Aminiya:
2025-11-03@01:53:16 GMT

Ɗaliban da aka sace a Binuwai sun kuɓuta 

Published: 1st, August 2025 GMT

Jami’an tsaro sun tabbatar da kuɓutar wasu ɗalibai shida na Makarantar Horon Ilimin Shari’a ta Najeriya da aka sace.

Rundunar ’yan sandan Jihar Binuwai ce ta bayyana hakan a ranar Juma’a.

’Yan Najeriya miliyan 34 na cikin barazanar yunwa Mun ci ribar Naira biliyan 414 a cikin wata 6 a Najeriya – Kamfanin MTN

Kakakin ’yan sandan, Udeme Edet, ya ce ɗaliban sun taso ne daga Jihar Anambra, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa makarantar horon ilimin shari’a da ke Yola, a Jihar Adamawa.

’Yan bindiga ne suka tare su a iyakar Binuwai da Taraba.

“An ceto ɗalibai shida da aka sace a ranar 26 ga watan Yuli, 2025, yayin da suke kan hanyarsu daga Anambra zuwa Adamawa.

“An sako su lafiya ƙalau kuma sun koma wajen iyalansu a safiyar yau, 1 ga watan Agusta, 2025,” in ji sanarwar.

Maharan sun nemi Naira miliyan 120 a matsayin kuɗin fansa, kuma sun yi barazanar kashe ɗaliban idan ba a biya buƙatarsu ba.

Matsalar na ci gaba da ta’azzara a Jihar Binuwai.

A bara ma, an sace ɗalibai 20 yayin da suke kan hanyar zuwa Jami’ar Jos a Jihar Filato.

Maharan sun sako su bayan shafe makwanni a hannunsu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda Binuwai Ɗalibai Garkuwa

এছাড়াও পড়ুন:

Kotu ta tsige dan majalisar da ya sauya sheka zuwa APC

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tsige dan majalisar wakilai, Abubakar Gummi daga kujerarsa saboda sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Gummi yana wakiltar mazabar Gummi/Bukkuyum ta Jihar Zamfara a majalisar wakilai.

An raba wa iyalan jami’an ’yan sandan da suka rasu a bakin aiki a Borno N63.4m An sake kama shi a cikin ’yan fashi kwana 5 da fitowa daga kurkuku

Mai shari’a Obiora Egwuatu ne, ya yanke hukuncin, inda ya umarci kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, da ya daina amincewa da Gummi a matsayin dan majalisar da ke wakiltar mazabar Gummi/Bukkuyum.

Haka kuma ya umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta shirya sabon zabe cikin kwanaki 30 domin cike gurbin kujerar dan majalisar.

Jam’iyyar PDP tare da shugaban ta na jihar Zamfara, Jamilu Jibomagayaki, ne suka shigar da karar dan majalisar.

Sun ce bai dace Gummi ya ci gaba da zama a kujerar ba bayan barin jam’iyyar da ta tsayar da shi takara.

Gummi, ta bakin lauyansa ya ce ya fice daga PDP ne saboda rikicin cikin gida da jam’iyyar ke fama da shi a matakin kasa da kuma a mazabarsa.

Amma kotu ta yi watsi da wannan hujjar, inda ta bayyana cewa babu takaddama da za ta ba shi damar ya sauya sheka.

A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Egwuatu ya ce ’yan siyasa dole su mutunta zabin jama’ar da suka kada musu kuri’a a karkashin jam’iyyar da ta tsayar da su takara.

Ya ce doka ba ta yadda da dan siyasa ya bar jam’iyyar da ta taimaka masa wajen lashe zabe sannan ya koma wata jam’iyya ba tare da ajiye mukaminsa ba.

Ya kara da cewa kuri’un da aka kada don dan takarar na jam’iyya ne, ba nasa ne na kashin kansa ba.

“Idan mutum yana son sauya sheka, ka da ya dauki amanar jama’ar da ta zabe shi ya tafi da ita,”  in ji alkalin.

Kotu ta kuma umarci Gummi da ya daina karbar albashi da wasu hakkoki a matsayin dan majalisa, tare da mayar da duk kudaden da ya karba daga ranar 30 ga watan Oktoba, 2024, zuwa ranar da aka yanke hukuncin.

Haka kuma, ya gabatar da hujjar mayar da kudaden ga kotu cikin kwanaki 30.

Mai shari’a Egwuatu ya kuma ci Gummi tarar Naira N500,000, domin biyan PDP kudaden da ta kashe wajen shigar da kara.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Al’ummar Kauru Sun Koka Game Da Karuwar Hare-hare Da Ke Barazana Ga Gonaki Da Rayuka
  • Hamas ta musanta zargin Amurka na cewa tana sace kayan agaji a Gaza
  • An Kashe Mutum 3 Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Kan Iyakokin Kano
  • Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci
  • Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar
  • ’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi
  • Gwamna Uba Sani Ya Gabatar Da Kudirorin Raya Jihar Kaduna A Taron Ƙoli Na Biranen Asiya A Dubai 
  • Kotu ta tsige dan majalisar da ya sauya sheka zuwa APC
  • Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda