Aminiya:
2025-06-15@05:48:27 GMT

’Yan bindiga sun harbe mata 2 a gona a Kogi

Published: 11th, April 2025 GMT

Wasu mahara sun harbe wasu mata biyu har lahira tare da banka musu wuta a gonakinsu da ke ƙauyen Okete a Ƙaramar Hukumar Dekina ta Jihar Kogi.

Lamarin ya faru ne a lokacin da kowacce daga cikin matan biyu ke tsaka da kula gonarta.

An ce maharan sun yi musu ruwan harsasai baya wata taƙaddama da ta ɓarke, sannan suka tsere zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Wani mazaunin yankin ya ce, “Muna cikin juyayi tun da muka samu labarin harin da aka kai wa ’ya’yanmu mata a gona. Sun je gonakinsu ne domin su kula da su a ranar Laraba, abin takaici sai wata ta ƙaddamanta ɓarke, kuma maharan, waɗanda ake zargin makiyaya ne, suka harbe su har lahira.

“Mun yi tunanin za mu ɗauko su da rai ne lokacin da muka samu labarin a ranar Laraba, amma sai muka iske gawarwakinsu an yi musu ruwan harsasai da kuma ƙuna a jikinsu.”

Cutar Kwastomomi: NERC ta ci kamfanonin rarraba lantarki tarar N628m ’Yan kasuwa da dama sun mutu bayan kifewar kwalekwale a Kogin Neja

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Ranar Dimokuraɗiyya: Gwaman Zulum ya yi wa fursunoni 66 afuwa

A ranar dimokuraɗiyyar Najeriya ta 2025, Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a ranar Alhamis, ya yi afuwa ga fursunoni 66 a babbar Cibiyar gyaran hali da ke Maiduguri.

Ziyarar da Gwamna Zulum ya kai a gidan yari a ranar 12 ga watan Yuni, 2025, ya yi amfani da ikon da sashe na 212 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba wa gwamnonin jihohi, wanda ya ba da damar yin afuwa bayan ya tattauna da wata majalisar ba da shawara kan jinƙai.

12 ga Yuni: Najeriya na bikin ranar dimokuraɗiyya An hana hawa babur da daddare a fadin jihar Gombe

“Dangane da ikon da aka bani a ƙarƙashin sashe na 212 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya (wanda aka gyara) da kuma shawarwarin kwamitin bayar da shawara kan jinƙai, don haka na yi afuwa ga fursunoni 66 da ke babbar cibiyar gyaran hali da ke nan Maiduguri,” in ji Zulum.

Ya kuma ƙara da cewa “Na kuma mayar da hukuncin kisa zuwa ɗaurin rai-da-rai tare da rage wa wasu fursunoni hukuncin zaman gidan yari a wani ɓangare na bukukuwan murnar zagayowar Ranar Dimokuraɗiyya ta bana.”

“Bayan afuwar, Gwamna Zulum ya yi wani gagarumin tallafi ta hanyar ba da gudummawar tsabar kuɗi Naira dubu 20 ga kowanne fursunoni 1,280 da ke cikin wannan gidan gyaran.”

Don ci gaba da gudanar da bukukuwan ranar dimokraɗiyya a cibiyar, ya kuma sanar da bayar da gudummawar buhunan shinkafa 300, galan 50 na man girki, da shanu guda 5.

Da yake mayar da jawabi Kwanturolan gidan gyaran hali na jihar Borno, Ibrahim Bawa ya yaba da ziyarar da Gwamnan ya kai wanda ya ce ba a taɓa yin irinsa ba.

“Wannan shi ne irinsa na farko,” in ji shi.

Yana mai cewa, babu wani gwamnan da ya gabata da ya ziyarci wurin domin yin murna ga fursunonin, musamman waɗanda suka yi sa’ar shaƙar iskar ’yanci.

Bawa ya kuma tuno da irin karamcin da Gwamnan ya yi a baya da suka haɗa da kyaututtukan buhunan shinkafa 100, galan-gadan na man girki 25, da bijimai 10 a lokacin bikin Sallah na Eid-el-Kabir na baya, wanda ya ce duk fursunoni da ma’aikata sun ji daɗin su.

Mista Gambo Samuel, wanda aka fi sani da Sarkin Gida, kuma shugaban fursunonin, ya nuna matuƙar godiya ga Gwamna Zulum dangane da wannan alfarma da ya musu na afuwar da kuma kayan abincin da ya kawo musu tallafinsa.

Ya kuma yaba wa ƙoƙarin Gwamnan na kawo sauyi a faɗin jihar, wanda ya lura akai-akai ana jin labarin sa daga sabbin fursunonin da ke shigowa wannan cibiyar lokaci zuwa lokaci.

Baya ga ziyarar da ya kai gidan gyaran halin, Gwamna Zulum ya kuma ƙaddamar da wasu ayyukan raya    ƙasa da dama na tunawa da ranar dimokuraɗiyya a cikin birnin Maiduguri da suka shafi hanyoyin mota, ruwan sha, cibiyoyin kiwon lafiya da makamantansu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Muhimmanci, Tasiri Da Kuma Amfanin Jigida Ga Mata
  • Wani Gidan Gona A Jihar Ogun Zai Fitar Da Tarwada Ta Kimanin Naira Biliyan Shida A 2025
  • Sauya Sheka Ya Sa APC Ta Samu Gagarumin Rinjaye A Majalisun Tarayya
  • Hajjin 2025: Yadda Alhazan Nijeriya 7 Suka Rasa Rayukansu A Saudi Arabiya
  • Sojoji sun kashe kasurguman ’yan bindiga 3 a Zamfara
  • Ranar Dimokuraɗiyya: Gwamna Zulum ya yi wa fursunoni 66 afuwa
  • Ranar Dimokuraɗiyya: Gwaman Zulum ya yi wa fursunoni 66 afuwa
  • Guguwa ta hallaka mutum 6, ta jikkata 30 a Taraba
  • Basaraken Da Aka Sace A Kogi Ya Kuɓuta Bayan Shafe Kwanaki 27 A Hannun ‘Yan Bindiga 
  • Ministan Tsaro Na Kasar Iran ya bada Labarin Gwajin Wani Sabom Makami Mai Limzami Mai Daukar abubuwan Fashewa Har Ton Biyu