Martani: Har yanzu muna ci gaba da yajin aiki — Ma’aikatan jinya
Published: 1st, August 2025 GMT
Kungiyar Ma’aikatan jinya da Ungozoma ta Ƙasa (NANNM) ta mayar wa da gwamnati martanin cewa har yanzu tana ci gaba da gudanar da yajin aikin da take yi.
Ministan Lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Ali Pate, ne dai ya bayyana cewa ƙungiyar ta janye yajin aikin gargaɗin.
An ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su a Kebbi Rundunar sojin ruwa za ta kafa sansaninta a KebbiDa yake magana da manema labarai bayan wani taron sirri da aka yi a Abuja ranar Juma’a, Pate ya ce matakin ya biyo bayan yarjejeniyoyin da gwamnati da shugabannin Ƙungiyar NANNM suka cimma ne.
Amma da aka tuntuɓi shugaban Ƙungiyar na ƙasa, Morakinyo Rilwan ya ce ba gaskiya ba ne cewa an janye yajin aikin.
“Idan har Ministan ne ya shirya yajin aikin, to zai iya janye yajin aikin, a ɓangarenmu yajin aikin da ƙungiyar ta shirya yana ci gaba da gudana, Ministan bai shirya yajin aikin ba, don haka ba shi da hurumin janye yajin.
Rilwan ya shaida wa Daily Trust ta wayar tarho cewa, “Akwai hanyoyin da za a bi, idan za a janye yajin aikin gaba ɗaya.
A ranar Laraba ne ma’aikatan jinya suka fara yajin aikin gargaɗi na kwanaki bakwai a faɗin ƙasar. Yajin aikin, a cewar shugabancin NANNM zai magance matsalolin da suka haɗa da rashin biyan albashi, ƙarancin ma’aikata, alawus-alawus da ba a biya ba da kuma rashin yanayin aiki mai kyau.
Wannan yajin aikin dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun takun saƙa tsakanin likitoci da gwamnati kan walwala da sauran batutuwa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Yajin aikin ma’aikatan jinya da ya biyo bayan cikar wa’adin kwanaki 15 da NNNM ta bai wa gwamnatin tarayya wanda ya kawo cikas ga harkokin kiwon lafiya a faɗin Najeriya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Farfesa Ali Pate Kungiyar Ma aikatan jinya da Ungozoma ta Ƙasa Ministan Lafiya da walwalar jama a janye yajin aikin aikatan jinya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jihar Kwara Ta Kafa Kwamitoci 2 Don Tantance Wadanda Suka Yi Ritaya
Daga Ali Muhammad Rabi’u
Gwamnatin Jihar Kwara ta kafa kwamitoci biyu domin tantance bayanan wadanda suka yi ritaya a matakin jiha da kananan hukumomi.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinar Kudi ta jihar, Dakta Hauwa Nuru ta fitar, ta bayyana cewa kwamitocin za su tantance tare da tabbatar da sahihancin bayanan wadanda suka yi ritaya, domin a biya su bisa lokacin da suka bar aikin gwamnati.
A cewarta, kwamitin mutum takwas da aka kafa don kula da kudaden ritaya na matakin jiha zai kasance karkashin jagorancin Mai Duba Asusun Jiha, wato (Auditor General), yayin da wanda ke kula da matakin kananan hukumomi zai kasance karkashin Mai Duba Asusun Kananan Hukumomi.
Sanarwar ta bayyana cewa babban burin kwamitocin shi ne tabbatar da cewa an tattara bayanan masu ritaya bisa gaskiya da adalci, tare da biyan su kai tsaye ta asusun ajiyar banki.
Ta kara da cewa, mambobin kwamitocin sun hada da wakilan tsofaffin manyan sakatarorin, kungiyar tsofaffin ma’aikata, Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), da kungiyar kwadago ta TUC, da sauransu.