Iran Ta Ce Batun Neman Dakatar Da Tace Uranium Zai Rusa Duk Wata Jarjejeniya Da Ake Son Cimmawa
Published: 1st, August 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Matukar dai Trump ya bukaci dakatar da inganta sinadarin Uranium gaba daya a Iran, to ba za a cimma wata yarjejeniya ba
Ministan harkokin wajen Iran Sayyid Abbas Araqchi ya jaddada a wata hira da jaridar Financial Times cewa: Iran na neman a biya ta diyya kan irin hasarar da ta yi a harin wuce gona da irin kwanaki 12 na ta’addanci kan kasarta.
Araqchi ya yi nuni da bukatar Amurka ta bayyana dalilin da ya sa ta kai farmaki kan Iran a tsakiyar shawarwari tare da bayar da tabbacin cewa ba za a sake daukar irin wannan mataki ba.
Araqchi ya kara da cewa, warware rikicin makamashin nukiliya na bukatar nemo hanyar da za a cimma nasara, yana mai jaddada cewa hanyar yin shawarwari tana da kankanta amma mai yiwuwa ce.
Ya jaddada mahimmancin Amurka na daukar matakan tabbatar da gaskiya na gaske, gami da biyan diyya na kudi da kuma ba da tabbacin rashin cin zarafi a yayin tattaunawar.
Ministan harkokin wajen na Iran ya yi la’akari da cewa wuce gona da iri da aka yi a baya-bayan nan ya tabbatar da cewa babu wata hanyar soji kan shirin makamashin nukiliyar kasar Iran, kuma warware takaddamar da ake yi ta hanyar tattaunawa ita ce zabin da za a iya cimma nasara, yana mai jaddada matsayin Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan shirinta na makamashin nukiliya na zaman lafiya da kuma girmama fatawar Jagoran juyin juya halin Musulunci dangane da haramcin kera makaman nukiliya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Yi Watsi Da Duk Wani Zarge-Zargen Neman Bata Mata Suna August 1, 2025 Limamin Sallar Juma’a Ya Ce; Iran Zata Mayar Da Isra’ila Kufai Idan Ta Sake Kai Hari Kan Kasarta August 1, 2025 Kasar Slovenia Da Haramta Tura Makamai Zuwa Haramtacciyar Kasar Isra’ila August 1, 2025 Kasar Spain Ta Bayyana Abin Da Ke Faruwa A Gaza A Matsayin Abin Kunya Ga Bil’Adama August 1, 2025 Iran ta yi watsi da zargin gwamnatocin turai na yunkurin kashe wasu mutane a kasashensu August 1, 2025 Mali da Rasha sun tattauna kan hadin gwiwar makamashi August 1, 2025 Afirka ta Kudu na shirin daukar matakan kauce wa tasirin harajin Amurka August 1, 2025 Haaretz: Sojojin Isra’ila 7 ne suka kashe kansu a watan Yuli August 1, 2025 Gaza: Mutane Da Dama Sun Yi Shahada A Yau Wasu Kuma Sun Jikkata August 1, 2025 Kungiyar AU Ta Yi Watsi Da Kafa Gwamnatin Adawa Da Kungiyar RSF Ta Yi A Sudan August 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Afirka ta Kudu na shirin daukar matakan kauce wa tasirin harajin Amurka
Ministan kasuwanci na Afirka ta Kudu Parks Tau ya fada jiya Alhamis cewa kasarsa na shirin yin shawarwarin kasuwanci da nufin kaucewa harajin kashi 30% na Amurka a kan kasarsa, wanda zai fara aiki daga wannan Juma’a.
A farkon watan Mayu ne Afirka ta Kudu ta gabatar da wani shirin yarjejeniya ta kasuwanci ga gwamnatin Trump, amma kuma gwamnatin Amurka bat a bayar da amsa kan hakan ba.
kuma ta sake duba ta a watan Yuni, ba tare da bayar da amsa ba.
Ya kara da cewa, jami’an Afirka ta Kudu sun yi magana da jami’an Amurka a yammacin Laraba a ofishin jakadancin Washington da ke Pretoria da kuma wakilin kasuwanci na Amurka, amma har yanzu akwai rashin tabbas game da abin da zai faru yayin da wa’adin haraji yake karewa.”
Ya kara da cewa, “Sun ce za su kara mana kwarin gwiwar sake mika kudirinmu, mai yiyuwa ya karfafa gwamnatin Amurka ta sake yin nazari kan batun haraji.”
Amurka ita ce kasa ta biyu wajen cinikayya da kasar Afirka ta Kudu bayan kasar Sin. Afirka ta Kudu na fitar da motoci, wasu kayayyaki da aka kerawa, ‘ya’yan itatuwa, da inabi zuwa Amurka.
Dangantaka tsakanin kasashen biyu ta yi tsami ne kan manufofin karfafa tattalin arziki ga bakaken fata ‘yan Afirka ta Kudu, da nufin magance matsalar rashin daidaito da aka yi a shekaru aru-aru, da kuma batun karar da Afirka ta kudu ta shigar kan kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Haaretz: Sojojin Isra’ila 7 ne suka kashe kansu a watan Yuli August 1, 2025 Gaza: Mutane Da Dama Sun Yi Shahada A Yau Wasu Kuma Sun Jikkata August 1, 2025 Kungiyar AU Ta Yi Watsi Da Kafa Gwamnatin Adawa Da Kungiyar RSF Ta Yi A Sudan August 1, 2025 Shugaban Kasar Iran Zai Ziyarci Pakistan A Gobe Asabar August 1, 2025 Habasha Ta Kaddamar Da Shirin Shuka Bishiyoyi Miliyan 700 A Rana Daya August 1, 2025 Sayyid Abdulmalik Husi: Taimakon Da Ake Jefawa Gaza Ta Sama Yaudara Ce August 1, 2025 Amurka Ta Kakabawa Jami’an Gwamnatin Falasdinawa Takunkuman Hana Shiga Amurka July 31, 2025 Ministan Harkokin Wajen Siriya Yana Rasha Don Bude Sabon Shafi Tsakaninsu July 31, 2025 Kananan Yan Wasan Dabben Gargajiya Na Iran Sun Zama Zakara A Gasar Wannan Shekara July 31, 2025 Canada Zata Amince Da Samuwar Kasar Falasdinu A Taron MDD July 31, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci