Iran ta yi watsi da zargin gwamnatocin turai na yunkurin kashe wasu mutane a kasashensu
Published: 1st, August 2025 GMT
Iran ta yi watsi da zarge-zargen marasa tushe balantana makama da kasashen yammacin duniya ke yi a kanta, kan cewa tana yunkurin kashe wasu mutane a cikin kasashensu.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya yi Allah wadai da ikirarin da ya kira na kin jinin Iran da Amurka da Canada da wasu kasashen Turai goma sha biyu suka yi a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar a wannan Alhamis.
Ya ce wannan batu a fili wani yunkuri ne na karkatar da hankulan jama’a daga batun da ya fi daukar hankali a wannan lokaci, wato kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Palastinu da ta mamaye.
Ya kara da cewa, “Amurka, Faransa, da sauran kasashen da suka sanya hannu kan wannan sanarwa ta kin jinin Iran, tilas ne su kansu su dauki alhakin ayyukan da suka saba wa dokokin kasa da kasa, yayin da suke goyon baya da daukar nauyin ‘yan ta’adda da kungiyoyi masu tayar da hankali, domin yin amfani da hakan ajen cimma manufofinsu na siyasa.
Baghaei ya tabo batun hare-haren wuce gona da iri da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran a watan Yuni da kuma kisan kiyashin da Isra’ila ke ci gaba da yi a zirin Gaza, da kuma yin shiru da kasashen yammacin duniya 14 da suka rattaba hannu kan sanarwar suke yi a kan manyan laifukan yaki da Isra’ila take aikatawa a kan idanun dukkanin al’ummomin duniya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Mali da Rasha sun tattauna kan hadin gwiwar makamashi August 1, 2025 Afirka ta Kudu na shirin daukar matakan kauce wa tasirin harajin Amurka August 1, 2025 Haaretz: Sojojin Isra’ila 7 ne suka kashe kansu a watan Yuli August 1, 2025 Gaza: Mutane Da Dama Sun Yi Shahada A Yau Wasu Kuma Sun Jikkata August 1, 2025 Kungiyar AU Ta Yi Watsi Da Kafa Gwamnatin Adawa Da Kungiyar RSF Ta Yi A Sudan August 1, 2025 Shugaban Kasar Iran Zai Ziyarci Pakistan A Gobe Asabar August 1, 2025 Habasha Ta Kaddamar Da Shirin Shuka Bishiyoyi Miliyan 700 A Rana Daya August 1, 2025 Sayyid Abdulmalik Husi: Taimakon Da Ake Jefawa Gaza Ta Sama Yaudara Ce August 1, 2025 Amurka Ta Kakabawa Jami’an Gwamnatin Falasdinawa Takunkuman Hana Shiga Amurka July 31, 2025 Ministan Harkokin Wajen Siriya Yana Rasha Don Bude Sabon Shafi Tsakaninsu July 31, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: da Isra ila
এছাড়াও পড়ুন:
Rabin Sojojin Isra’ila da suka ji rauni a yakin Gaza na fama da ciwon damuwa
Ma’aikatar tsaron Isra’ila ta ce fiye da sojojin kasar 20,000 ne suka ji rauni tun farkon yakin da aka fara a Gaza a watan Oktoba 2023, inda fiye da rabinsu ke fama da matsalolin lafiyar kwakwalwa, ciki har da ciwon damuwa.
A cewar sashen bayar da shawarwari na ma’aikatar, kusan kashi 56 cikin 100 na wadanda suka ji rauni sun kamu da wasu matsalolin lafiyar kwakwalwa, wanda ke nuna irin tasirin matsalar kwakwalwa da wannan rikici ke haifarwa.
Ma’aikatar ta kara da cewa kusan kashi 45 cikin 100 na wadanda suka ji rauni suna fama da raunuka a jiki, yayin da kashi 20 cikin 100 na sojojin ke fama da matsalolin kwakwalwa da na jiki a lokaci guda.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sudan ta soki takunkuman da Amurka ta kakaba mata September 15, 2025 Dakarun Sojin Yamen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Saman Ramon Na Isra’ila. September 14, 2025 Isra’ila Za ta Gamu Da Mummunar Martani Idan Tayi Gigin Afkawa Iran September 14, 2025 Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Larabawa Da Na Musulmi Sun Fara Taro A Qatar. September 14, 2025 Gwamnatin Najeriya Ta Sanar Da Sabon Sharadi Na Bude Asusun Banki September 14, 2025 An Zabi Issa Tchiroma A Matsayin Dan Takara Daya Tilo A Kamaru September 14, 2025 Kasar Iran Ta Yi Fatali Da Zarge-Zargen Da Kungiyar G7 Da Kawayenta Suka Yi Kanta September 14, 2025 Iran Ta Bayyana Shirinta Na Halartar Taron Shekara-Shekara Na Hukumar Makamashin Nukiliya September 14, 2025 Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Bayyana Rashin Halarta Tawagarta A Kada Kuri’a Kan Batun Falasdinu September 14, 2025 Tsananin Masifar Da Falasdinawa Ke Ciki A Gaza Saboda Hare-Haren Gwamnatin Mamayar Isra’ila September 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci