Shugaban Kasar Iran Zai Ziyarci Pakistan A Gobe Asabar
Published: 1st, August 2025 GMT
Kamfanin dillancin labarun ” Mehr” ya bayyana cewa; Ziyarar da shugaban kasar ta Iran zai kai zuwa Pakistan amsa karan Fira minister Shahbaz Sharif ne.
Bugu da kari ziyarar za a yi ta ne a daidai lokacin da wannan yankin yake fama da sauye-sauye, haka nan kuma za ta mayar da hankali wajen bunkasa alakar kasashen biyu.
Majiyar kasashen biyu, Iran da Pakistan sun ce shugaban kasar ta Iran Mas’ud Fizishkiyan zai fara ziyarar tashi daga birnin Lahor ne, inda zai ziyarci hubbaren shahararren masanin kasar Allamha Muhammad Iqbal, sannan ya nufi binrin Islamaabab domin ganawa da jmai’an gwamnatin kasar.Daga cikin wadanda zai gana da su a can babban birnin kasar da akwai ‘yan siyasa da kuma jami’an soja da su ka hada da shugaban kasa Ali Zardari da Fira minister Shahbaz Sharif.
Bugu da kari shugaban kasar ta Iran zai gana da masanan kasar ta Pakistan da kuma ‘yan kasuwa domin bunkasa alakar tattalinn arziki da alakar al’adu da addini a tsakanin kasashen biyu.
Ta fuskar kasuwancin kuwa,kasashen biyu suna son ganin an kara yawan musayar haja a tsakaninsu domin ta haura dala biliyan 3.
Wannan dai ita ce Ziyara ta biyu da shugaban kasar Iran zai kai kasar Pakistan a cikin shekaru biyu. A cikin watan Aprilu 2024, shugaban kasar Iran shahida Ibrahim Ra’isi ya ziyarci Pakistan.
Watanni biyu da su ka gabata Fira Ministan kasar ta Pakistan Shahbaz Sharif ya kawo Ziyara Iran.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Habasha Ta Kaddamar Da Shirin Shuka Bishiyoyi Miliyan 700 A Rana Daya August 1, 2025 Sayyid Abdulmalik Husi: Taimakon Da Ake Jefawa Gaza Ta Sama Yaudara Ce August 1, 2025 Amurka Ta Kakabawa Jami’an Gwamnatin Falasdinawa Takunkuman Hana Shiga Amurka July 31, 2025 Ministan Harkokin Wajen Siriya Yana Rasha Don Bude Sabon Shafi Tsakaninsu July 31, 2025 Kananan Yan Wasan Dabben Gargajiya Na Iran Sun Zama Zakara A Gasar Wannan Shekara July 31, 2025 Canada Zata Amince Da Samuwar Kasar Falasdinu A Taron MDD July 31, 2025 Shugaban Kasar Lebanon Aun Ya Ce Mun Aike Wa Amurka Sakwanni Akan Dakatar Da Hare-haren HKI July 31, 2025 Sojojin Mamaya Suna Ci Gaba Da Kisan Kiyashi A Gaza July 31, 2025 Kassim: Duk Wanda Yake Neman Hizbullah Ta Ajiye Makamanta Yana Yi Wa Isra’ila Aiki July 31, 2025 Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Yi Allah Wadai Da Takunkumin Da Amurka Ta Kakaba Mata July 31, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: shugaban kasar
এছাড়াও পড়ুন:
Burkina Faso: Masu Ikirarin Jihadi Sun Kashe Fararen Hula 50 A Cikin Watanni Hudu
Hukumar kare hakkin bil’adama ta “Human Right Watch” ta fitar da wani rahoto da a cikin ta bayyana cewa; kungiyar nan mai ikirarin jihadi a kasar Burkina Faso, ( Jama’at Nusratul-Islam wal Muslimin) da kuma kungiyar Daular Musulunci a cikin yankin Sahara, sun kashe fararen hula 50 daga watan Mayu zuwa yanzu.
Rahoton ya ci gaba da yin bayanin cewa, a cikin Ogusta kungiyoyin na masu riya cewa suna yin jihadi sun kashe mutane 40 a cikin garuruwan Djibo da Youba.
Rahoton ya kuma ce; a watan Yuli kuwa kungiyar IS ta kai wa fararen hula hari da suke kan hanyar kai kayan agaji zuwa garin Gorom-Gorom da aka killace da hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 9.
Kungiyar kare hakkin bil’adama din ta ce, wadannan irin hare-haren sun sabawa dokokin kasa da kasa na jin kai, kuma suna a matsayin laifukan yaki.
Kungiyar kare hakkin bil’adaman ta “Human Right Watch” ta mika sakamakon binciken da ta gabatar ga hukumomin tsaro da na shari’a na kasar ta Burkina Faso. Sai dai har yanzu babu wani martani da ta samu.
Shekaru 3 kenan da kasar ta Burkan Faso take a karkashin mulkin soja da su ka sha alwashin kawo karshen masu tayar da kayar baya da sunan jihadi.
Tun daga 2016 ne kungiyoyin dake dauke da makamai suke kai hare-hare a sassa mabanbanta na kasar ta Burkina Faso da sunan jihadi.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Fira Ministan Spain: Bai Kamata A Rika Barin “Isr’ila” Tana Shiga Gasar September 15, 2025 Shugaban Kasar Iran Ya Gana Da Sarkin Kasar Qatar A Birnin Doha September 15, 2025 Dan Kasar Iran Mai Kirkira Ya Sami Kyautar Yabo A Kasar China September 15, 2025 Fizishkiyan: Wajibi Ne Musulmi Su Hada Kai Domin Dakatar Da Laifukan HKI September 15, 2025 Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Qatar, Turkiyya, Pakistan Da Labanon A Doha September 15, 2025 Kwamitin Kolin Tsron Kasar Iran Ya Amince Da Yarjejeniyar Da Aka Cimma Da Hukumar IAEA September 15, 2025 Jami’in Kasar Yemen Ya Aike Da Sako Ga Mahalarta Taron Birnin Doha Na Kasar Qatar September 15, 2025 Yawan Mutanen Da Suka Yi Shahada Sakamakon Kisan Kiyashin ‘Yan Sahayoniyya A Gaza Ya Kusaci 65,000 September 15, 2025 Gwamnatin Sudan Ta Ce: Babu Sulhu Da ‘Yan Tawayen Kasar Na Kungiyar Rapid Support Forces September 15, 2025 Kasashen Larabawa da na Musulmi na taron gaggawa kan harin Isra’ila a Qatar September 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci