Sabon Kwamishinan Na Kwara Ya Sha Alwashin Dakile Laifuka
Published: 11th, April 2025 GMT
Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, ta ce an shirya shirye-shirye domin karfafa tsaro a jihar da kuma tabbatar da mazauna yankin suna rayuwa cikin yanayi na zaman lafiya da tsaro.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Adekimi Ojo ne ya bayyana haka da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar ‘yan sanda da ke Ilorin.
Ya ce gwamnatinsa ba za ta amince da rashin da’a, take hakkin bil’adama, yana mai cewa ma’aikatan da suka yi kuskure za su fuskanci tsauraran mataki.
Ojo ya yi alkawarin samarwa jihar tsaro ta hanyar magance miyagun laifuffuka da kuma kiyaye da’a da kwarewa a cikin rundunar ‘yan sanda.
Ya bayyana cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yakar laifuka da aikata laifuka.
Kwamishinan ‘yan sandan ya jaddada cewa aikin ‘yan sanda mai inganci yana bukatar sanya hannun masu ruwa da tsaki da suka hada da shugabannin gargajiya da na addini da kungiyoyin farar hula da kuma kafafen yada labarai.
COV/ALI MUHAMMAD RABIU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Jihar Kebbi Ta Kammala Shirye-shiryen Aikin Hajjin 2025
Hukumar Jin Daɗin Alhazai a Jihar Kebbi ta bayyana cewa ta kammala dukkan shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin bana a Ƙasa Mai Tsarki.
Amirul Hajji na jihar na shekarar 2025 kuma Sarkin Argungu, Alhaji Samaila Muhammad Mera, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a lokacin taron farko da aka gudanar a hedkwatar hukumar da ke Birnin Kebbi.
Ya kuma yi alkawarin tabbatar da jin daɗin mahajjatan jihar yayin da suke a ƙasa mai tsarki.
Amirul Hajjin ya bayyana cewa jimillar mahajjata 3,800 daga jihar ne suka biya kuɗin kujerunsu gaba ɗaya domin aikin hajjin bana, kuma jigilar mahajjatan za ta fara ne ranar 9 ga watan Mayu, inda ya ce da yardar Allah za a ci gaba da jigilar ba tare wani tsaiko ba har sai an kammala.
Ya kuma bayyana cewa, a wannan shekarar, za a yi wa mahajjata canjin kuɗin guzirinsu na BTA zuwa kudin Saudiyya wato riyal kai tsaye, da nufin dakile ayyukan damfara da kuma kare mahajjata daga asarar kuɗi yayin musayar kuɗaɗe a nan gida da kuma Saudiyya.
Alhaji Muhammadu Mera ya shawarci mambobin tawagar gwamnati da jami’an hukumar jin daɗin mahajjata da su gudanar da ayyukansu bisa tsoron Allah, tare da kare haƙƙoƙin mahajjata, daidai da manufar Gwamna Nasir Idris na gudanar da sahihin aikin Hajji mafi kyau.
Shugaban Hukumar, Alhaji Faruk Musa Yaro, ya yi alkawarin bayar da cikakken haɗin kakaga tawagar gwamnati domin tabbatar da nasarar aikin Hajji da ba a taɓa irin sa ba a tarihin jihar.
Ya ce an riga an samu masauki da sauran abubuwan buƙata ciki har da sufuri da abinci a ƙasa mai tsarki, sannan kuma kamfanin jirgin samsada ya yi jigilar Alhazan jihar a shekarar da ta gabata, wato Flynas, a bana ma shi ne zau yi jigilar mahajjatan zuwa kasa mai tsarki.
Haka kuma, an an fara yi wa Amirul Hajj da sauran mambobin tawagar gwamnati allurar rigakafi yayin kaddamar da shirin rigakafin mahajjatan.
Daga Abdullahi Tukur