Haaretz: Sojojin Isra’ila 7 ne suka kashe kansu a watan Yuli
Published: 1st, August 2025 GMT
Gidan rediyon sojojin Isra’ila ya bayar da rahoto a wannan Alhamis cewa, wani soja ya kashe kansa bayan ya kwashe fiye da kwanaki 300 a cikin sojojin wucin gadi.
Jaridar Haaretz ta Isra’ila ta bayar da rahoton cewa, adadin sojojin da suka kashe kansu a wannan watan kadai ya kai bakwai.
A cikin wannan yanayi, wani bincike na Isra’ila ya nuni da karuwar masu kasha kansu a tsakanin sojojin Isra’ila tun daga lokacin fara yakin zirin Gaza.
Adadin wadanda suka kashe kansu tun daga watan Oktoban 2023 ya haura sojoji 43, ya zuwa ranar da aka fitar da binciken a ranar 16 ga watan Yuli, wanda ke nuna munanan yanayin da suke sakamakon ayyukan kisan kare dangi da suke kan mata da kananan yara da sauran fararen hula a Gaza.
Wani Shafin yanar gizo na Isra’ila ya bayyana cewa, asarar sojojin da Isra’ila ke yi bai takaita ga wadanda aka kashe a wurin yaki ba, hakan ya hada har ma da sojojin da suke kashe kansu saboda damuwa, da kuma masu mutuwa sakamakon raunuka da suka samu.
Bayanai sun nuna cewa sojoji 15,000 ake kula da su sakamakon matsalolin ad suka samu a wajen yaki, kashi 35% daga cikinsu suna fama da matsaloli na kunci da damuwa ko kuma tabuwa ta hankali.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gaza: Mutane Da Dama Sun Yi Shahada A Yau Wasu Kuma Sun Jikkata August 1, 2025 Kungiyar AU Ta Yi Watsi Da Kafa Gwamnatin Adawa Da Kungiyar RSF Ta Yi A Sudan August 1, 2025 Shugaban Kasar Iran Zai Ziyarci Pakistan A Gobe Asabar August 1, 2025 Habasha Ta Kaddamar Da Shirin Shuka Bishiyoyi Miliyan 700 A Rana Daya August 1, 2025 Sayyid Abdulmalik Husi: Taimakon Da Ake Jefawa Gaza Ta Sama Yaudara Ce August 1, 2025 Amurka Ta Kakabawa Jami’an Gwamnatin Falasdinawa Takunkuman Hana Shiga Amurka July 31, 2025 Ministan Harkokin Wajen Siriya Yana Rasha Don Bude Sabon Shafi Tsakaninsu July 31, 2025 Kananan Yan Wasan Dabben Gargajiya Na Iran Sun Zama Zakara A Gasar Wannan Shekara July 31, 2025 Canada Zata Amince Da Samuwar Kasar Falasdinu A Taron MDD July 31, 2025 Shugaban Kasar Lebanon Aun Ya Ce Mun Aike Wa Amurka Sakwanni Akan Dakatar Da Hare-haren HKI July 31, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Qatar Ta Ba Da Tallafin Gaggawa Ga Al’ummar Sudan Bayan Gumurzun El-Fasher
Qatar ta bayar da tallafin gaggawa ga mutanen da suka rasa matsugunansu a Sudan
Gwamnatin Qatar ta aika da agajin gaggawa da tallafin jin kai zuwa birnin Ad-Dabba da ke Jihar Arewacin Sudan domin rage wa dubban mutanen da suka rasa matsuguninsu da ke tserewa daga El Fasher, babban birnin Jihar Arewacin Darfur.
Ma’aikatar Harkokin Waje ta Qatar ta bayyana cewa: “Wannan tallafin ya zo ne a cikin tsarin jajircewar Qatar na tallafawa ‘yan uwantaka na Sudan, musamman idan aka yi la’akari da mawuyacin halin jin kai da fararen hula ke ciki, ciki har da karancin abinci mai tsanani da kuma karuwar bukatar matsugunai da kayan masarufi.”
Sanarwar ta kara da cewa wannan tallafin wani bangare ne na kokarin da Qatar ke yi na tsayawa tare da ‘yan uwantaka na Sudan da kuma rage musu wahalhalun da rikicin yaki da makamai ya haifar. Haka nan ya kunshi rawar da Qatar ke takawa wajen karfafa martanin jin kai da kuma gina gadoji na hadin kai da al’ummar da abin ya shafa a fadin duniya.
Tallafin ya kunshi kimanin buhuhunan abinci 3,000, tantuna 1,650, da sauran kayayyakin bukatu, wanda Asusun Ci Gaban Qatar da kuma Hukumar Ba da Agaji ta Qatar suka bayar, don tallafawa wadanda suka rasa matsuguninsu daga El Fasher da yankunan da ke kewaye. Ana sa ran sama da mutane 50,000 za su amfana daga wannan tallafin, wanda ya haɗa da kafa sansanin agaji na musamman na Qatar mai suna Qatar Charity.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka IAEA : Babu wata shaida da ke nuna cewa Iran na kera makaman nukiliya November 2, 2025 Amurka : zamu dauki matakin soja idan Najeriya ta gaza kawo karshen kashe Kiristoci November 2, 2025 Hamas ta musanta zargin Amurka na cewa tana sace kayan agaji a Gaza November 2, 2025 Wasu Yan Ta’adda Sun Kashe Dakarun Sa Kai 2 A Kudu Maso Gabashin Iran November 2, 2025 Sojojin Amurka Na Kara Fuskantar Venezuwela Adaidai Lokacin da Trump Ke Musanta Batun Kai Hari November 2, 2025 Isra’ila Ta Kashe Mutane 4 Tare Da Jikkata Wasu Guda 3 A Kudancin Labanon November 2, 2025 Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya November 2, 2025 Shugaban AmurkaTrump ya yi barazanar daukar matakin soji kan Najeriya November 2, 2025 Kamaru: Jagroan ‘Yan Hamayya Ya Yi Kira Da A Tsayar Da Harkoki A Fadin kasar November 1, 2025 MDD Tana Sa Ido Akan Kashe-kashen Da Ake Yi A Zaben Kasar Tanzania November 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci