Shekara 2 Ta Gwamnatin Tinubu: Gwamnonin Arewa Sun ƙaryata Zargin ACF Na Watsi ɗa Yankin
Published: 1st, August 2025 GMT
Ya nuna rashin jin daɗinsa da rabon ayyukan tituna kamar yadda aka samu a cikin wata sanarwa da ma’aikatar ayyuka ta fitar a watan Mayun 2025, wanda a cewarsa, an ware Naira tiriliyan 1.394 wa yankin Kudu-maso-Yamma, yayin da ɗaukacin yankin Arewa-maso-gabas suka samu Naira biliyan 30, sai kuma yankin Arewa-maso-Yamma Naira 105 biliyan.
“Rashin tsaro ya zama babban abin damuwa, ƴan fashi, tada ƙayar baya, da kuma garkuwa da mutane na ci gaba da wanzuwa a sassan Arewa da dama, inda jihohi kaɗan ne kamar Kaduna da Bauchi suka samu kwanciyar hankali,” in ji shi.
Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta fito da manufofin siyasa don kawo ƙarshen rikicin.
ɗalhatu ya kuma soki manufofin gwamnatin tarayya kan harkokin noma, inda ya ce sun jawo ce-ce-ku-ce a harkar noma a cikin gida, sakamakon ƙaruwar shigo da abinci daga ƙasashen waje, lamarin da ya sa aka rufe wasu masana’antun shinkafa a yankin. Ya yi gargaɗin cewa irin waɗannan manufofin suna raunana ƙashin bayan tattalin arzikin yankin.
Ya ƙara da nuna damuwa game da giɓin da ake samu na wutar lantarki a yankin, ya kuma buƙaci shugaba Tinubu ya kafa dokar ta-ɓaci a fannin wutar lantarki. Ya buƙaci a gaggauta kammala wasu muhimman ayyukan makamashi kamar madatsar ruwa ta Mambilla da bututun iskar gas daga Abuja zuwa Kaduna da Kano, waɗanda a cewarsa, suna da matuƙar muhimmanci ga makomar masana’antun Arewacin Nijeriya.
A ɓangaren ilimi kuwa, ɗalhatu ya buga misali da bayanan bankin duniya da ke nuni da cewa kashi 80 cikin 100 na yara miliyan 20 na Nijeriya da aka ƙiyasta ba sa zuwa makaranta ƴan Arewa ne. Ya buƙaci gwamnatin Tinubu da ta sake ƙaddamar da shirin ilimi na bai ɗaya (UBE) tare da himma wajen da mai da hankali kan ilimi kyauta.
Ya kuma yi tir da taɓarɓarewar ababen more rayuwa na kiwon lafiyar al’umma, da sake ɓullar cututtuka, da yawaitar shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin matasan Arewa, inda ya yi kira da a gaggauta ɗaukar matakin na gwamnatin tarayya a fannonin kiwon lafiya na matakin farko, da sarrafa magunguna, da samar da ruwan sha.
Ya bayyana tafiyar hawainiyar da ake yi a kan aikin kamfanin tama da ƙarafa na Ajaokuta a matsayin abin takaici, ya kuma yi gargaɗin a kan dogaro da ƙawancen jama’a da masu zaman kansu (PPP) fiye da kima wajen samar da irin waɗannan kadarorin.
ɗalhatu ya zargi gwamnatin Tinubu da nuna ɓangaranci, son zuciya, da rashin sanin halin da Arewa ke ciki.
Hausawa na Karin magana cewa “Gyara kayanka ba ya zama sauke mu raba,”. Ya ba da shawarar sake farfaɗo da kwamitin tuntuɓar gwamnatin tarayya domin zurfafa tattaunawa.
Sai dai kuma a wani martani da ya mayar, Shugaban ƙungiyar gwamnonin jihohin Arewa (NSGF) kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ce Shugaba Tinubu ya cika alƙawuran da ya ɗaukar wa Arewa kuma yana ci gaba da aiwatar da ajandarsa ta ‘Renewed Hope’
Gwamna Yahaya ya ce tarurrukan da suka haɗa da ƙungiyar SABMF na da matuɗar muhimmanci wajen ƙarfafa dimokuraɗiyya da tabbatar da bin doka da oda, amma ya jaddada cewa shaidun da ke ƙasa na nuna ci gaba mai ma’ana a sassa daban-daban na faɗin yankin.
“Lokacin da Bola Ahmed Tinubu ya yi yaƙin neman zaɓe a faɗin Arewa a shekarar 2023, ya yi alƙawuran da ya dace, a yau muna ganin cikarsu ta hanyar ayyukan da aka kammala da kuma waɗanda ke ci gaba da gudana,” in ji Yahaya, inda ya ƙara da cewa an samu gagarumin ci gaba a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano, layin dogo na Kano-Katsina-Maradi, gyaran matatar mai ta Kaduna, da kuma bunƙasa man fetur na Kolmani.
Yahaya lauded the newly established Ministry of Liɓestock ɗeɓelopment, calling it a major step towards modernising pastoral systems in the region.
Ya kuma bayyana cewa an samu ci gaba a harkokin tsaro a jihohi da dama, inda ya yi nuni da yadda aka kawar da shugabannin ta’addanci da ƴan fashi sama da 300.
Yahaya ya yaba wa sabuwar ma’aikatar kula da kiwon dabbobi da aka kafa, inda ya bayyana hakan a matsayin wani babban mataki na zamanantar da tsarin kiwo a yankin.
A cewarsa, sabbin ababen more rayuwa na tituna da na dogo, inganta kiwon lafiya, ayyukan noma, da kuma ɗaukar matakan da suka dace a fannin ilimi, musamman kan matsalar Almajirai da yaran da ba su zuwa makaranta, na nuni da dabarun da gwamnatin tarayya ta yi domin ɗaukaka yankin.
A nasa jawabin, Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Sanata George Akume, wanda ya wakilci Shugaba Tinubu, ya nanata ƙudurin Shugaban ƙasa na samar da ci gaba mai amfani, yana mai bayyana cewa “ba wani yanki da za a barI baya.
Akume, wanda ya jagoranci tawagar ministoci, shugabannin hukumomi, da mataimakan shugaban ƙasa a wajen taron, ya ce ajandar Renewed Hope an kafa ta ne a kan ginshiƙan daidaito, shiga tsakani, da kuma gaskiya.
Ya zayyana muhimman ayyukan da ake gudanarwa a Arewa da ma faɗin ƙasar nan.
Ya ambaci babbar hanyar Legas zuwa Calabar, babbar titin Sokoto-Badagry, Kano-Maradi da Fatakwal-Maiduguri, da ayyukan gina gidaje da na noma da dama a matsayin shaida na ayyukan gwamnati.
Akan sake fasalin tattalin arziki, Akume ya ce cire tallafin man fetur da kuma haɗewar farashin canji abu ne mai zafi amma an yi su a matakan da suka dace domin daidaita tattalin arzikin ƙasar.
Ya bayyana cewa an riga an bayar da sama da Naira biliyan 53 ta tsarin bayar da lamunin rancen ɗalibai don cin gajiyar ɗaliban manyan makarantu sama da 400,000 a faɗin ƙasar nan.
Akume ya ce Tinubu ya ɗau turbar kai Nijeriya matsayin da ya yi alƙawri, inda ya ƙara da cewa.
“Zan buƙaci ƴan siyasa daga yankin Arewa da su jira har zuwa 2031. Kada ku shiga ƙungiyar da za ta haifar da lalata ci gaba daban-daban da Shugaba Tinubu ya samu. Shugaban ƙasa ya taɓa dukkan sassan ƙasar nan da kowane ɗan ƙasa.”
Ya kuma jinjinawa marigayi Firimiyan Arewacin NIjeriya, Sir Ahmadu Bello, inda ya bayyana shi a matsayin ɗan siyasa mai wakiltar haɗin kai, hangen nesa, da gudanar da mulki na bai ɗaya. Ya kuma yaba da gudunmawar da wasu fitattun shugabannin Arewa suka bayar da suka haɗa da Cif Solomon Lar da Malam Adamu Ciroma.
Waɗanda suka yi wa ƙasa hidima da tsaffin gwamnonin Arewa, ministoci, masu ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA) Malam Nuhu Ribadu, Shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban ƙasa Sanata George Akume, shugabannin gargajiya, shugabannin MɗA na tarayya, shugabannin tsaro, da shugabannin masana’antu ne suka hallarci taron.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: gwamnatin tarayya
এছাড়াও পড়ুন:
Zargin Kisan Kiristoci: ’Yan majalisar Amurka sun yi amfani da bayanai marasa tushe — Gwamnati
Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata zargin da wasu ’yan majalisar dokokin Amurka suka yi cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya.
Ministan Watsa Labarai, Mohammed Idris, ya ce wannan zargi ya ta’allaƙa ne da bayanai marasa tushe, waɗanda ba su san yanayin tsaron Najeriya ba.
“Wasu daga cikin iƙirarin da jami’an Amurka suka yi sun dogara ne da bayanai marasa inganci da tunanin cewa yawancin waɗanda ake kai wa hare-hare Kiristoci ne,” in ji Idris.
“Waɗannan miyagu (’yan ta’adda) ba su ware addini ɗaya ba, suna kai wa Kiristoci da Musulmai hari musamman a Arewacin ƙasar nan.”
Ya bayyana cewa Najeriya ƙasa ce mai yawan addinai da ke zaune lafiya tare, kuma irin waɗannan rahotanni na ƙarya na iya haddasa rikici da tayar da fitina.
“Keɓe waɗannan hare-hare da sunan wani addini abu ne mai hatsarin gaske. Najeriya ƙasa ce wadda mutane suka yadda da juna inda mutane masu addinai daban-daban ke rayuwa cikin lumana,” in ji ministan.
Idris, ya ce gwamnati na ci gaba da inganta fannin tsaro, ciki har da samar da sabbin kayan aiki da haɗin kai mai ƙarfi tsakanin hukumomin tsaro.
Ya bayyana cewa tun daga shekarar 2009, Najeriya ke yaƙi da ta’addanci da ’yan fashin daji, kuma sauye-sauyen da aka yi kwanan nan sauke Hafsoshin Tsaro na nufin inganta tsaro.
Ministan, ya ƙara da cewa gwamnati tana amfani da hanyoyin zaman lafiya ta hanyar noman abinci, samar da ayyukan yi, da shirye-shiryen tallafa wa jama’a don rage talauci da ƙarfafa haɗin kai a tsakanin al’umma.