Afirka ta Kudu na shirin daukar matakan kauce wa tasirin harajin Amurka
Published: 1st, August 2025 GMT
Ministan kasuwanci na Afirka ta Kudu Parks Tau ya fada jiya Alhamis cewa kasarsa na shirin yin shawarwarin kasuwanci da nufin kaucewa harajin kashi 30% na Amurka a kan kasarsa, wanda zai fara aiki daga wannan Juma’a.
A farkon watan Mayu ne Afirka ta Kudu ta gabatar da wani shirin yarjejeniya ta kasuwanci ga gwamnatin Trump, amma kuma gwamnatin Amurka bat a bayar da amsa kan hakan ba.
kuma ta sake duba ta a watan Yuni, ba tare da bayar da amsa ba.
Ya kara da cewa, jami’an Afirka ta Kudu sun yi magana da jami’an Amurka a yammacin Laraba a ofishin jakadancin Washington da ke Pretoria da kuma wakilin kasuwanci na Amurka, amma har yanzu akwai rashin tabbas game da abin da zai faru yayin da wa’adin haraji yake karewa.”
Ya kara da cewa, “Sun ce za su kara mana kwarin gwiwar sake mika kudirinmu, mai yiyuwa ya karfafa gwamnatin Amurka ta sake yin nazari kan batun haraji.”
Amurka ita ce kasa ta biyu wajen cinikayya da kasar Afirka ta Kudu bayan kasar Sin. Afirka ta Kudu na fitar da motoci, wasu kayayyaki da aka kerawa, ‘ya’yan itatuwa, da inabi zuwa Amurka.
Dangantaka tsakanin kasashen biyu ta yi tsami ne kan manufofin karfafa tattalin arziki ga bakaken fata ‘yan Afirka ta Kudu, da nufin magance matsalar rashin daidaito da aka yi a shekaru aru-aru, da kuma batun karar da Afirka ta kudu ta shigar kan kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Haaretz: Sojojin Isra’ila 7 ne suka kashe kansu a watan Yuli August 1, 2025 Gaza: Mutane Da Dama Sun Yi Shahada A Yau Wasu Kuma Sun Jikkata August 1, 2025 Kungiyar AU Ta Yi Watsi Da Kafa Gwamnatin Adawa Da Kungiyar RSF Ta Yi A Sudan August 1, 2025 Shugaban Kasar Iran Zai Ziyarci Pakistan A Gobe Asabar August 1, 2025 Habasha Ta Kaddamar Da Shirin Shuka Bishiyoyi Miliyan 700 A Rana Daya August 1, 2025 Sayyid Abdulmalik Husi: Taimakon Da Ake Jefawa Gaza Ta Sama Yaudara Ce August 1, 2025 Amurka Ta Kakabawa Jami’an Gwamnatin Falasdinawa Takunkuman Hana Shiga Amurka July 31, 2025 Ministan Harkokin Wajen Siriya Yana Rasha Don Bude Sabon Shafi Tsakaninsu July 31, 2025 Kananan Yan Wasan Dabben Gargajiya Na Iran Sun Zama Zakara A Gasar Wannan Shekara July 31, 2025 Canada Zata Amince Da Samuwar Kasar Falasdinu A Taron MDD July 31, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kasar Lebanon Aun Ya Ce Mun Aike Wa Amurka Sakwanni Akan Dakatar Da Hare-haren HKI
Shugaban kasar Lebanon wanda ya gabatar da jawabi da safiyar yau ya ce; A cikin sakwannin da mu ka aike wa Amurka, mun bukaci ganin an kawo karshen hare-haren da Isra’ila take ci gaba da kawo wa Lebanon, ta sama, kasa da ruwa, haka nan kuma kisan gillar da take yi wa mutane a cikin kasar.”
Shugaba Aun ya kuma yi jinjina ga dukkanin shahidan kasar da su ka kwanta dama saboda kare Lebanon,kuma yana a matsayin wani abu ne mai kima da daraja a wurinmu.”
Shugaba Aun na Lebanon ya kuma ce, Isra’ila abokiyar gaba ce wacce take hana mutanen da yaki ya tarwatsa komawa zuwa garuruwansu da kuma sake gina kudancin Lebanon da yaki ya rusa.”
Haka nan kuma ya ce , sojojin Lebanon sun sadaukar da kawukansu ta hanyar kasancewa a tare da mutanen kudancin Lebanon.
Danagen da makaman Hizbullah, Shugaban kasar ya ce nauyi ne da ya rataya a wuyansa da kuma dukkanin ‘yan siyasa da su ga cewa makamai suna hannun gwamnati ne kadai, a hannun soja da jami’an tsaro.”
Har ila yau ya kara da cewa, yanayin da ake ciki baya da bukatuwa da duk wani abu da zai zama tsokana da tayar da hankali, ba kuma za su bari ‘yan ta’adda su cutar da al’umar Lebanon ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sojojin Mamaya Suna Ci Gaba Da Kisan Kiyashi A Gaza July 31, 2025 Kassim: Duk Wanda Yake Neman Hizbullah Ta Ajiye Makamanta Yana Yi Wa Isra’ila Aiki July 31, 2025 Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Yi Allah Wadai Da Takunkumin Da Amurka Ta Kakaba Mata July 31, 2025 Tawagar Iran Ta Fice A Taron Majalisun Dokokin Kasashen Duniya A Lokacin Jawabin Wakilin Isra’ila July 31, 2025 Kasar Iran Ta Bayyana Gushewar Hasashen Raunin Karfin Sojinta Kuma Ba Zai Dawo Ba July 31, 2025 Sojan Amurka Ya Bada Ruwayar Yadda Sojojin Sahayoniyya Suka Kashe Wani Yaro Balasdine July 31, 2025 Sojojin Yemen Sun Kai Zafafan Hare-Hare Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Guda Uku July 31, 2025 Qolibaf: Barin HKI Ta Yi Abinda Taga Dama Ne Yana Karfafa Mata Giwa July 30, 2025 Yunwa Ta Kashe Karin Falasdinawa 7 A Gaza July 30, 2025 Malta Zata Amince da Samuwar Falasdinu a Cikin Watan Satumba Mai Zuwa July 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci