HausaTv:
2025-11-02@05:40:54 GMT

Mali da Rasha sun tattauna kan hadin gwiwar makamashi

Published: 1st, August 2025 GMT

Wakilan kasashen Mali da Rasha sun gudanar da taron farko na kwamitin hadin gwiwa na gwamnatocin kasashen biyu, karkashin jagorancin ministan tattalin arziki da kudi na kasar Mali Husseini Sanou, da ministan makamashi na kasar Rasha Sergey Tsivlev, inda suka tattauna kan “hadin gwiwa a fannin makamashi, musamman wajen yin amfani da makamashin nukiliya domin ayyukn farar hula.

Taron ya samu halartar wakilan “manyan kamfanonin makamashi na Rasha da ma’aikatun gwamnatin tarayya,” kamar yadda ya zo a cikin wata sanarwa da ma’aikatar makamashi ta Rasha ta fitar a shafinta na intanet, a cewar kafar yada labarai ta African Readings.

Bangarorin biyu sun tattauna kan fagagen da suka yi alkawarin yin aikin hadin gwiwa a fannin hakar albarkatun kasa, binciken sararin samaniya, tsaro ta yanar gizo, da kuma aikin gona,” baya ga hanyoyin da za a bi wajen samar da kayayyakin masarufi a kasar Mali da kasashen Sahel, wanda ke da muhimmanci wajen tabbatar da dorewar tsarin ayyukan hadin gwiwa,” a cewar sanarwar ma’aikatar makamashi ta kasar Rasha.

A ziyarar da ya kai birnin Moscow a watan Yunin da ya gabata, shugaban majalisar rikon kwarya a kasar Mali, Janar Assimi Goita, ya amince tare da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin kan kafa kwamitin hadin gwiwa na gwamnatocin Mali da Rasha.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Afirka ta Kudu na shirin daukar matakan kauce wa tasirin harajin Amurka August 1, 2025 Haaretz: Sojojin Isra’ila 7 ne suka kashe kansu a watan Yuli August 1, 2025 Gaza: Mutane Da Dama Sun Yi Shahada A Yau Wasu Kuma Sun Jikkata August 1, 2025 Kungiyar AU Ta Yi Watsi Da Kafa Gwamnatin Adawa Da Kungiyar RSF Ta Yi A Sudan August 1, 2025 Shugaban Kasar Iran Zai Ziyarci Pakistan A Gobe Asabar August 1, 2025 Habasha Ta Kaddamar Da Shirin Shuka Bishiyoyi Miliyan 700 A Rana Daya August 1, 2025 Sayyid Abdulmalik Husi: Taimakon Da Ake Jefawa Gaza Ta Sama Yaudara Ce August 1, 2025 Amurka Ta Kakabawa Jami’an Gwamnatin Falasdinawa Takunkuman Hana Shiga Amurka July 31, 2025 Ministan Harkokin Wajen Siriya Yana Rasha Don Bude Sabon Shafi Tsakaninsu July 31, 2025 Kananan Yan Wasan Dabben Gargajiya Na Iran Sun Zama Zakara A Gasar Wannan Shekara July 31, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: hadin gwiwa

এছাড়াও পড়ুন:

Samia Suluhu Hassan ta lashe zaben shugaban kasa a Tanzaniya

Hukumar zaben kasar Tanzaniya ta bayyana shugabar kasa mai ci Samia Suluhu Hassan a matsayin wadda ta lashe zaben shugaban kasar.

Shugaban hukumar zaben ya ce Shugaba Samia ta yi nasara a zaben da kashi 98% na jimillar kuri’un da aka kada.

Bayanai sun ce manyan ‘yan takarar adawa ba su shiga ba, wasu kuma an tsare su ko kuma an hana su tsayawa takara, wanda hakan ya haifar da tashin hankali.

Jam’iyyar adawa ta kasar ta ce daruruwan mutane ne suka mutu sanadiyyar zanga-zangar da aka kwashe kwanaki ana yi tun bayan zaben na ranar Laraba.

Wani mai magana da yawun jam’iyyar adawa ta Chadema ya shaida wa AFP cewa kimanin mutane 700 ne suka mutu, a alkalumman da aka tattara daga asibitoci.

Gwamnatin Shugaba Samia ta musanta duk wani “yin amfani da karfi fiye da kima,” yayin da Ministan Harkokin Waje Mahmoud Thabit Kombo ya shaida wa Al Jazeera cewa babu “bayani” kan adadin wadanda suka mutu.

Hukumomin sun katse hanyar intanet, sun sanya dokar hana fita, kuma sun takaita ‘yan jarida, wanda hakan ya takaita samun bayanai.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Najeriya ta musanta ikirarin Trump, na cewa Kristoci na fuskantar babbar barazana a kasar November 1, 2025 Majalisar Dinkin Duniya ta damu da hare-haren Amurka a Caribbean da Pacific November 1, 2025 Israila Ta Kai Hari  Kan Ofishin kungiyar UNICEF Dake Gaza A November 1, 2025 Amurka Na Shirin Kai Hari Kan Kasar Venzuwela A Kowanne Lokaci November 1, 2025 Iran Ta Sanya  Da Ranar 30 Ga Watan Nuwamba A Matsayin Ranar Kasa Ta Tsibirai 3 October 31, 2025 Isra’ila Na Ci Gaba Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza October 31, 2025 An Tube Yarima Mai Jiran Gado Na Birtaniya Bayan Da Aka Tabbatar Da Laifinsa October 31, 2025 Kasashen Pakistan Da Afghanistan Sun Tsawaita Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta October 31, 2025 M D Duniya Tayi Gargadi Game Da Gwajin Nukiliya Da Amurka Ta Sanar Za ta yi October 31, 2025 Sudan Ta Yi Kira Ga Kwamitin Tsaro Da Ya Ayyana RSF A Matsayin Kungiyar ‘Yan Ta’adda October 31, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kamaru: Jagroan ‘Yan Hamayya Ya Yi Kira Da A Tsayar Da Harkoki A Fadin kasar
  • MDD Tana Sa Ido Akan Kashe-kashen Da Ake Yi A Zaben Kasar Tanzania
  • Shugaban Kasar Najeriya Ya Mayar Da Martani Ga Takwaransa Na Amurka Akan Rikicin Addini
  • Iran ta damu da halin da ake ciki a yankin El Fasher na Sudan
  • Samia Suluhu Hassan ta lashe zaben shugaban kasa a Tanzaniya
  • Israila Ta Kai Hari  Kan Ofishin kungiyar UNICEF Dake Gaza A
  • Amurka Na Shirin Kai Hari Kan Kasar Venzuwela A Kowanne Lokaci Daga Yanzu
  • Masar da Eritrea Sun Tattauna Bukatar Tallafawa Kasar Sudan
  • Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Kutsen Na Isra’ila A Kudancin Kasar
  • Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Duk Wani Kutse Na Isra’ila A Kudancin Kasar