Asusun Tallafawa Dalibai Da Rancen Kudi Ya Koka Akan Ayukkan Wasu Jami’o’in Nijeriya
Published: 11th, April 2025 GMT
Asusun ba da lamuni na ilimi na Najeriya ya yi barazanar daukar matakin shari’a a kan cibiyoyin da ke boye bayanai kan yadda ake biyan dalibai rancen kudi yayin da suke neman biyan kudaden makarantun daga hannun daliban.
Sanarwar da Manajin Darakta na NELFUND, Mista Akintunde Sawyerr ya fitar ta bayyana cewa, sakamakon binciken da aka gudanar a baya-bayan nan ya nuna cewa wasu cibiyoyi bayan karbar lamunin dalibai kai tsaye a cikin asusunsu, sun kasa sanar da daliban da abin ya shafa ko kuma nuna kudaden da aka biya a cikin takardun kudin makarantarsu, wanda hakan ya haifar da rudani da bai kamata ba.
Mista Sawyerr wanda ya bayyana lamarin a matsayin rashin da’a, ya kuma gargade su da su daina ko kuma su fuskanci fushin doka.
“Wannan matakin na hana mahimman bayanan kuɗi daga ɗalibai ba rashin da’a ba ne kawai amma cin zarafi ne kai tsaye ga ƙa’idodin da aka kafa NELFUND a kai. “Ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen daukar matakin shari’a kan duk wata cibiya da aka samu da aikata irin wadannan ayyukan yaudara.”
Ya shawarci dukkanin cibiyoyi da su tabbatar da gaskiya tare da yin aiki tare da Asusun don tabbatar da isar da ayyukan sa yadda ya kamata.
Mista Sawyerr ya jaddada cewa manufar NELFUND ita ce fadada hanyoyin samun ilimi mai zurfi ta hanyar sauke nauyin kudi a kan daliban Najeriya da iyalansu, daidai da hangen nesa na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Asusun yana tabbatar wa ɗalibai da jama’a jajircewar sa na yin riko da gaskiya, yin adalci, da samun nasarar aiwatar da shirin rancen ɗalibai a faɗin ƙasar.
HAKURI OLUMATI
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
An Kama Tsohon Firaministan Mali Bisa Zargin Karkatar Da Dukiyar Gwamnati
Lauyan Maïga, Cheick Oumar Konaré, ya bayyana cewa kamun bai dace ba saboda Maïga ba shi da niyyar guduwa ko lalata shaidu, yana kuma zargin cewa wannan wani mataki ne na siyasa saboda tsohon Firaministan ya daɗe yana sukar gwamnatin soja tun bayan tsawaita mulkinsu ba tare da gudanar da zaɓe ba.
Maïga, ya hau kujerar Firaminista a watan Yulin 2021 bayan gwamnatin sojoji ta yi juyin mulki, inda ya goyi bayan dakatar da shirye-shiryen zaɓe don bai wa gwamnatin soja ƙarin lokaci.
Sai dai daga baya ya fara sukar wasu matakan gwamnati, musamman bayan an dakatar da shi daga kujerarsa a watan Nuwamban 2024.
Tun bayan juyin mulkin 2020 da na 2021, Mali ta kasance ƙarƙashin mulkin soja, kuma ana zargin gwamnati da take haƙƙin ɗan adam da murƙushe ‘yan adawa.
A kwanakin baya ma an kama wasu sojoji bisa zargin kitsa juyin mulki.
Kamun Maïga ya janyo ce-ce-ku-ce a ƙasar, inda wasu ke ganin matakin a matsayin wani yunƙuri na yaƙi da cin hanci, yayin da wasu kuma ke kallonsa a matsayin dabarar murjushe ‘yan adawa, musamman a wannan lokaci da ake buƙatar haɗin kai don dawo da tsarin dimokuraɗiyya a Mali.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp