Amurka Ta Kai Hare-hare A Yankunan Kasa Yemen
Published: 11th, April 2025 GMT
Rahotanni daga kasar Yemen sun ambaci cewa jiragen yakin Amurka sun kai jerin hare-hare a yankuna mabanbanta na kasar Yemen da su ka hada da birnin San’aa.
Tashar talabijin din al-masirah ta ambaci cewa; jiragen yakin Amurka sun kai hare-haran ne har sau 7, biyu a cikin yankin Hamadan, da Banu Hashish sai kuma babban birnin kasar Sanaa.
Kawo ya zuwa babu cikakken bayani akan adadin wadanda su ka jikkata ko shahada sanadiyyar wannan harin.
Amurkan dai tana kai wa Yemen hare-hare ne saboda taimakawa HKI a yaki, da kokarin hana dakarun Ansarullah ci gaba da kai hare-hare akan manufofin HKI.
A daren jiya Alhamsi shugaban kungiyar Ansarullah Sayyid Abdulmalik al-Husi ya bayyana cewa; hare-haren da Amurka take kai musu ba su yi wa makaman da suke da su illa ba,kuma akasin haka suna kara musu azama ne.
Sojojin Yemen suna kai hare-hare a HKI saboda yin matsin lamba akan HKI ta dakatar da hare-haren da take kai wa Gaza, sannan kuma da mayar da martani akan jiragen dakon jiragen yaki na Amurka a tekun “Red Sea’ bayan da su ka fara kai wa Yemen din hari.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: hare hare a
এছাড়াও পড়ুন:
Yara masara zuwa makaranta barazana ne ga kasa — Shettima
Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ya ce yawan yara marasa zuwa makaranta a Najeriya a barazana ce da ke buƙatar haɗin gwiwa daga dukkan matakan gwamnati da masu ruwa da tsaki.
Shettima ya yi wannan bayani a taron Zauren Ilimin Najeriya na 2025 da aka gudanar a Abuja, wanda Kungiyar Gwamnonin Najeriya tare da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya da abokan hulɗa suka shirya.
Ya ce matsalar ilimi ba za ta iya warwarewa da ƙoƙarin gwamnati kaɗai ba, yana mai jaddada cewa: “Yawan yaran da ba sa zuwa makaranta bukatar gaggawa ce ta ƙasa da ke buƙatar haɗin kai tsakanin Gwamnatin Tarayya, jihohi, kananan hukumomi da al’umma.”
Shettima, wanda mai ba shi shawara na musamman Aliyu Modibbo Umar ya wakilta, ya ce dole malamai su samu horo mai kyau, kulawa da kuma kima a matsayinsu na ƙwararru domin a samu ingantaccen ilimi.
An dakatar da Shugaban Karamar Hukumar Lafia NAJERIYA A YAU: Yadda Abincin Da Mutane Ke Ci Ke Zamewa GubaYa kuma yi kira da a faɗaɗa ilimin sana’o’i da fasaha domin matasa su samu ƙwarewar da za ta taimaka musu a kasuwa. Ya ce hakan na buƙatar kuɗi masu dorewa da aka tsara yadda ya kamata.
Mataimakin Shugaban Kasa ya bayyana cewa duk da ƙarin kuɗin da gwamnati ta ware wa ilimi daga Naira tiriliyan 1.54 a 2023 zuwa Naira tiriliyan 3.52 a 2025, gibin kuɗi ya yi yawa fiye da abin da gwamnati za ta iya ɗauka ita kaɗai.
Ya ambaci ƙarin kuɗin da aka ware wa hukumar TETFUND, UBEC da asusun tallafin ilimi na NELFUND, ciki har da Naira biliyan 86.3 da aka raba wa ɗaliban jami’a sama da 450,000 a ƙarƙashin tsarin lamunin ɗalibai.
Sai dai ya jaddada cewa gina tsarin ilimi mai ɗorewa na buƙatar haɗin gwiwa daga kamfanoni masu zaman kansu, shugabannin masana’antu, ƙungiyoyin tsoffin ɗalibai, masu bayar da tallafi da al’umma.
Shettima ya ce: “Dole mu wuce tsarin gwamnati kaɗai wajen bayar da kuɗi, mu rungumi haɗin gwiwa da zai tallafa wa dakunan gwaje-gwaje, cibiyoyin bincike, cibiyoyin sana’o’i, ƙungiyoyin kirkire-kirkire da asusun tallafi.”
Ya kuma bukaci kananan hukumomi da masarautu su ɗauki nauyin gine-ginen makarantu, gyara, tsaro da kuma kulawa da malamai.
Shettima ya yi kira ga duk masu ruwa da tsaki a taron da su jajirce wajen samar da kuɗin ilimi mai dorewa, yana mai cewa haɗin kai ne kaɗai zai iya sauya tsarin ilimi a Najeriya tare da shirya matasa domin fuskantar duniyar zamani.