Senegal, Ta Karbi Wasu Sansanonin Sojin Faransa A Kasar
Published: 9th, March 2025 GMT
Senegal ta karbi wasu sansanonin soja na faransa a kasar a wani bangare na janye sojojin faransar daga kasar ta Yammacin Afirka.
Ofishin jakadancin Faransa a Dakar ya sanar da cewa an mika wurare da gidaje a yankunan Marechal da Saint-Exupery na Dakar ga hannun gwamnatin Senegal.
Sauran kuma “za a mika su ne kamar yadda bangarorin biyu suka amince da jadawalin da suka sanya wa hannu”.
A ranar 12 ga Fabrairu Faransa ta sanar cewa ta kafa wani kwamiti na hadin gwiwa da Senegal da zai shirya tsare-tsaren ficewar sojojin Faransa da kuma mika sansanonin zuwa karshen shekarar nan.
“Kwamitin ya kuma kaddamar da aikin yin garen-bawul ga hadakar tsaro,” a cewar sanarwar.
A watan Nuwamban 2024 ne Shugaba Bassirou Diomaye Faye wanda ya lashe zabe bisa akidar kawo sauyi, ya bayyana cewa duka sojojin Faransa da na kasashen waje za su fita daga Senegal zuwa karshen 2025.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kungiyar M-23 Ta Kasar Kongo Ta Kara Nusawa Gaba A Don Mamaye Karin Yankuna A Gabacin Kongo
Yan tawayen M-23 na kasar Kongo wadanda suke samun goyon bayan gwamnatin kasar Ruwanda sun kara nosawa zuwa gaba a mamayar da sukewa gabancin kasar ta Kongo.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa yan tawayen sun kama garin Walikale a jiya Laraba kuma a halin yanzun sun kokarin zuwa sauran garuruwa a yankin.
Labarin ya kara da cewa wannan labarin na zuwa ne a dai dai lokacinda shuwagabanninkasashen Kongo da Rwanda suke kira ga bangarorin biyu su tsagaita budewa juna wuta su kuma dawo kan teburin tattaunawa.
Wani mazaunin garin walikale ya fadawa reuters yana jin karar bindigogi a garin Nyabangi wanda yake kusa da inda yake.
Janvier Kabutwa yace, yan tawayen sun afafatawa da sojojin Gwamnati da kuma sojojin sa kai a garin bayan da mayakan M-23 suka tunkari sansanin sojojin gwamnati a garin.