’Yan Najeriya miliyan 34 na cikin barazanar yunwa
Published: 1st, August 2025 GMT
Akalla ’yan gudun hijira miliyan daya da dubu 400 da ke Arewa maso gabashin Najeriya ne suke fuskantar barazanar yunwa bayan yanje tallafin da Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ke bayarwa.
Wani rahoton majalisar a kan abinci da tsaro wanda gwamnatin Najeriya, Shirin Kula da Abinci na Majalisar (FAO) da sauran masu ruwa da tsaki a baya dai sun yi hasashen ’yan Najeriya miliyan 33.
Hakan dai na nufin a yanzu yan kasar miliyan 34.7 ne ke nan suke cikin barazanar yunwar.
Ofishin Majalisar mai kula da Agaji (UNOCHA), a rahotonsa na mai taken “Najeriya a 2025 bukatun agajinta da kuma hanyoyin magance su” ya yi bayani daki-daki kan kalubalen da ake fuskanta a jihohin Adamawa da Borno da kuma Yobe.
Rahoton ya ce akwai akalla yara miliyan daya da dubu 800 da kef ama da matsanancin karancin abinci.
Rahoton ya alakanta hakan da ci gaba da karuwar farashin kayayyaki a Najeriya wanda ya kai kaso 40.9 cikin 100 a watan Yunin 2024.
Kazalika, karuwar adadin na da nasaba da rage tallafin da MDD ke bayarwa ba, sanadiyyar yanke mata kudaden tallafin da musamman Amurka ke bayarwa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yunwa
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar Ruwa
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Ambaliyar ruwa na cigaba da salwantar da dukiyoyi da rayukan al’ummomi da dama a sassa daban-daban na Najeriya.
Ko a farkon makon nan, hukumomi sun yi gargadin cewa akwai yiwuwar samun ambaliyar a jihohi akalla 11.
Sai dai wasu alummomin tuni suka dauki matakai don rage barnar da ambaliyar ka iya yi musu.
NAJERIYA A YAU: Masu Nau’in Jinin AS Sun Fi Masu Nau’in AA Lafiya DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau UkuA kan wadannan matakai shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari.
Domin sauke shirin, latsa nan