Ekpoufot ya gabatar ranar Talata, bai samu ko da dan majalisa daya da ya mara masa baya ba.
Yau Majalisar Dattawa za ta tantance sabon Ministan Tsaro Mako mai Majalisa za ta kada ƙuri’a kan ƙudurin ƙirƙirar sabbin jihohiJaridar nan ta gano cewa Uduak ya roki majalisar da ta yi la’akari da matsalolin kiwon lafiya da ke tattare da cin nama kare, yana gargadin cewa yadda ake yanka dabbobin ba tare da tsafta ba na iya jefa masu cin nama cikin haɗarin kamuwa da cututtuka irin su rabies, salmonella, trichinella da sauran kwayoyin cuta.
Ya kuma bayyana hanyoyin da ake amfani da su wajen kashe karnuka a kasuwancin a matsayin na rashin tausayi.
Duk da hujjojin da ya gabatar, babu wani ɗan majalisa da ya goyi bayan kudirin, lamarin da ya tilasta wa kakakin majalisar ya yi hukunci da cewa an ƙi amincewa da shi.
Akwai dai sassa da dama na Najeriya, musamman a kudancin kasar nan da ma wasu sass ana Arewacin kasar da ke cin nama kare.
A farkon wannan shekara, wani masani kan namun daji, Edem Eniang, ya ce mata ’yan Najeriya suna cin nama kare fiye da maza, bisa wasu al’adu da ke ɗaukar cewa naman yana inganta laushin fata.
Ya ce wannan al’ada ta fara fitowa fili ne a wata lakca da wani masanin dabbobi, Richard King, ya gabatar.
Eniang ya kuma nuna damuwa kan raguwar adadin karnuka saboda yawan cin naman su da ake yi.
Ya ba da misalan wasu lamarin da suka faru a Ibeno da Oron a jihar ta Akwa Ibom, inda aka sace karnuka aka yanka su don abinci, cikin su har da wata karya mai shayarwa da ’ya’yanta ƙanana.