Aminiya:
2025-08-01@22:25:10 GMT

Mun ci ribar Naira biliyan 414 a cikin wata 6 a Najeriya – Kamfanin MTN

Published: 1st, August 2025 GMT

Kamfanin sadarwa na MTN ya sanar da cin ribar Naira biliyan 414 a watanni shida na farkon shekarar 2025 a Najeriya.

Kamfanin ya bayyana hakan ne a rahotonsa na karshen wata shidan da ya gabatar a gaban Hukumar da ke Kula da Kasuwar Hannun Jari ta Najeriya a ranar Alhamis.

Za a kashe biliyan 712.26 don yi wa filin jirgin saman Legas garanbawul NAJERIYA A YAU: Me dokar kasa ta ce kan karin wa’adin aiki da Shugaban Kasa ke yi?

A cewar rahoton, kamfanin ya kuma tafka asarar da ta kai ta Naira biliyan 90 saboda musayar kudaden kasashen waje.

Rahoton ya kuma ce jimillar abin da kamfanin ya samu a tsawon lokacin kafin a cire riba ya kai Naira tiriliyan daya da biliyan 200.

Kazalika, MTN ya ce kudaden shigar da ya samu daga kiran waya a watannin sun kai biliyan 887, yayin da na data kuma suka kai tiriliyan 1.23.

Kamfanin dai ya alakanta nasarorin da ya samu da ingantuwar yanayin kasuwanci a Najeriya, ciki har da daidaita farashin Naira da kuma saukar farashin kayayyaki.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Majalisa ta ba NNPCL mako uku ya yi mata bayanin inda tirilyan 210 ta shiga

Kwamitin Majalisar Dattawa na bin Diddigi ya ba Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) wa’adin mako uku ya amsa tambayoyi kan rashin ba da ba’asi kan Naira tiriliyan 210 da ba a san inda suka shiga ba daga shekarar 2017 zuwa 2023.

An dai bayar da wa’adin ne ga shugaban kamfanin na kasa, Bayo Ojulari, wanda ya bayyana a gaban kwamitin ranar Talata, bayan ya bayar da hakuri kan rashin bayyanarsa yayin gayyatar da kwamitin ya yi masa a baya.

Yadda ’yan bindiga sun tarwatsa ƙauyuka sama da 10 a Katsina Gwamnatin Tinubu ta mayar da Arewa saniyar ware – ACF

Kwamitin, wanda ke karkashin jagorancin Ahmed Wadada Aliyu (Nasarawa), ya tsaya kai da fata cewa dole kamfanin ya bayyana inda kudaden suka shiga.

Ojulari dai ya ba kwamitin hakuri, inda ya ce yana bukatar karin lokaci kafin ya iya amsa tuhumar da aka yi masa har guda 19.

Ya kuma ce, “Da kadan na haura kwana 100 a matsayin shugaban wannan kamfanin. Ina bukatar karin lokaci kafin na iya zakulo bayanan da kuka bukata. Wannan kuma na zuwa ne a daidai lokacin da sauran tarin ayyuka ke jira na.

“Ni kaina ina bukatar fahimtar abubuwan da kaina kafin na iya bayar da amsa a kansu. Amma zan je na zauna da sauran ma’aikatana da suka dace mu tattauna domin bayar da abin da ake bukata,” in ji shugaban na NNPCL.

Kodayake mako hudu ya bukata, amma kwamitin ya ba shi mako uku ne domin ya gabatar da bayanan.

Da yake karin haske a kan kudaden, Sanata Wadada ya ce kudaden da ake magana a kan su rubi biyu ne, akwai Naira tiriliyan 103 da kuma Naira tiriliyan 107 da suke bukatar bayanan a kan su.

“Amma fa ba mu ce wadannan kudaden da ake magana a kan su sace su aka yi ko kuma sun bace ba. Abin da kwamitinmu kawai yake kokarin yi shi ne bincike domin gano yadda aka yi tusarrufi da su,” in ji Sanata Wadada.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sin Ta Samu Bunkasar Tafiye-Tafiye Cikin Gida Da Kashi 20.6% A Rabin Farko Na Bana
  • Bashin Naira Tiriliyan 4 Na Barazanar ɗorewar Wutar Lantarki A Nijeriya – Minista
  • Tinubu Ya Cika Alƙawurran Da Ya Ɗauka – Ƙungiyar Gwamnonin Arewa
  • Za a kashe biliyan 712.26 don yi wa filin jirgin saman Legas garanbawul
  • NNPCL ya sake haƙa sabbin rijiyoyin man fetur 4 a Kolmani
  • Kamfanin NNPCL ya sake haka sabbin rijiyoyin man fetur 4 a Kolmani
  • Gwamna Namadi Ya Kaddamar da Tallafin Miliyoyin Naira Ga Ƴan NURTW da Mahauta a Jigawa
  • Gine-gine 8 Sun Ruguje, Makabarta Ta Nutse A Wata Sabuwar Ambaliyar Ruwa A Borno
  • Majalisa ta ba NNPCL mako uku ya yi mata bayanin inda tirilyan 210 ta shiga