Gaza: Mutane Da Dama Sun Yi Shahada A Yau Wasu Kuma Sun Jikkata
Published: 1st, August 2025 GMT
Haramtacciyar kasar Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare a zirin Gaza a yau Juma’a, inda ta kai munanan hare-hare kan yankunan fararen hula da sansanonin ‘yan gudun hijira.
Wadannan hare-haren sun yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da kuma jikkatar wasu a fadin yankin, lamarin da ke kara zurfafa damuwar da ake da ita game da mawuyacin da al’ummar yankin suke ciki.
Kamfanin Nasser Medical Complex ya bayar da rahoton a wannan Juma’a cewa, wani harin da jiragen saman Isra’ila suka kai kan tantunan da mutane suke fakewa a yankin Al-Mawasi da ke yammacin Khan Younis, ya kashe mutane hudu tare da jikkata wasu da dama.
A wani harin na daban a kusa da Morag a kudancin birnin Gaza, an kashe mutane biyu tare da jikkata wasu sama da 70 da ke neman agaji.
A wani harin da aka kai a yankin Ard al-Fara da ke kudancin Khan Younis, an kashe fararen hula uku da suka hada da yaro daya da mace daya a lokacin da aka kai hari kan tantunan ‘yan gudun hijira.
A yankin Deir al-Balah da ke tsakiyar Gaza kuwa Isra’ila ta kashe mutane hudu tare da jikkata wasu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Haaretz: Sojojin Isra’ila 7 ne suka kashe kansu a watan Yuli August 1, 2025 Kungiyar AU Ta Yi Watsi Da Kafa Gwamnatin Adawa Da Kungiyar RSF Ta Yi A Sudan August 1, 2025 Shugaban Kasar Iran Zai Ziyarci Pakistan A Gobe Asabar August 1, 2025 Habasha Ta Kaddamar Da Shirin Shuka Bishiyoyi Miliyan 700 A Rana Daya August 1, 2025 Sayyid Abdulmalik Husi: Taimakon Da Ake Jefawa Gaza Ta Sama Yaudara Ce August 1, 2025 Amurka Ta Kakabawa Jami’an Gwamnatin Falasdinawa Takunkuman Hana Shiga Amurka July 31, 2025 Ministan Harkokin Wajen Siriya Yana Rasha Don Bude Sabon Shafi Tsakaninsu July 31, 2025 Kananan Yan Wasan Dabben Gargajiya Na Iran Sun Zama Zakara A Gasar Wannan Shekara July 31, 2025 Canada Zata Amince Da Samuwar Kasar Falasdinu A Taron MDD July 31, 2025 Shugaban Kasar Lebanon Aun Ya Ce Mun Aike Wa Amurka Sakwanni Akan Dakatar Da Hare-haren HKI July 31, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Samia Suluhu Hassan ta lashe zaben shugaban kasa a Tanzaniya
Hukumar zaben kasar Tanzaniya ta bayyana shugabar kasa mai ci Samia Suluhu Hassan a matsayin wadda ta lashe zaben shugaban kasar.
Shugaban hukumar zaben ya ce Shugaba Samia ta yi nasara a zaben da kashi 98% na jimillar kuri’un da aka kada.
Bayanai sun ce manyan ‘yan takarar adawa ba su shiga ba, wasu kuma an tsare su ko kuma an hana su tsayawa takara, wanda hakan ya haifar da tashin hankali.
Jam’iyyar adawa ta kasar ta ce daruruwan mutane ne suka mutu sanadiyyar zanga-zangar da aka kwashe kwanaki ana yi tun bayan zaben na ranar Laraba.
Wani mai magana da yawun jam’iyyar adawa ta Chadema ya shaida wa AFP cewa kimanin mutane 700 ne suka mutu, a alkalumman da aka tattara daga asibitoci.
Gwamnatin Shugaba Samia ta musanta duk wani “yin amfani da karfi fiye da kima,” yayin da Ministan Harkokin Waje Mahmoud Thabit Kombo ya shaida wa Al Jazeera cewa babu “bayani” kan adadin wadanda suka mutu.
Hukumomin sun katse hanyar intanet, sun sanya dokar hana fita, kuma sun takaita ‘yan jarida, wanda hakan ya takaita samun bayanai.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Najeriya ta musanta ikirarin Trump, na cewa Kristoci na fuskantar babbar barazana a kasar November 1, 2025 Majalisar Dinkin Duniya ta damu da hare-haren Amurka a Caribbean da Pacific November 1, 2025 Israila Ta Kai Hari Kan Ofishin kungiyar UNICEF Dake Gaza A November 1, 2025 Amurka Na Shirin Kai Hari Kan Kasar Venzuwela A Kowanne Lokaci November 1, 2025 Iran Ta Sanya Da Ranar 30 Ga Watan Nuwamba A Matsayin Ranar Kasa Ta Tsibirai 3 October 31, 2025 Isra’ila Na Ci Gaba Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza October 31, 2025 An Tube Yarima Mai Jiran Gado Na Birtaniya Bayan Da Aka Tabbatar Da Laifinsa October 31, 2025 Kasashen Pakistan Da Afghanistan Sun Tsawaita Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta October 31, 2025 M D Duniya Tayi Gargadi Game Da Gwajin Nukiliya Da Amurka Ta Sanar Za ta yi October 31, 2025 Sudan Ta Yi Kira Ga Kwamitin Tsaro Da Ya Ayyana RSF A Matsayin Kungiyar ‘Yan Ta’adda October 31, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci