2025-05-07@18:46:36 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2940

«Sauya Sheƙa»:

      Rundunar sojan Ruwan Amurka ta sanar da cewa; Jirgin sama samfurin F-18 wanda kudinsa ya kai dalar Amurka miliyan 67 ya fadi akan jirgin dakon jiragen ruwa na ” USS Harry Truman” a tekun “Red Sea”. Jaridar ” Washington Post” ta buga labarin dake cewa; Jirgin ta fado ne a lokacin da yake kokarin sauka...
    A yau Laraba kungiyar kare hakkin bil’adama ta “Amnesty Interantional” ta fitar da rahoto da a ciki ta yi kira ga HKI da ta kawo karshen shirinta na korar Falasdinawa daga Gaza da karfi, tare da cewa; Har yanzu Isra’ilan tana ci gaba da tafka laifukan yaki a Gaza da yi wa mutane kisan kiyashi.”...
    Wani rahoto na musamman da HKI ta gudanar akan asarar da ta fuskanta sanadiyyar yaki da Hizbullah, ya bayyana cewa, a fagen aikin gona kawai sun yi asarar dalar Amurka miliyan 108 wacce ta fara daga 8 ga watan Oktoba 2023. Kungiyar ReGrow Israel” ta ce, yakin da aka yi da Hizbullah ya yi barna...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayana labarummu na yau zai yi magana dangane da ‘Mahangar Jumhuriyar Musulunci na Iran ta yadda za’a kai ga fahintar juna a tattaunawanta da kasar Amurka da suke yi wanda ni tahir amin zan karanta. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi a wata tattaunawa ta wayar tarho da tokwaransa...
    Al’ummar garin Izge da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza ta Jihar Borno sun fatattaki ’yan ƙungiyar Boko Haram bayan kai musu hari a ranar Laraba. Ƙungiyar ‘yan ta’addan ta kuma kashe wani kaftin ɗin soji a harbin na ba zata. Jami’an tsaro na ba da gudunmawar aikata miyagun laifuka a Nijeriya — Zulum Jami’an tsaro na...
    “Dole ne mu daina tallata miyagun ayyukan ‘yan ta’adda. Dole ne mu cire su daga jerin shafukan manyan labarai na jaridunmu, mu rahoto ayyukansu a matsayin masu aikata laifuka, sannan mu kore labaran karya.”   Ministan ya jaddada cewa, kungiyoyin ta’addanci da masu aikata laifuka sukan yi amfani da kafafen yada labarai da shafukan sada...
    Ma’aikatar kula da harkokin cinikayya ta kasar Sin, ta ce sabuwar gwamnatin Amurka ta dauki jerin matakan kakaba haraji na ba gaira ba dalili, lamarin da ya kawo tsaiko ga dangantakar cinikayya da tattalin arziki tsakanin kasashen biyu da ma tsarin cinikayya da tattalin arziki na duniya, tare da kawo kalubale mai tsanani ga farfadowar...
    Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya yi zargin cewa sojoji da sauran jami’an tsaro na bayar da gudunmawar aikata miyagun laifuka da cin zarafin jama’a a Nijeriya. Zulum ya faɗi hakan ne yayin da yake haramta sayar da barasa a birnin Maiduguri da kewaye. Ka-ce-na-cen da ya biyo bayan ziyarar Tinubu a Katsina DAGA...
      Duk da yadda Amurka ke haifar wa tattalin arzikin duk fadin duniya da barazana da kalubale bisa matakin harajin kwastam da ta kara kakkaba wa sauran kasashen, da yanayi maras tabbas da Sin take fuskanta a waje, ingancin tattalin arzikin Sin yana shaida abun da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fada, wato tattalin...
    Malam Bala Dutse, wanda ɗansa Amadu yana cikin waɗanda aka kashe, ya bayyana cewa gwamnati na ƙoƙarin mantawa da al’amarin. “An ce an kama wasu, amma har yau ba mu ji komai ba. Na rasa ɗana, kuma rayuwata ta shiga taka mai wuya. Mafi ƙaranci, gwamnati ta fito ta faɗa mana abin da ke faruwa,”...
    Gwamnan Jihar Katsina Umaru Dikko Raɗɗa, ya ce ba shi da masaniyar wani allo da aka kafa mai ɗauke da saƙon ce wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu babu ƙorafi a Katsina ba kamar yadda ake ta muhawara a kai a ƙasar. Hakan na ƙunshe cikin wani saƙon murya ta gwamnan da aka fitar da...
    Kasashen duniya na ci gaba da nuna matukar damuwa game da rikicin da ya barke tsakanin Pakistan da Indiya. Iran na daga cikn jerin kasashen da a baya bayan nan suka nuna damuwa. Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Iran ta fitar ta ce “Jamhuriyar Musulunci ta bayyana matukar damuwarta kan yadda takun saka tsakanin Indiya...
    Kungiyar gwagwarmaya ta Ansarullah ta bayyana cewa yarjejeniyar tsagaiat wutar da ta cimma da Amurka, ba ta sauya matsayin kasar ba na kai wa Isra’ila hari. Kakakin kungiyar Ansarullah Mohammed Abdul-Salam ya jaddada cewa Dakarun Yeman za su ci gaba da kai hare-hare kan Isra’ila domin goyan bayan Falasdinawa a zirin Gaza. Yarjejeniyar da Amurka...
    Sai dai, rikice-rikicen cikin gida da matsalolin tsaro da tattalin arziƙi sun sa gwamnatin ke ci gaba da yin gyare-gyare don samar da hanyoyin da za su ba ta kariya da cikakken iko kan harkokin leƙen asiri da tsaro. Wannan mataki yana iya nuni da cewa Nijar na ƙoƙarin zama mai dogaro da kai a...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk shekara, dalibai kan rubuta jarabawa a matakai daban-daban na makarantu daban-daban. Ɗaya daga cikin nau’ukan jarabawa da ɗaliban Najeriya suke yi ita ce Jarabawar Neman Shiga Manyan Makarantu, wato UTME. Kamar kowace shekara, a bana ma ɗalibai sun rubuta wannan jarabawa kuma a cewar Hukumar Shirya Jarabawar...
    Yaƙi ya ɓarke tsakanin Indiya da Pakistan yayin da a safiyar wannan Larabar ƙasashen biyu suka riƙa yi wa juna musayar wuta da manyan makaman atilari. Hakan na zuwa ne bayan harin da Indiya ƙaddamar kan Islamabad da sassafe, lamarin da ke nuna ɓarkewar rikici tsakanin maƙwaftan biyu masu makaman nukiliya. Indiya ta ce ta...
    A ranar Litinin ne hukumar JAMB ta bayyana cewa daga cikin ɗalibai miliyan 1.95 da suka zauna jarabawar bana, kusan miliyan 1.53 — wato kashi 78 cikin 100 — ba su samu maki 200 ba. Sai dai ɗalibai 12,414 kacal suka samu maki 300 ko sama da haka. Ministan ya jaddada cewa wannan mataki na...
    Kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen ta mabiya Al-Houthi ta sanar da cewa: Sanarwar da shugaban Amurka ta fitar kan Yemen gazawa ce ga Netanyahu Kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen ta sanar a jiya Talata cewa: Sanarwar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi dangane da kasar Yemen gazawa ce ga Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar...
    Gwamnatin kasar Indiya ta yi luguden makamai masu linzami kan kasar Pakistan, yayin da Pakistan ta sha alwashin mayar da martani Gwamnatin Indiya ta kai hare-haren makamai masu linzami kan wasu wurare a kasar Pakistan da yammacin jiya Talata, kuma sojojin Pakistan sun sha alwashin mayar da martini, yayin da ake ci gaba da samun...
    Kasar Sudan ta yanke huldar jakadancinta da kasar Hadaddiyar Daulart Larabawa tana mai ayyana UAE a matsayin ‘kasa mai cin zali’ Kamfanin dillancin labaran Sudan (SUNA) ya watsa rahoton cewa: Kwamitin tsaro da kula da matakan tsaron kasar Sudan ya sanar a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Talata cewa: Sudan ta yanke...
    Da yake tsokaci game da wasan na karshe na jiya, Mark Williams daga yankin Wales, ya ce Zhao abokin karawa ne mai hazaka. Don haka ba abun da zai fada game da shi illa jinjinawa. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
    Wata ƙungiya mai rajin kare muradun al’ummar Hausawa a Nijeriya mai suna Kungiyar Hausawan Nijeriya ta tsaya kai da fata cewa dole a ƙyale Hausawa su kafa ƙungiyarsu kamar kowacce ƙabila tun da dai doka ba ta hana su ba. Martanin nasu na zuwa ne a daidai lokacin da masu kiran ke shan sukar cewa...
    Majalisar Dattawa ta kafa kwamiti mai mambobi 18 domin sanya idanu kan yadda gwamnan riƙo na Jihar Ribas Vice Admiral Ibok Ete Ibas mai ritaya ke tafi da aikinsa. Majalisar ta ce ta ɗauki matakin ne a wani yuƙuri na ƙarfafa shugabanci na gari ba tare da rufa-rufa ba a jihar da ke kudu maso...
    Trump ya bayyana cewa, waɗanda suka zabi barin ƙasar da kansu na iya samun dama ta hanyar doka don dawowa cikin Amurka nan gaba idan suka cika ka’idojin da suka dace.   A cewar rahoton, an riga an sayo tikitin jirgi ga mutum na farko da ya karɓi wannan tayin — daga birnin Chicago zuwa...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaaei ya bukaci kasashen turai da su shiga a dama da su kan tattaunawa dangane da shirin nukliyar kasar Iran na zaman lafiya. Ya kuma jaddada cewa Iran tana turjiya ga dukkan tunanin Amurka na wargaza shirin Nukliyar kasar Iran kwata-kwata. Baghaei ya kara da cewa duk da...
    A yau, rukunin farko na tawagar wanzar da zaman lafiya da martanin gaggawa na kasar Sin kashi na biyu wadda za ta je yankin Abyei, ya tashi daga birnin Zhengzhou na kasar Sin, da jirgin saman soja domin gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya na tsawon watanni 12. Bugu da kari, ana shirin tura...
    Kawamcen jam’iyyun siyasa na kasar Ivory Coast ya bukaci a sake lalen yadda aka tsara yadda ake ristar jam’iyyu a hukumar zaben kasar, ganin yadda ta hana rijistar wasu jam’iyyun saboda dalilai daban daban. Shafin yanar gizo na labarai Afirka news ya bayyana cewa an kafa kawancen ne wanda aka sanyawa suna CAP-CI a farkon...
    A safiyar yau ne jiragen yakin HKI suka kai hare-hare kan tashar Jiragen sama na birnin San’a na kasar Yemen inda ake ganin hakan kara ruruta wutan yaki a yankin ne. Klamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a dai-dai lokacinda jiragen yakin Amurka suka dauki kimani watannin biyu suka kai hare...
    Karamar Hukumar Birnin Kdu tace tana nazarin samar da cibiyar horas da maniyyata aikin hajji ta dindindin a yankin domin karawa mahajjata kaimi wajen gudanar da aikin karbabbe.   Shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Muhammad Uba Builder ya bada wannan tabbacin a lokacin rufe bitar da aka shiryawa maniyyatan yankin na Birnin kuudu.   Yana mai...
    Friedrich Merz na jam’iyyar CDU ya zama sabon shugaban gwamnatin Jamus. Majalisar Dokokin Jamus ta Bundestag ta zabi Merz a matsayin sabon shugaban gwamnati lokacin zaɓen zagaye na biyu, bayan ya gaza samun ƙuri’un da yake buƙata a zagayen farko na zaɓen. A zaɓen farko Merz ya samu ƙuri’u 325 na jam’iyyun ƙawance daga majalisar...
    A bidiyon da wani mai suna Nawab Sheikh ya fitar na nuna yadda ya hau motarsa, wacce yake tuka ta a kan titunan birnin Murshidabad a cikin ƙasar Indiya, don nishaɗantar da mahaya babur, wanda ya sa bidiyon yake ta yaɗuwa a shafin sada zumunta na Instagram. Babu wani wuri mafi kyawun nuna bajintar kirkira...
    Wani matashi dan shekarar 20 ya fada hannun hukuma kan zargin kashe mahaifinsa da adda a Jihar Jigawa. Rundunar ’yan sandan Jihar Jigawa ta kama wanda ake zargin kashe mahaifinsa mai shekara 57, da adda. Wanda aka kashe ya samu raunuka a kafadarsa da wuya da kirjinsa, kuma an kai shi Babban Asibitin Tarayya (FMC)...
    Ya gode wa jami’an tsaro da ‘yan banga bisa ƙoƙarinsu, amma ya buƙaci su ƙara ƙaimi don hana faruwar irin haka a gaba. Shugaban ya kuma buƙaci shugabannin al’umma, jami’an tsaro da mazauna yankin su haɗa hannu don kawo ƙarshen rikicin da tabbatar da zaman lafiya. Gyang ya roƙi Allah Ya bai wa iyalan waɗanda...
    Mambobin Jam’iyyar PDP shida a Majlisar Wakilai daga Jihar Delta sun sauya sheka zuwa Jam’iyya APC. Kazalika wasu biyu daga Jihar Enugu sun sauya sheka daga Jam’iyyar adawa ta LP zuwa PDP. Shugaban Majalisar Wakiliai, Abbas Tajuddeen, ne ya sanar da hakan bayan dawowar majalisar daga hutu a ranar Talata. Shugaban Majalisar ya bayyana cewa ’yan...
    Akalla mutum shida ne aka tabbatar da mutuwarsu a wani sabon hari Karamar Hukumar Barikin Ladi da ke Jihar Filato. ’Yan bindigar sun kuma jikkata mutane da dama a hare-haren da suka kai unguwannin  Marit da Gashish a ranar Litini. Aminiya ta samu labarin cewa an garzaya da wadanda suka ji raunin asibiti, bayan harin...
    Wani sabon rikici ya dabaibaye Hukumar Raya Yankin Arewa maso Yamma (NWDC) kan shirin daukar nauyin dalibai zuwa karatu a kasashen waje. Wannan dambarwar ta kunno kai ne bayan sanarwar da hukumar ta fitar na shirin daukar nauyin daliba domin karatun jami’a daga yankin. Majalisar Amintattun Hukumar ta ce ba a taba tattaunawa kan shirin...
    Hukumar Kula da Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna za ta fara jigilar maniyyata zuwa kasar Saudiyya a ranar 14 ga watan Mayu, 2025. Shugaban hukumar, Malam Salihu S. Abubakar, ne ya bayyana hakan a wani shirin rediyo kai tsaye da aka watsa daga Kaduna, inda ya bayyana shirye-shiryen da jihar ta kammala domin aikin...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yin gwagwarmaya ko fafutuka wani abu ne da ke cikin jinin dan Adam, musamman idan yana kokarin ganin an samu sauyi ko cigaba a al’umma. Sai dai a Najeriya, sau da yawa ana danganta kalmar “gwagwarmaya” da rikici ko sabani da gwamnati. NAJERIYA A YAU: Abin da ke...
    Ya ƙara da cewa Ganduje mutum ne da kullum yana cikin yi wa ma’aikatansa fara’a. Ya ce masu yaɗa bidiyon na ƙoƙarin tada rikici ne domin dalilan siyasa. “Wannan ba zai rage farin jinin Ganduje ba,” in ji shi. “Ya yi wa Jihar Kano aiki tuƙuru, yanzu kuma yana yi wa ƙasa. ‘Yan adawa ba...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yin gwagwarmaya ko fafutuka wani abu ne da ke cikin jinin dan Adam, musamman idan yana kokarin ganin an samu sauyi ko cigaba a al’umma. Sai dai a Najeriya, sau da yawa ana danganta kalmar “gwagwarmaya” da rikici ko sabani da gwamnati. NAJERIYA A YAU: Abin da ke...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da zaluncin ‘yan sahayoniyya a kan kasar Yemen Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi kakkausar suka kan harin wuce gona da iri da sojojin yahudawan sahayoniyya suka kai tashar jiragen ruwa na Hodeidah da sauran ababen more rayuwa na kasar Yemen, yana mai...
    Jamhuriayar Musulunci ta Iran ta sha alwashin mayar da martani cikin gaggawa ga duk wani kasadan ‘yan Sahayoniyya da Amurka kan kasarta Jakada kuma zaunannen wakilin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani ya jaddada cewa: Duk wani kasadan harin soji da Amurka ko wakilliyarta gwamnatin ‘yan  sahayoniyya suke yi, ko...
    A wani bangare na wasikar na cewa, “An umurce ni da in isar da amincewar Gwamnati na fitar da jimillar kudi Naira miliyan 15,227,272.72 a asusun kowace karamar hukuma domin gyaran motoci biyu tare da siyo karin wasu guda hudu ga Majalisar masarautar Kano wanda kamfanin Sottom Synergy Resources Ltd zai dauki nauyin siyowa.  ...
    Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da “Bankasar tattalin arzikin Iran duk tare da takunkuman tattalin arziki masu tsanani wadanda kasashen yamma musamman Amurka suka doramata, wanda ni tahir amin zan karanta. ////…A dai-dai lokacinda gwamnatin kasar Amurka take barazanar zata hana sayan danyen man fetur daga kasar Iran kwatakwata,...
    Bisa kididdigar da kamfanin layin dogo na kasar Sin ya fitar, daga fara zirga-zirgar hutun ranar ma’aikata a ranar 29 ga Afrilu zuwa ranar 4 ga Mayu, jiragen kasa na kasar Sin sun yi jigilar fasinjoji miliyan 112, adadin da ya karu da kashi 10.5 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara,...
    ’Yan bindiga sun kashe wata mata da suka sace tare da mijinta Yakubu Dada watanni bakwai da suka gabata a yankin Kontagora da ke Jihar Neja. Aminiya ta ruwaito cewa ’yan ta’addan sun halaka matar mai suna Lami bayan karɓar Naira miliyan 10 kuɗin fansa. ’Yan fashi sun kashe matashi a Kano Kwankwaso: Abba ya...
    An labarto cewa harin ya wakana ne da safiyar ranar Lahadi kuma ‘yan bindigan sun yi awun gaba da shanu da sauran dabbobin al’umman yankin a yayin farmaƙin.   Kazalika, wakilinmu ya gano cewa baya ga ‘yan bijilante da suka rasa rayukansu akwai wasu fararen hula mazauna ƙauyen Sabuwar Sara su ma sun gamu da...
    Ana fargabar cewa wasu da ake zargin ’yan fashi da makami ne sun kashe wani matashi a unguwar Ɗanbare da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano. Bayanai sun ce waɗanda ake zargin sun kashe matashin ne mai suna Shuaibu Muhammad da adda, bayan sun shiga gidan da yake zaune da nufin sata. Wani abokin...
    A cikin wata daya kadai sojojin HKI sun rushe gidajen Falasdinawa 152 a yammacin Kogin Jordan. Majiyar Falasdinawa ta ambaci cewa a kudancin garin Khalil ‘yan mamayar sun rushe gidaje 25 da kuma wasu cibiyoyi, da hakan ya sa adadin gidajen da su ka rushe zuwa 152 kamar yadda hukumar Falasdinu ta ambata. Bugu da...